Page 9

2.1K 183 8
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
 
           *_MENENE MATSAYINA ?_*
                 *(fictional story)*

       *Written by*
Phatymerhsardauna
       *🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated to My Lovely sister Maryam*

*🌈Kainuwa Writers Association*

~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~

~[23 Friday August 2019]~

       *Wattpad*
@fatymasardauna

*Editing is not allowed 📵*

*Page1⃣4⃣*

Faɗuwar gabanta ne yatsananta, bayan sun gama waya da Farhan ɗin, cikin sanyin jiki tawuce bathroom haɗe da sakarmawa, kanta shower koda zataji sanyi acikin ranta.

Koda tafito doguwar riga marar nauyi na material tasanya, ba kaɗan ba kayan ya amshi jikinta, mayafin kayan kawai tayafa akanta, haɗe da sa kai tafice daga ɗaki, zuwa yanzu abun data keji ya girmemawa tunaninta.

Kaitsaye wajen Ummie dake tare , da baƙinta afalo tanufa ,  kwan ciya tayi ajikin Ummien haɗi da kwantar da kanta abisa kafaɗan Ummi'n,, cike da kulawa Ummie kekallonta haɗi da cewa " maike da munkine Farhana , keda zuwa yanzu yakamata ace kinshirya amma yana ganki haka ? ,,

" bazan iya shiryawaba Ummie, faɗuwar gaba nakeji kirjina yana bugawa da sauri sahanun ki kiji Ummie, ina tsoron abun da zai faru agareni ,, takai karshen zancennata alokacin data ɗaura hanun Ummie akan kirjinta.
Kallonta Ummie tashiga yi har na tsawon wasu sakanni, kafun ta nisa haɗi da cewa " ki kwantar da hankalinki kinji Farhana, ba bu abun dazai sameki insha Allah, me yiyuwa  kina jin hakanne saboda auren ki da za a ɗaura gobe, kar ki wani damu kanki dama duk Amare sukan tsintar kansu acikin irin wannan yanayin,, Ummie tafa ɗi haka dan ta kwantar mata da hankali.
Kwarai ta ɗanji sanyi acikin zuciyarta, dajin maganan Ummie'n dan haka ta miƙe daga jikin Ummien tawuce ɗakinta, da kallo kawai Ummie ta bita harta ɓacewa ganinta.

tana shiga cikin ɗakinnata kan bed tafaɗa, haɗi da sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi , some minute bacci yayi awon gaba da'ita.

Farhan ne kwance cikin jini akan titi, yayinda Farhana ke tsaye agefensa tamkar statue bata ko motsi, hanun sa ya miƙomata cikin wata irin murya yace da'ita " zomu tafi Farhana, kizo mutafi karki barni ni kaɗai ina da buƙatarki ako'ina zo mutafi,, daga haka kuma saitaga yadaina motsi komai nasa yadaina aiki,, 

Arazane Farhana ta tashi daga mafarkin datakeyi, take jikinta yasoma ɓari zufa yashiga ketowa takowani , saƙo na jikinta , mafarkin datayine yashiga da wowa cikin kwakwalwarta filla filla,  a ki ɗime talalumi wayarta dake aje gefen gado, haɗi da dannamawa numbern Farhan ƙira , abun da bata taɓa jiba idan taƙira wayarsa shi taji  wato "Switchoff" batayi yun ƙurin sake ƙiraba, tayi cilli da wayar amatuƙar zabure ta mike daga kan gadon , aguje tafice daga cikin ɗakin.

Da gudu ta ƙarasa wajen Ummie dake tsaye idanunta cike tab da ƙwalla, sam bata lura da halin da Ummien take cikiba,  rungumeta tayi ta baya haɗe da fashewa da kuka " Ummie kitai makeni nayi mafarki wai Farhan ɗina ya rasu, kitai makeni Ummie wlhy bazan iya rayuwaba, idan babu shi nima mutuwa zanyi, kitai makeni Ummie kiƙira wayansa, kice yazo gare ni ina buƙatarsa acikin rayuwata,, tana maganar ne cikin kuka.

Hawaye ne suka sauƙo daga cikin idanun Ummien, haɗi da sanya hanunta ta rungume Farhana'n sosai tanamai jin tausayin yarinyar acikin zuciarta.
Janye jikinta Farhana tayi daga na Ummie  ,  haɗe da bin Ummien, da kallon tuhuma , muryarta na rawa tace " Ummie kuka kuka kikeyi , Ummie...  " Farhana !!! ,, Abba yaƙira sunan ta adai dai lokacin dasuka ida shigowa cikin falon shida Dady,

Fuskokinsu tashiga bi da kallo, wanda ala momin damuwa dana tashin hankali,suka baiyana akansu, kasa koda motsawa tayi daga inda take , sai kafesu da'idanu da tayi.

" Abba ina Farhan ? ,, taje famawa Abba tambayar da baizataba,

kallon kallo Abba da Dady suka shiga mawa juna, 

"Yace zaizo gareni Abba kace masa yazo, ina jiransa, yace daga gidan su Jalal nan zai nufo, kaƙirasa kace mai ina jiransa" takai ƙarshen zancennata alokacin da ruwan hawaye ke gangarowa daga kan fuskarta.

Take tsananin tausayinta yacika zuciyar kowa dake falon, cikin rashin kuzari Abba yanufo gareta,   hannayenta yakama haɗe da zaunar da'ita akan kujera, cikin tausasa zance dakuma nuna kulawa Abba yace " haƙiƙa Allah shine ya haliccemu kuma shine yake raya mu , yake kuma kashemu, idan Allah ya ɗauki rayuwarka bawai baya sonka bane, haka idan yabarka aduniya, bawai yafi sonka fiye da wanda yaɗauka bane,  haƙiƙa Duk mai aikata aikin alkhairi mutuwa hutu ce agaresa,  duk kuma mai rai mamacine ,  Kiyi haƙuri Farhana haka Allah yatsaramiki,  kinyi rashin mahaifiya tun kina ƙarama, yanzu kuma kinyi rashin, babban masoyi kuma ginshiƙi a rayuwarki, kiyi haƙuri da abun dazan faɗa agareki, Farhan Allah yayimasa Rasuwa !!!! ,,

Azabure Farhana tatashi daga zaunen datake, kai tashiga kaɗawa haɗi da ja da baya, wani irin ihu ta kurma daya ratsa dodon kunnen duk wanda ke falon haɗi da zube wa awajen sumammiya.

*😭😭 Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, haƙiƙa nikaina naji mutuwar Farhan ba Farhana kaɗaiba, Allah yaji ƙanka da Rahama Farhan.😭😭*

*Allah kajiƙan musulmai, Ameen 👏🏻*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

MENENE MATSAYINA ? حيث تعيش القصص. اكتشف الآن