💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
*This page is for u my group members, i really appreciate ur comments and du'as, Allah ya barmu tare da alkhairi, much love❤ inji Haermeen Haermmaerh💃🏻*
Page 18:
"Wai me yasa yanzu kk min abinda kk ga dama ne? Ko dan kin ga ina matuqar son ki? Ko dan kinga yanzu shiriya ta sameni kin san komai nawa shiyasa kk ganin zaki iya ci min fuska ko ki wulaqanta ni?"
Kallon shi tayi tare da sassauta fushin ta, ta aje rigar da take ninkewa zata saka a akwatin ta, ta taka gaban shi, riqe hannayen shi biyu tayi, yaso ya fisge amma kallon da take masa ba zai bashi dama ba, kwantar da kan ta tayi a qirjin shi, tana shafawa da hannin ta daya,
"Suhail ba haka bane, ina son ka gane dik abinda ka lissafa banda burin yi maka daya daga cikn su, ina son ka gane cewar mahaifin ka ya gano kuskuren shi, yana neman ka, mahaifiyar ka da take ta yarda da kai tin fari baka tinanin ya zafin rashin da yake? Ya kk jin zafi a ran ka in ka nemi wani abu ka rasa, ko ka manta yanda ka sha dambe da Samha a gidannan, don neman biyan buqatar ka ka rasa, ya zuciyar ka ta maka,.......
"Plssss Amatullah ki daina dawo da abind ya wuce, tsananin jahilci da son zuciya ne ya kaini neman qanwar ki uwa daya uba daya, dan Allah ko me za ai daga yau ki daina dakko wannan maganar abun na dukan zuciya ta,ni yanzu kunyar hada ido da Samha nake ma, inna gan ta nace mata mi?"
"Ka ce mata Samha koyi hakuro da dikkan abinda ya faru,inshaa Allahu ba zaki sake ganina da wata ba ma balle na neme ki, faqat an kashe boss ko ya kace mijina?"
Ta qarasa maganar tare da dukan qirjin shi da dunqulallen hannun ta, ta daga masa gira.
"Wannan ai wayon duka ne, kice kawai baki huce ba shine kk daken, in bai ishe ki bama qara ga qirjin nan sai na cirs rigar ki daka,"
"Haba? Cire ka gani ban huce ba,"
Aiko cire rigar yayi, vata bata lokaci ba wajen kai ma qirjin shi naushi iya qarfin ta, qara yayi ya riqe wajen, yana tari,
"Auchhhh Amatullah zaki kashe me rai, irin wannan naushi haka, da dikkan alamu kin dade kina imagening yi min irin shi,"
"Ohhhh yes na dade ina hango ni ina kirba maka naushi kamar haka,"
Naushin shi take tayi yana gudu tana bin shi, sai da suka hada zufa ta gaji ya dauke ta ya dora kan cinyat shi, yana shafa bayan ta,sai lumshe ido take tana maida ninfashin ta dake sauri,
"Yanzu dai kin huce ko?"
"Ya dangan ta da inda kace mu fara zuwa sai kaga hucewa ta, dan Allah muje ka min wanka ma, na gaji ba zan iya ba, gashi ka sa nayi zufa😏"
"Yes ma'am ur wish is my command, muje,"
Daga ta yayi, ya sauke ta qasa, ya riqe ta ta gefe anan sika cire kayan su dika suka shiga wanka, a karo na biyu,, anan ma sai da suka taba wasan da tin tana amarya ma basu taba irin shi ba.
(Ina fatan kun fahimci wani abu a wannan fadan na masoya, a dik sanda aka samu sabani tsakanin miji da mata, zama a tattauna matsala na sake saka wani bond mai qarfi tsakanin ma'aurata wanda a da ba a da shi, sabanin a yi ta ririta magana, ba a zauna an tattauna ba kowa ya fuskanci kowa, ko a zontattaunawar kowa ya riqe ego, baya son ace shine baida gaskiya, in ka saukar da kan ka kuka fahimci junan ku kai ke da riba, ga dai Suhail ya samu ribar yi mata wanka, kowa dai ya san yi ma mace wanka akwai ribaaaaa🤣🙊🙊🙊🙈🏃🏻♀)
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomantikLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.