Page 13

1.1K 48 0
                                    

💅🏼  MIJIN YA TA KO MIJINA  💅🏼









     BY HAERMEEBRAERH











Page 13:







Basu bude ido ba sai da suka ji mota ta tsaya, sannan suka bude idon su, kusan a tare, Ameer ya riga Amrah tashi, ganin matar da ta dakko su sukai a waje da wani suna magana, ba su san shi ba,


"Amrah ina ne nan?"

"Ni ma.na sani, wataqila wajen Abban mu zata kai mu, Allah yasa wani gidan aka canja mana mu huta da dukan Aunty,"


"Ameen, amma ni dai nafi son naga Abbana nan wajen bansan ina ne ba,"

"Kids kun tashi? Maza muje to gidan da zaku sauya kaya, kuci abinci sannan muje mall, Abban ku ya turo saqo ba zai samu damar zuwa ba, saboda aiki ya masa yawa,"


Daga mata kai kawai suka yi, ta bi motar Fahad, a baya suka wuce unguwar da yake da zama, wani babban gate suka ga an bude, Fahad ya saka motar shi ciki, bakin ta hude dana yaran tare da kiran

"Wowww"

Basu sake sakankancewa da kyaun gidan ba sai da ta kama hannun su suka shiga ciki, gaskiya Maleeka tinda take bata taba ganin gida mai kyau haka ba.


"Bismillah muje mana, naga kun tsaya,"

"Yah Fahad wace sana'a kake haka? Wannan gidan...... and all the cars out side.....ban gane ba? Ni yanzu a tsorace nake da kowa, dan Allah kamin bayanin gaskiya, zai yu mu zauna anan ko na kama mana haya har na gama me nake?"


Dariya yayi sosai, sanan ya nuna masu wajen zama, ya dauki Amrah ya dora a jikn shi, bayan sun zauna ne yayi gyarab murya sannan yace,



"Maleeka ,Maleeka, Maleeka, wato kina zaton ko ina wani sana'a mara kyau kenan? Hhhhh gaskiya kin ban dariya, sana'ar da muke yi ni Abba, Anwar, ita nake yi har yanzu ban sauya ba,in kin kula ni banda iyali, banda uwa banda uba, sai 'yan uwan mahaifana, danake kula dasu, a qauye, da ina da mata da yara shine dukiyata ba zata ba kowa mamaki ba, amma yanzu na tara ba masu cin ta kamar masu iyali, kinga ko dole kiga gida haka,"



Ajiyar zuciya ta sauke mai qarfi, wadda zata nuna ma kowa cewar hankalin ta ya kwanta.


"To ku tashi muje mu ku yi wanka, muje aci abinci, a siyo sabbin kaya, dan a sauya na makaranta ko?"

"Dan zo muyi magana pls,"

"K"

Tashi sukai suka je wajen dinning, suka tsaya, kallon yaran take cike da so da qauna, da kuma tausayawa, dan ta na sane da wahalar da Auntyn tasu take basu, da dik wata rayuwa da suke ciki, sun san mahaifiyar su rabuwa sukai da Abban su, dan haka tace ma Fahad,

"Yah Fahad shawara nake nema, kana ganin na nuna ma yarana nice mahaifiyar su ko nayi shiru, na rasa ya zan, ga qarya danake ta shara masu, gashi na tabbata ba yau ko gobe zan maida su ba, plsss ya zanyi da ba zai affecting tinanin yarana ba?"



"Kar ki damu muje mu sanar dasu komai, yaran nan suna da wayo fiye da yanda kk zaton su, muje,"


Cikin dari2n abinda zasuyi ta bi bayan shi, zama sukai ta toshe bakin ta da hannayen ta da sukai sanyi, ta qurama yaran ido, tana kallon kuma Fahad.



"Kids, ku saurari abinda zan sanar daku da kyau, ku fahimta kunji? Abinda baku gane ba inna gama fada maku komai sai ku min tambaya kunji?"

MIJIN YA TA KO MIJINAWhere stories live. Discover now