💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 10:
"Tana ganin yanda Suhail yake damqar jikina kamar na ta ne, amma haka naga hawaye a idon ta kamar pampo ta juya ta fita da gudu, a zatona wani makamin zata dakko ta maka masa dan kubutar dani, amma ina sai qarar dakin ta naji ta buga qofar, da qarfi, ta rufe, a tare da qofar na kulle idona, wasu sabbin hawaye naji suna zuba min, Suhail qoqari yake ya kwantar dani akan gado na,wani qarfi ne ya zo min, na sa qafata a qasan shi, da alama dadin hakan yaji ya sake bude qafar shi, yana murmushi, janyewa nai nayi baya da qafartawa na buga masa a tsakiyar shi, wata qara ya sake ya kwanta a wajen yana murgususu, idon shi a rufe,dukan shi nai tayi da qafata, sannan na duqa na ja shi zuwa waje, da ga gani dukan ya shige shi ba kadan ba, ina kaishi waje na danne qofar na rufe, na saka key, maza na zira rigata na fice, da niyyar na zo wajen ku, ina fita ya riqe ni, ya dinga mari na, na sha mari har na gode Allah, yana dukana ina ramawa, haka mukai tayi, har Allah ya ban sa'a na fisge na fada mota, na kulle, gadan2n na nufi gate, da sauri me gadi ya buden, na fice, shine akaro na farko dana zo gidan nan ina kuka,kukai ta tambaya ta dalili ban fada ba, sai da na kwana uku anan, sannan Yah Amatullah ta dinga min waya da text tana ban hakuri,tana nuna min Suhail yayi nadama, d sauran su, harda tina min ashe ba zan iya riqe alqawarin da mukai wa juna ba, zan iya barin ta kamar yanda iyayen mu suka tafi suka barmu? Maganganu kala2 da suka sa dole na koma gida,"
"Lokacin dana shiga gidan yana zaune a kujera yana kallo, kallon irin finafinan turawan nan, ana ta iskanci a ciki bai damu ya sauya tasha ba, ya shagala da kallo, zuwa nai na wuce shi, kafin na shige dakina naji muryar shi,"
"Well come back home sweetheart, how was ur loooonnngg vacation, ina fatan kin manta da komai, Yayar ki ta matsa sai na baki hakuri dan ki dawo gida, she don't wanna loose a sister like u, bayan ta rasa iyaye, ok to be honest nima bana son n rasa ki, u ar such a durling u knw,"
Tsayawa nai cak a lokacin danaji maganar shi ta tsaya a dokin wuyana, ban juya ba, ya sa hannu ya shafi wiyan nawa, sannan ya yi ma wuyana kiss ya koma mazaunin shi, raina a bace yake matuqa, ji nai kamar na dawo wajen ku amma na dake na sa qafa zan shige ya sake magana,"
"Ko zaki zo muyi kallo ne, na kula rashin sanin dadin abun ya sa kk gudun shi, amma ki zo ki ga yanda ake yi, wataqila zaki bada hadin kai,"
"Na so na bashi amsa amma ance kulawa ma ai yabawa, da qarfi na rufe qofata, daga ranar ya zamana bana baccin kirki, saboda ban san me zai je ya zo ba, wata rana ya fita na kira kafinta ya zo ya sa min sakata ta ciki, Yah Amatullah bata ce komai ba, har haushin ta nake ji in bata magana akan abinda ya dace ace ta nuna bacin ranta ma ba iya magana ba, gashi tsananin son da take masa komai namu basirri sai ta kwashe ta sanar da shi, gaba daya ta zama kamar wata doluwa, kai ko da period nake sai Suhail ya sani, dik wani zance na ya zama kamar a kan idon shi ne, in kaya na siyo musamman qanana sai tace itama tana son su, zata siya ta sa Allah yasa ya mata kyau kamar ni, shi kuma da dadin baki sai yace ai sai ya ma fi maki kyau, sai da ta kai na daina hira da ita, na daina fada mata dil wani abu nawa, saboda kar naji shi a bakin shi, adadin yanda yake bamu kudi ya ninka shi, kashe mana kudi yake kamar baya son su, a yanzu duk.kulawar shi ta dawo gareni, ya zama ko a gidan yake bai zaman parlourn dakin su, sai dai babban parlour, dik wata wucewa ta a kan idon shi, wataran in zan wuce sai dai na ji shi ya daki duwawuna ta baya yace "Nice Ass babe" da ire-iren kalaman nan na marasa tarbiyya,"
"Akan abinda yake ya sa mun maida gidan kamar na 'yan dambe, gobe wance za a kai asibiti, jibi shi za a kai, gata ita ko ni, masu aiki kuwa saboda wai sa ido ya kori sunfi biyar, zaman arna kawai ake a gidan, a dalilin haka ne dana koma ya nemi ya ketan mutuncina na kare kaina, ya koma wajen ta, na caka masa wiqa shine aka kaishi a sibiti dan rashin zuciya kuma take masa girki ta kai masa,"
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.