💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 4:
Bayan sun idar ne, suka dumama sauran abincin su a oven, suka zauna suka ci, suka qoshi, Ladeefa ce ta dakko kwalba wadda da ganin ta na san ta wani abun mayen.ce, Samha ta kwace,
"Gaskiya ya kamata just for today mu tsahirta ma komai na.maye har sai mun gama sanin junan mu, baki da aiki sai watsa abun maye kin fimu zalama fa besty,"
Dariya sukai, ita kuma ta bata rai, dan a ganin ta kadan zata dan sha a ci gaba, murguda ma Samha baki tai ta turo harshe tare da kada idanun ta masu haske, ta.ja hannayen.ta.ta nade, wai ita.tayi fushi, ba wanda ya kula ta, illa Maleeka da ta miqa mata chocolate mai dadi , karba tai ta sake murmushi second weakness din ta kenan in ba kayan maye ba.
Zama Maleeka ta gyara tare da.dorawa daga inda ta tsaya a labarin nata.
"Ba a jima ba mutanen gidan mu suka san halin da muke ciki, nan Abbana ya ce a kaishi a sibiti, ana.kaishi suka duba shi suka gane ciwon rashin.bacci ke damun shi, nan aka bashi magunguna, wanda na bacci ne, daga nan Anwar baya bacci in.ba maganin nan.ya sha ba, daga baya ma ya zamana ko yasha sai ya yi halin nashi,.wato dukana, gashi lokacin cikina ya girma, ni kuma bani da wani dan uwa danake da shi mace da zai zo ya tayani zama, dan haka na shiga maqotana,.suna da wata budurwar yarinya, mai suna Khairat, a lokacin a iya ganina su ne kadai mutanen kirki a unguwar dika, ashe ban sani.ba sune zasu ja na bar komai nawa na dawo nan da zama😭"
Kallon ta sukai gaba dayan su, ta gyada masu kai cikin hawaye sannan ta ci gaba.
"Da farko Khairat komai nace tayi yi take, har wanda ban saka ta ba ma, yarinya ce mai biyayya da hankali, kafin kuce mi na fara dawowa hayyacina saboda ba aikin wahala kamar da, har na dinga jin dama qanwata ce, tinda ya hana daukan me aiki sai tana kwana, dik inda dare yayi hankalina ya tashi dan tafiya zatai, mahaifin ta dattijo ne sai yace budurwa kamar wannan bazata kwana.mana ba, ni kuma ina son ta kwana, mahaifiyar ta da suke kira da Habi itace babbar shu'umar da ban san shu'uma bace sai bayan abinda ya faru ya afku, amma a ido in ka gan ta sai ka rantse ko yatsa aka saka mata ba zata iya cizawa ba"
"Abbana.ne ya tara mu a gidan mu watarana, bayan na haihu na haifi yaro na.miji, an saka mishi sunan Abbana, muna kiran shi da Amir, nayi arba'in zan koma gidana, Abba.ya umarci Fahad daya koma gidan mu ya zauna a qasa kafin yayi aure, saboda yanzu ciwon Anwar ya yawaita, jikina kamar yanda kuka ga tabo ko ta ina haka in ciwon shi ya tashi ko giftawa nayi sai na ci duka,ko yayi ta jefe2n abubuwa, kuma ba damar na hana shi, abun ya zama.masa kamar me tabin.hankali, amma da rana sak zaki gan shi.bai da wata damuwa,"
"Ran da Fahad ya tare na kula da ba haka Khairat ta so ba ita da Habi, amma sai naga su a su wa to? Ko bi ta kan su ma ban ba, na rasa me.na masu haka kawai sai suka fara janye min, nayi tambayqr duniya sunce ba komai, Fahad shike kula da komai, wataran har shara yake mana ta tsakar gida, Anwar ko kula mu baya yi, sannan rabon da ya kusanceni har na manta, a duniya banda wanda nake qanwace da shi ya san sirrina kamar Fahad, dan haka da shi nake shawara, in ya rasa shawarar da zai ban sai yayi ta ban hakuri, yana nuna min yanda matan sahabbai da annabawa ke hakuri a gidan mazan su, saboda haka sai naji hakuri ya shigen, bana sake tada maganar,"
"Sai da Amir ya shekara daya da watanni, amma Anwar bai sauya hali ba, hakuri na ya gaza,inna zauna ina tinanin da yanda yake tattalina sai naji a da ina da dalilin zama da shi saboda ya na tattalani dik da bana son shi, amma ba zai yu ba.yanzu ba wani abu dake shiga tsakanin mu ga duka da rashin mutunci kuma na zauna, ko shawara da Fahad ban ba na je.na samu Abbana.da Mama na fada masu komai, suka ban hakuri suka ce na dawo zai sauya ne, haka na koma gidana, cikin takaici,"
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.