💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 24:
Yana bude qofar shiga parlourn su ya fara kiran iyayen nashi, da hanzari kuwa suka fito, musamman Bilkisu dake tintibe da carpet, zama yayi ya yi tagumi, Abban shi ne ya dafa shi, cike da tausayawa, kallon Maman nashi yayi, wadda har fuskar ta ta sauya, saboda ta ga alamun rashin nasara, dariya sukaji ya yi da qarfi, yana nuna su,
"Kalli yanda kuka yi da fuskokin ku tin kan kuji me zan ce, albishirin ku,"
Cike da zumudi Bilkisu tace,
"Goro yaya"
"Ta amince dani dari bisa dari, sannan ina ganin ba zan zuwa sama da biyu ba gaskiya za a tura magabatana ayi magana Abba sai kaga yanda ta mato da ganin dan ka,"
Daga gira yayi, Abban nashi kuma ya dan daki qeyar shi,
"Oh yanzu da ta amince da kai ka shigo mana da fuska kamar wanda ya amshi maruka? Ba wannan ba ma, ni har yanzu banji ka fadi asalin su ba ko wani abu mai mahimmanci da ake nema wajen neman aure, saboda a gaskiha dik yanda kk son ta ba zan bari ka auri yar gidan qananan mutane ba, qanqanta kuwa ina nufi marasa tarbiyya,"
"Abbbaaaa komaii fa a hankali ake yin shi, ka bari inshaa Allahu zaka ji komai, all i knw now is that she is an orphan, iyayen ta dik sun rasu, amma Abba Mama in kuka gan ta zaku so ta, tana da tarbiyya sosai, kuma na tabbata abinda kuke so kenan, tana tare da Yayar ta, a gidan yayar take da mijin ta, a yanzu tana shekarar qarshe na karatun likita, Abba dan Allah kuyi sauri a yi bincike, ina son ta sosai,"
Mamakin dan nasu sike sosai, wanda ya hana Maman shi magana, dan a iya sanin ta in ana son a ga bacin ran shi ko ya qi magana daga dare har rana a masa maganar mace, har tana cewa za a nema masa taimako wata qila baida lfy ne, amma daga ganin Samha ya rikice, dole tana son ganin wannan yarinyar data sace ma danta zuciya da ruhi.
"Mama bakice komai ba tin dazu,"
"Humm me zan ce? Iyaka nace ubangiji ya tabbatar mana da dikkan abinda yake alkhairi ya kare mu daga kishiyar shi, in matar ka ce ta alkhairi Allah ya baka ya sanya albarka dana, ina son farin cikin ka, dan haka bn da ja a maganar auren nan, iyaka ta kulan da kai ko mu sa qafar wando daya da ita,"
"Ni kina ban dariya in kina wasu maganganun sai kace ba da namiji bane, ki cirs ranki akan Imaam, ki jira muga wace irin mace zai aura, wadda zatana ara mana shine ko wadda zata dauke shi ne sai taso mu gan shi,"
"Dan Allah Abba ku daina magana haka mana, ni dinnan ba macen da zata juyar da ni daga barin iyayena abin sona, na yi imani wannan yarinyar sai dai ta kusanta ni da ku ba zata taba nesanta ni da ku ba,"
"Allah ya sa,nima nace Allah ya sanya albarka yaya, ko ba a neman albarkar qanne?"
"Ana nema dear sis, zo mije na baki labarin yanda muka sha hira,"
Kama hannun ta yayi suka shiga dakin shi, suna tafe yana fara bata labarin zuwan shi gidan, tana ta dariya, iyayen na su kuwa suka kalli juna cike da so da qauna, suna jin dadin yanda yaran su ma suke son junan su.
(Ina fatan makaranta mun kula da abubuwa masu tarin yawa, daga kan soyayyar dake cikin gidan su Imaam, wadda ta sa yaran da iyayen kansu yake a hade, inda aka samu hadin kai kuwa ba abinda ke kawo ma wajen naqasu a rayuwa, komai za a yi shi yanda ya kamata, rabuwar kai ke kawo tabarbarewar al'umma da zuri'a gaba daya. Sannan ina fatan mun kula da yanda Imaam ke yabn tarbiyya irin ta Samha tin kafin ya san ita din wacece, ana son mace ta kasance, mai kyakkyawan hali da dabi'a ta yanda mijin ta zai so ta domin su, kuma in ya kaita gidan ya same ta yanda ya tsammata koma fiye da haka, mafi aksarin mata yanzu, a waje suke nuna su na Allah ne, da kyaun hali, sai sun shiga daha ciki kuma halayen su su sauya gaba daya, ina fatan baki daga cikin su,🙊)

YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.