💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 3:
Tana tashi daha skul gidan su Malika ta wuce, dan ba ta son su yi ja in ja da yayar ta ta akan kai masa abinci da tai, tana son ta dan huta da komai da yake faruwa da ita kan ta koma.
Kitchen ta gan su, da sallama ta shiga, ta daga masu hannu ta wuce, sai da tai alwala tayi sallah, sannan ta sako dan qaramin wando da vest ta gyara gashin ta ta taho kitchen din itama,
"Wai me kuke yi ne tin dazu, ga gidan ya cika da qamshi, ga shi kun dade baku fito ba,"
Kallon ta sukai,.sannan suka ja hannun ta, qaton cake ta gani, an saka Happy 25th birth day Samha, idon ta ne ya cika da kwalla, dan ita ta manta ma gaba daya yau birthday din ta tana cikin tashin hankali, ya zata samu tinawa, rungume su tai suka dan jima a haka,
"Thanks guys, i love u,"
Ladeefa ce ta kama kumatun ta, ta turo baki kamar tana wasa da yaro,
"Awww u ar so cuteee, we love u more,"
Kwacewa tai ta harare ta, dan ita ce sa'ar ta, Malika ta girme su, lakutar cake din zatai Ladeefa ta make hannun ta, tana kada mata tsaya, sama tai da idon ta ta kwantar da kan ta a bayan Malika, tace,
"Ki mata magana, kar na shaqe mata wuya, ba ruwana ni,"
"Eh ai ni ce qaramar dangar ki kin shaqe ni mana,.baki shaqe shegen Yayan nan naki ba sai ni, matsoraciya kawai"
Kallon ta tayi da fuskar da ta sa suka daina dariyar domin sun san me hakan ke nufi, ta wuce parlour, ta zauna dabar a kujera, tare da limshe idanun ta,
"Da baki mata wannan wasan ba, this is her day, shiyasa tin da muke bana son na zurfafa tambayar kowa labarin shi sai iya abinda kowa ya so mu sani, dan haka u have to say sorry,"
"Ok"
Daukan cake din sukai, suka je parlourn suma, tare da mata waqar BD,murmushi tayi mai kama da yaqe, ajewa sukai suka koma kwaso sauran su pepper chicken da fride race with salad, sai drinks wanda Ladeefa ta so a saka da na maye Maleeka tace a'a yau so take su taba hirar yaushe gamo.
Dan haka cikn dabara da wayo suka hilace ta, suka yanka cake suka zauna suna cin abincin suna hira, cikin raha da shaquwa irin ta qawaye.
A tare suka gyara wajen, suka wanke kwanukan, sauran abincin suka saka a fridge, kiran sallar magariba ne ya sa suka tashi yin sallah, Maleeka da bata sallah tana zaune, tana latsa wayar ta.
Bayan sun dawo ne suka zauna, Maleeka ta kalle su ta yi gyaran murya, sannan ta fara magana,
"Sanin kan ku ne munyi shaquwar da ta wuce ta qawance ta kai ta 'yan uwan taka a cikin shekaru qalilan, amma har yanzu kowa tana riqe sirrin rayuwar ta, wanda ina ganin zama da sirri a tsakanin junan mu ba zai bamu damar zama cikakkun amintattun juna ba, kuma ba laifin kowa bane illa nawa, dan haka nayi maku alqawarin jin labari na a yau, inshaa Allahu, dan yanzu banda 'yan uwan da suka fi min ku"
Gyara zaman su sukai, tare da tabbatar mata da abinda ta fada gaskiya ne kuma suna sauraron ta, dan haka ta fara magana..
"Kamar yanda kuka ji suna na, Maleeka, to sunan mahaifina Muhammad Auwal, Mahaifiyata Zulfa'u, mu asalin 'yqn jihar Nija ne,mahaifina attajiri ne wanda ya gaji dukiya wajen mahaifin shi, shi kuma ya gada wajen mahaifin shi, kenan dukiyar gado gare mu, mahaifin na da son talakawa, nice babbar diyar shi, daga ni ba su sake haifr wata ba, har na bar gida, mahaifina anyi2 ya qara aure yace ba zai ma mahaifiyata kishiya ba,"
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
عاطفيةLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.