Page 6

1.1K 70 0
                                    

💅🏼  MIJIN YA TA KO MIJI NA  💅🏼




     BY HAERMEEBRAERH




*Ina godiya da addu'o'in ku, ina ma kowa fatan alkhairi, Allah ya kiyaye mu ya kare mu daga sharrin zamani, jazakumullahu bi afdhadul khair*




Page 6:




"Wai ya naga yau gaba daya ko bacci bamu da alamar yi ne, dare fa yayi,"



"Wanne bacci mutum yaji wannan labarai na tashin hankali? Sannan ai ba wani daren da yayi sosai akan yanda muke bata lokaci a banza ma"


"Besty ni dai yunwa nake ji, ina mamakin masu aiki a gidan redio, wataqila suna gama labarai suke zuwa cin abinci,"

"Ba wani nan ke dai dake rumbu ce komai a zuba shiyasa kk ji haka,"


Kokawar wasa suka kaure da ita da kyar Maleeka ta shiga tsakanin su, Ladeefa miqewa tai taje fridge din su ta kwaso masu cimar zaqi kala2, da fruits, ta hado da ragowar cake din da sukai baking, ta zuba a tsakiyar su, ta zauna, cinyoyin ta duk a waje, duka Samha ta daka mata a guda daya ta kalle ta, ita kuwa a furgice ta fara sosawa tana neman ba'asin dukan,


"Malama wannan wai banawa bane? Wayace ki dakko da shi,"



"Shine zaki min wannan dukan kamar an danan iron naji, an dakko din, kuma kin san Allah kin gama ci kenan,"



"Tabbb ko a ban naci ko na fasa fadan labarin"

Da sauri ta tura mata gaban ta har sauran abubuwan da ta debo, dariya sukai, sannan suka fara taba kayan ciye2n at the same time Samha ta fara magana.



"Ku kunji dadi koma me ya faru kun taso cikin gatan ku, da dukiya da wadata, amma mu, hummm mu, daga wahala sai baqin talaouci daya mamaye zuri'ar Dan Kano,  haka ake kiran kakan mu, wanda yake da yara hudu, maza, Abbanmu shine qarami, a cikin su dika, Abbana shine mafi talaucin cikin su, komai sai 'yan uwan shi sun taimaka masa, hatta aure yi.masa kawai akai, amma ko sana'a ya kama ba abinda ke zama masa, Umman mu itace suke da dan abin hannu, ita da Yayan ta namiji, da yayar ta mace, sun gaji gonaki da wasu kudade wajen iyayen su, dan haka Ummana da dangin ta, Kawu Abu, da Inna Samirah, suna taimakawa, amma muna shan gori sosai, wajen su, su basu da yara a lokacin, dan haka suke cewa Umman mu tana ta zuba yara ga shi mijin ta talaka bai da halin riqe mu, a dole suka kaita aka juya mata mahaifa dan kar ta sake haihuwa, Abbana bai da tacewa saboda da yayi magana za a zage shi tass, saboda talaka ne shi,"



"Da sanyi ana yawan yin gobara, a wannan lokacin ne gidan su Abbana ya kama da wuta, 'yan uwan shi dika ba wanda ya tsira, har mahaifin shi, sai mu kadai, dake dakin mu ne na qarshe, amma kunsan me mutane suka ce? "

Girgiza mata kai sukai, nima da nake rakube na girgiza qaton kaina irin na Mum Sultan🤣.

"Cewa ake tayi Abbana shine sanadin kashe 'yan uwan shi, dan ya samu ya gaji dikkan wasu dukiyar da suke da ita, tinda ya fisu talauci, yana baqinciki da samun su, Abbana haukane kawai bai ba, yayi kuka, muma mun koka sosai, saboda ya san ba abinda ya janyo masa hakam sai baqin talauci, da yana da kudi da ba mai zargin shi, dangin Ummata ma sun yarda da hakan, kowa ya fara gudun Abbana saboda wai baqin hali ne da shi, da yaga kana da shi zai kassara ka, mutane qalilan ke hulda damu, saboda sun san halin Abbana mai kyau ne, sharri ake masa,"


"Ba wanda ya san Abbana na da ciwon zuciya , dan bai taba tashi mun gani ba, kwatsam watarana yana kasuwa, yana saida albasa, aka dawo mana da shi a hannu, da guntun albasar a daure a buhu, ya rasu, Ummana kasa komai tayi, har kukan ma bai zo mata ba a lokacin, ni da Amatullah kuwa sai kuka muke muna kiran ya dawo kar ya barmu, bamu da kowa bamu da komai, in ya barmu ya zamu rayu ba shi? Shine gatan mu, abu daya Umman mu ta iya furtawa shine,"




MIJIN YA TA KO MIJINAWhere stories live. Discover now