Page 15

1.1K 57 0
                                    

💅🏼  MIJIN YA TA KO MIJINA  💅🏼







       BY HAERMEEBRAERH







Page 15:






Suna isa gidan ya tsaya kalle2n harabar gidan, masu aiki na ta masa sannu da dawowa, suna mishi ya jiki, daga kai kawai yake kamar wani me nazari, bai ga motar Samha ba, kallon Amatullah yayi wadda tai kicin2, dan ta kula da me yake kallo, wucewa tayi, ciki, ya bi bayan ta,



"Ina take?"


"Bata zama anan yanzu,"

"What do u mean bata zama anan yanzu? Kina hauka ne? Ina kk barta ta tafi?"


"Indai Amatullah kk aure ga ta a gaban ka, amma in Samha ka ke aure bata nan, ta tafi inda hankalin ta zai kwanta, ta kammala karatun ta ta tsaya da qafar ta ba tare da wani ya keta mata haddi ba har mijin da zata aura ya raina.ta yace ta gama.lalata da mijin yayar ta sannan tai aure ba,"


Cikin matsanancin fushin da bai san tana da shi ba take magana, yayi matuqar mamaki kuma da kasancewar hakan,  barazana ya mata ya daki table din gaban.shi ya na zaro ido,



"Ki buga mata waya ta dawo yanzunnan, bana son iskanci, koma me ya faru Kawu da Inna ni suka bawa amanar riqe ta, dan haka dole ta dawo gidannan da zama, ko na janye dikkan tallafin danake bata na makaranta, kuma ta ajen mota ta,"


Cikin takun isa da bacin rai, ta kafe shi da ido, ta taka gaban shi, ganin yanayin idon ta da yanda fuskar ta tayi jawur, ya sashi ja da baya,




"Alhaji Suhail bari kaji na fada maka wata magana guda daya, maganar da zan fada maka daga zuciyata take fitowa, ka sani muddin kayi abinda zai lalata rayuwar qanwata, ko da da kallo ne this time around ba zan raga maka ba,in raina ya baci na kan aikata abinda daga baya kowa yake dana sani, in baka da wannan ilimin kaje ka tambayi Kawu, ko a baya na.kyale ka ne saboda tsananin son danake maka,amma a yanzu, zan iya aje son na maka dik wani rashin mutuncin d baka zata ba,"


Tana gama fadin haka ta wuce shi ta zari wayar ta tayi daki, ta bar shi nan yana hadiyar yawun da ya qafe a maqoshin shi, jin ba wani yawu a bakin nashi.ne yasa shi nufar fridge dan daukan ruwa ya sha, yana balle murfin kuwa ya kafa kai yana zuqar ruwan, sai da yasha rabi ya sauke, wace ce wannan? Ko an saiya masa mata ne?




Amatullah na shiga daki ta dinga maida numfashi tana shaqa, tsabar tsoro, lallai she ia a great actress, ta ya akai ta iya masa maganganu haka, da ace koya mata akai lallai da bata haddace su ba, amma dake daga zuciyar ta suka.fito ga su nam ta zayyana masa su, dole ne ta jinjinawa kan ta, tsalle tayi ta fada gadon tana juyi,daga farkon gadon zuwa qarshe, tare da addu'ar Allah yasa yaji gargadin ta.



Yau sati daya kenan da dawowari shi, sai Samha ta san baya nan take zuwa, dan sai ta ma Amatullah waya take zuwa, bata wuce awa daya ta tafi, Amatullah kuwa ta riqe wuta, kwata2 ta daina sake masa fuska yana raina mata wayo kamar da, yaje yayi.iskancin shi ya dawo ya qarasa da ita, ko kudi ya bata yanzu sai ta tambaye shi na.meye? Sai ya hau cewa ba zai mata kyauta ba kenan sai da dalili? Ta kan ce masa ba haka bane,kawai dai gwanda ta sani.ne,kar taje wani part na jikin ta akai ciniki, ranshi ko yanzu zai baci ya hau masifa, yau ma hakan ce ta faru.



"Amatu ga wannan ko zaki buqata ni zan dan fita, ina da wani.kira da aka min mai mahimmanci,"



"Me za ai da su?"


"Wai ni yaushe kk sauya halaye ne? Waya koya maki halayen nan na banza ne. Da bana baki kudi sai na fada maki na meye?"





"Tabbas kana ban kudi mana,amma kuma ai qanwata kk nema shiyasa, yanzu ko da bata nan dole ne na tambaya na meye ko? Kai ni na ma gaji fa, na aure ka ban san kowa na ka ba, ban san sana'ar ka ba, na baka nan da kwana uku ka sanar dani komai, in ba haka ba zan bar maka gidan ka,"

MIJIN YA TA KO MIJINAWhere stories live. Discover now