💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 21:
"Ouchhh wannan marin fa?"
Jan shi Heeshaam yayi ya rungume tsam a jikin shi, haka shima Suhail, ji suke wani farin ciki na ratsa zuqatan su,sun dade kafin su sake juna, su kalli juna,
"Ina jiran bayanin marin daka min"
"Kana son na qara maka wanine,"
Ya daga hannun shi aaar zai kai masa wani marin, da sauri Suhail ya rife fuskar shi da dika hannayen shi,
"Allah ya kiyaye, wancan ma da na san da zuwan shi dana tare, kaima kasan ba a dukana ko?"
"Eh ni din ma ba wai daya na so na maka ba, na so na.maka iya adadin garuruwan da nai ta zuwa neman ka ban same ka ba sai anan,ashe anan din ma kana kusa dani ban sani ba sai yanzu,"
"Yeh thanks to Ladeefa and ur love for her, da wataqila sai dai ka jini a Abuja jibi,"
Da murna sosai Heeshaam ya kalle shi, ya sake rungume shi,
"Da gaske zaka je cikin son ran ka ba tare da an maka dole ba? Alhamdu lilLAAH Suhail munyi kewar ka, Mum cewa take Allah kar ya dau ran ta bata sake ganin ka ba,amma ni da zaka taimaka da.mun tafi gobe, dan na ma Mum alqawarin dik randa na gan ka a ranar ko washegari zan kai mata kai,"
"Eh tinda ni kudi ne ba, Alhaji ka bari sai jibi, kawai muje, saurin n meye,"
"A'a Suhail ba za ai hk ba, mu je goben, me mukeyi? B binda zamuyi ai,"
"K Dear dik abinda kk ce,"
"Wait, is she ur wife,"
"Yup kai ba ka qi aure ba, mata ta ce, ga ta nan har da baby,"
"Na kula da hakan ai, masha Allah, tayi gaskiya kawai kaje ka fara parking gobe mu wuce, but i have to go and see ur house,"
"Hakane ya kamata,"
"😭😭Yau bama a tani,ko kallo ban ishi mutum ba har yana shirin tafiya bai zauna ba ma, shikenan,"
Da sauri Ladeefa ta dauki ha yar shigewa ciki, Heeshaam ya bi bayan ta, yana waige yana kama baki, alamar yayi laifi babba.
"Habaaa Sweetheart kema kin san ba zan manta ki ba ai, kawai ina cikin murna ne mun dade shekara da shekaru bamu hadu da shi ba, qanina ne uwa daya uba daya, plsss smile for me mana, ko naji sanyi,"
"😏shikenan sai aka ce dan kaga qanin ka ka dauki hanyar fita ko kallo ma van ishe ka ba, sai wani leqen ka nake ina sake haqora kai kuma bama ka gani ba, to na gaji da tallata murmushin nawa nima yau kam bazaka same shi ba, kaje kawai,"
"Ni ba inda zani, sai kin yi min murmushi in ba haka ba na kwana a nan,"
Rufe baki tayi tana kallon shi, nan dariya ta kama ta,
"Ka kwana anan fa kace, tabbb tashi maza van isa ba,"
"Me yasa? Baki son ganina a inda kk ke?"
"Ba haka bane,ka bari lokaci yayi, dan kasan komai da lokacin shi, amma ka kwana anan inaaa ba zai yu ba, muje kar a ga mun dade ma ni,"
Dariya yayi, yanda ta nuna da gaske ya tafi dan kar a ga sun dade,
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.