Page 2

1.8K 86 2
                                    

💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼






      BY HAERMEEBRAERH




*Page din farko na so a ce ya zama naki Sister Sherryna❤, amma ba komai, ke din ta daban ce ko ba page kina ruhina, Allah ya bar mu tare da aminci, ya kawo miji na gari mumini salihi, Allah ya bada ikon kammala karatu cike da nasarori da sa'a, MUCH LOVE DURLING❤*





Page 2:




Kasa zaro wuqar tai a jikin shi tsabar yanda jikin ta ke rawa, ga halin da take ganin yayar ta ta a ciki, da sauri ta isa wajen ta janyo rigar ta ta miqa mata, cikin kuka da rawar jiki ta karba ta zura, a hankali cikin azaba ya miqe, yana qoqarin kamo Samha, ta zille, ta so tabi ta bayan shi ta qara caka masa wuqar amma ba hali, saboda yanda ya ke qoqarin kama ta ta qarfi, jan hannun yayar ta tayi, suka fice daga dakin da gudu, dakin ta suka shige suka kulle qofa,tare da rungume junan su suna kuka, sai kace wadan da iyayen su suka rasu yanzunnan.

Gani yayi jinin dake zuba a jikin shi yaqi yankewa, zai iya rasa ran shi, cikin jiri ya isa waje,  a qofar dakin drivern shi  ya tsaya, kwalawa mai kira yayi, a guje ya fito, yana bude qofa yayi tuntuve da maigidn na su a qasa, cike da tsoro ya kama shi yana

"Yallabai lfy? 'Yan fashi ne suka.shigo? Subhanallahi, Yallabai kana buqatar zuwa asibiti fa, muje Yallabai na kaika asibiti,"

Cikin hanzari ya kama Suhail suka bar gidan gaba,daya zuwa wani private hospital dake kusa da su, nan da nan likitan dake duty ya hau duba shi, Allah ya taimaka sun samu blood type din shi, da sauri aka fara qara masa jini, domin jinin shi yayi qasa, Suhail baya gane komai a wannan lokacin, baya sauraron komai, ji yake kamar a mace yake ma, bayan sun yi nasarar zare wuqar ne, suka duba bata shiga cikin jikin shi yanda zata yi ma wani sashe na ciki illa ba, likitan ya dinke, suka barshi a kife, aka maida shi dakin da zai zauna, hannun shi na hanni drivern shi ya riqe masa kar ya taba jinin da ake qara masa.

Suhail bai tashi farkawa ba sai wajen goma na safe, dishi2 yake gani, a galabaice ya bude ido ya ga yana kallon qasa ba sama ba, juyawa yayi qoqarin yi ya kwalla qarar azaba, tini ya koma ya kife,nan take abinda ya faru ya dawo masa, cike da bacin rai ya lumshe ido, yana tinanin irin uqubar da zai saka su Amatullah in ya samu sauqi, musamman Samha.


Driver ya samu dama ya aje masa hannun shi a gefen gadon ya wuce gida, nan ya sanar da Amatullah abinda yake zargi ko barayi ne suka shiga suka caka.masa wuqa,bata nuna masa komai ba ta tambayi asibitin da yake ciki, ya fada mata ta koma ciki ya wuce wajen mai gadi,


"Kai yanzu kana ina jiya har barayi suka shigo sukai aika2?"

"Barayi kuma, da yaushe, me suka dauka?"

"Ina kyautata zaton ba abinda suke so sai ran me gidannan dan kuwa an caka masa wuqa ta baya,"

Gyada kai kawai Me gadi yayi, dan ya san me ya faru, dan tin gidan na sabo suke tare,drivern ne sabo a gidan bai san komai ba,


"Kaga abinnan daya faru, in kana son zama a gidannan na dindindin, to ka ja bakin ka ka ja idon ka ka ja kunnuwan ka ka toshe,ka barshi a barayi ne suka shigo, saboda direbobi da yawa sun rasa aikin su saboda rashin sirri, zaka ci gaba da ganin irin wadannan ta'addancin na faruwa a gidannan, ko a matan ko a mijin, dan haka kai dai naka ido, in bazaka iya ba ina mai baka shawara ka sa kai ka bar gidan tin kan Alhaji ya maka korar kare, ina fatan ka jini?"


Bude baki yayi xai masa tambaya da sauri ya dakatar da shi...



"Kar ka zurfafa a sanin meke faruwa, dan baida amfani, in ma ka sani ba abinda zaka iya yi"



MIJIN YA TA KO MIJINAWhere stories live. Discover now