💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
*I am sorry for the late update durlings, i was kinda busy ne shiyasa, amma kun san ba zan qi typing haka kawai ba, thanks for the calls, messages and du'as, much love from Haermeen Haermmaerh*❤
Page 22:
Alhamdu lilLAAH komai nisan jifa zai fado qasa, komai nisan dare gari zai waye, su Maleeka da Ladeefa sun samu nasarar kammala karatun su sun zama cikakkun likitocin mata,babban abinda suke buri kenan a rayuwar su, sakamakon ganin yanda asibitoci suka rasa likitoci mata, kuma mata kullum qaruwa suke a asibitoci da lalurori kala2 wanda mata 'yan uwan su ne kawai yafi dacewa su kula da wannan bangaren.
Ladeefa kuka take tayi, kamar wata qaramar yarinya, d kyar Samha ta lallashe ta,
"Haba besty meye abin kuka? So kk kan ki ya fara ciwo, ko muma ki samu kuka,ya zama ba mai lallashin wani? Zafa ki dinga zuwa ganin mu muma zamuna zuwa ganin ki, plss ki daina kuka😥😪"
Itan ma dauriya kawai take yi, yanzu ita daya za a bari a wannan gidan ta qarasa karatun ta, ga abokan ta na qut da qut zasu tafi su barta, gaba daya sai taji ai kuka ita ya kama.ma ba su ba.
"Besty Ladeefa bai kamata kina kuka gaba Samha ba ma ai, ita ce za.mu lallasa saboda ita zamu bari fa ta qarasa nata, dama kuma rayuwa haka ta gada, dik shaquwar uwa da diyar ta zasu rabu in aure yaxo,dik shaquwar yaya da qanwar ta zasu ravu in aure yazo, dik shaquwar qawaye watarana sai sun rabu, gamu muma lokacin mu ya zo,dan haka zama zamuyi mu yiwa kan mu nasiha, mu yafi junan mu, a zama harshe da haqori ma ana sabawa, balle mu masu satar abubuwan junan mu,"
Dariya suka saka suna hawayen rabuwa da juna, rungume junan su sukayi, suna sake kokawa, ko horn basu ji ba sai maganar shi suka ji.
"Gurls ku tashi haka, is gatting late, yau nake son komawa Abuja, kuyi hakuri, ai ba a rabu ba ana tare, Ladeefa Baban ki ya turo mota, guy dinnan, yana ta zaune a mota bai kamata ba fa, ko ruwa baku bashi ba, kuna nan kuna zubda ruwan hawaye,"
Maleeka ce ta kalle shi cikin shagwaba,
"Kaii Yah Fahad baka san zafin rabuwa d masoyi bane?"
Kallon ta yayi, wanda ya sa ta shagaltu itama da kallon nasa, cikin so da qauna ya matsa gaban ta, sannan yace,
"Ni kuwa na san zafin rabuwa da masoyi, ni da nai shekara da shekaru bana tare da abar so na, kuma ina ganin ta tare da wani cikin gida daya, daga baya na dade ban gan ta ba sai dai naji muryar ta lokaci zuwa lokaci a waya, kin ga ko dik wani wanda zai bayanin radadin rabuwa da masoyi a bayana yake ko? Dan haka hakuri zakuyi,"
"Inshaa Allahu ba zaku sake rabuwa ba har abada, sai mutuwa, annnnddd ka bar kallon ta haka kar ta narke dan naga dik ta wani lagwabe;"
A tare suka ce
"Samhaaa,"
"Whattt?? Qarya nayi? Dube ta fa,"
"I will miss u so much besty, ko dan tsokanar ki,"
Haka dai suka fita, Fahad zai maida Maleeka gida, motar shi cike da kayan ta, har bayan seat, Ladeefa kuma tare da drivern da Baban ta ya taba hado ta, ya bata rai kamar bai taba dariya ba saboda bata mai lokacin da tayi, itan ma bata rai tayi, sai da ta shiga, ta dagawa Samha dake qoqarin yin kuka gira, ta mata magana qasa2
"Makewa zan na bata rai nima kar ya latsa ni, yace na dade,"
Murmishi Samha tayi, irin wannan qarfin halin na Ladeefa ke sata nishadi, ga ta bata da gaskiya sai ta fika fushi.
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.