Yau kawu baki har kunne,sai murna yake,zai aurar d diya,mutane na taya shi murna,wasu na ganin ya riqe zumunci,sun aurar d ta farin ga shi zasu aurar da ta biyun ma,sai addu'a ake masu,ana jinjina masu,wasu har sanar d su suke, a wannan zamanin ba a samun masu riqo d zumunci kmr su,kawu fa jiki ya yi sanyi,dan d mutanen nan zasu san me y aikata,da tsinuwa ce zata raba su,an daura auren Samhah d Imaam akan sadaki dubu Hamsin,a can unguwar su Maleekaa ma haka abun yake,inda aka daura auren ta da masoyin ta Fahad,akan sadaki kwatankwacin na Samhah,sai garin zariya,inda aka daura auren Heeshaam da Ladeefah,akan sadaki dubu dari,ko wanne bangare, cike suke da murna d farin ciki, dik wani masoyin su, ya samu halartar bikin.
Ranar daurin aure ranar iyayen su mata sukayi walimar su,da yamma kuma aka shirya amare sai Abuja,ta jirgi suka wuce, tare d angwayen su,sun so kama hotel amma Dad din su Suhail y hana,dan yana d gidan d yake saukar baqi,mai girman gaske, anan amaren suka hadu, babban parlourn da ke gidan, Amatullah d cikin ta yayi qato,haihuwa ko yau ko gobe,Suhail baya iya barin gefen ta,ko cup t aje sai tayi d gaske take iya duqawa dauka,wannan ne dalilin da ya sa yake tare da ita a koda yaushe.
Hira suke tayi, ba su ji shigowar angwayen ba,sun yo masu siyayyar kayan kwalama, da abubuwan sha.
"Gurls na ga alama kuna cikin murna,irin wannan shewa haka?Allah ya sa ba gulmar mu kuke ba"
"Malam ya naji kace gurls ko baka ganni cikin su bane?"
Dariya sukai masa Heeshaam yace,
"To ai gani mukai kun saje"
"Ban son wulaqanci fa, baku ga madam ba lfy ba ne? Ai sai ina kusa,wadannan ban basu amanar mata ta ba,suna wannan halin"
"Yah Suhail ka dai so zama ka hn mu hirar da mukai niyya ne,amma da ka bisu,ba abinda ba zamu mata ba,kuma ma ai ba a son mai cikin daya tsufa d son jiki"
"Babu ruwan ku, muna motsa jiki, ko maman biyu?"
Nan d nan ta bata rai,kullum tsokanar ta yake saboda girman cikin,ita ko wahalar da take sha shi yasa bata son taji yana kiran biyun nan.
"Yi hakuri my Ama, daya zaki haifa abin ki"
Dan murmushi tayi, dan kta magana ma yanzu wahala take bata,kawai bikin dan ya zama dole ne, amma zama a gidane yaa kamace ta ba yawo ba.
Bubbude abinci sukai kowa ya zauna kusa da matat shi,Imaam na debo abinci sai saitin bakin Samhah,wata kunya ce ta kama ta ganin dik wajen an girme ta,da sauri ta kauda kai,tana masa nuni d ido,alamar akwai mutane a wajen, kallon ta yake tare da langwabe kai,ya aje spoon din,tare da nade hannayen shi,alamar ba zai ci ba to.
Kallon gefe d gefe tayi taga kowa qoqari yake ya ciyar d matar shi,Ladeefa kuwa a tare suke ciyar d juna,ba wanda ya damu d su,nan ta sake kafadun ta da ta riqe saboda kunya,diba tayi ta kai masa daidai bakin shi,kamar jira yake kuwa,Anwar da bai d kowa kuwa gefe ya je ya haye saman dinning yana ci, yana danna wayar shi,ya matuqar basu tausayi, Imaam na da wani babban qudiri a kan Anwar da Bilkisun shi,dan haka ya dauke kan shi daga kallon Anwar din,nan sika ciyar d junan su suka qoshi, suna gamawa matan suka gyara wajen kowaccen su ta kalli 'yar uwar ta,suka dan yi dariya,kusan a tare suka miqe, da sauri suka nufi wani daki,mazanne suka bisu d kallo,Imaam mara hakuri bai gaza ba wajen magana.
"Ladies ban gane b?ina zaku?"
Samhah ce ta juya dawani salon kashe jiki, ta kashe mashi ido sannan tace,
"Bacci, good nyt to u all"
Suhail d Amatullah sai dariya suke,Maleekaa ma sai d safe ta masu,Ladeefaa kuwa ko juyawa batai ba,saboda Heeshaam na mata kwarjini, in yace ta koma rusa masu plan zatayi,dakin ta fada, su Samhah suka bita, dariya suke masu, Fahad ya kalli 'yan uwan nashi baki bude,Me matan nan suke nufi??? A zaton su zSu kwana gu daya kowa d matar shi,tinda dakunan zasu isa,shi ne sika hade kai suka bar su nan?lallai basu kyauta masu b kuwa.
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.