🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*MENENE MATSAYINA ?*
*(fictional story)**Written by* phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated To My Lovely Sister Maryam*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*INSTAGRAM* @phatymasardauna*Editing is not allowed 📵*
'''Ina kuke masoyana inayi muku albishir cewa na fara yi muku sabon book mai suna''' *SHU'UMIN NAMIJI*''' shidai wannan book ɗin yazo muku da labari maicike da salo na daban, kada ƙubari abaku labari,domin dai zan baje duk wata basira ta wajen ƙawata muku labarin yanda zai nishaɗantar daku...'''
*PAGE 5⃣3⃣to5⃣4⃣*
Wani irin ihu Beedah ta kwarara haɗe da cakumo Farhana daga jikin Hameed, wani kyakkyawan shaƙa tayi mawa Farhana, lokaci ɗaya idanunta suka birkice, tamkar mai junnu, ji takeyi inama da ace akwai wuƙa ahanunta, to da tabbas babu abun da zai hana ta lumawa Farhana acikinta....
Cikin tsananin ɓacin rai Hameed ya janye Beedah gefe, haɗe da yi mata wani irin kallo mai cike da tsananin gargaɗi, kuka kawai Beedah tafashe dashi domin kuwa wani irin malolon baƙinciki ne yazo maƙoshinta ya daskare, juyawa tayi da gudu tanufi ɗakinta, Farhana kuwa hanu tasanya ta gyara dogon gashinta daya zubo kan wuyarta, batare da tace da shi ƙala ba itama tabi ta gefenshi ta wuce, da wani irin mayataccen kallo yabita harta ɓacewa ganinsa, kansa kawai yagirgiza shima yayi bedroom ɗinsa yana mai rumtse idanunsa, da suka kaɗa sukai ja....
Farhana tana shiga cikin ɗakinta itama ta sake wani irin kuka marar sauti, bakomai ke da munta ba face tsananin kishin mijinta, duk wannan abun da tayi, tayi shine cikin daurewa dakuma danne zuciyarta, amma da za'a bincika zuciyarta tamafi Beedah jin zafin kishin Hameed ɗin...
Beedah ma dai kukanta tasha taƙoshi, lallai dole saita tashi tsaye, idan ba haka ba tofa tanaji tana gani ƴar iska Farhana zata sanya mata hawan jini....
Hameed kuwa wanka yayi haɗe da shirya kansa cikin wasu riga da wando ƴan kanti masu kyau da tsadar gaske, sosai kayan suka amshi jikinsa, babu abun dake fita daga kowani saƙo najikinsa face daddaɗan ƙamshin turarensa...
Kaitsaye ɗakin Beedah yanufa domin yana da buƙatar ganinta adaidai wannan lokacin,,
Haryanzu dai kuka yataradda ita tanayi tamkar wata ƴar 16 years, zama yayi a gefen gadon nata haɗe da sanya hannayensa duka biyu, ya jawota zuwa jikinsa, cike da lallashi yasoma shafa bayanta haɗe da cewa " Kada kibani kunya My Beedah, yanzu Farhana kike mawa kuka ? ƙanwar bayanki, yanzu idan dana barki kamata da kokuwa zakiyi kuyi dambe ko? kinaga idan har haka yafaru a tsakaninku bazata rainaki ba ? haryanzu fa keɗin amatsayin Aunty'n ta kike, bana so kina irin wannan halin kinji my dear " yaƙare maganar yana wani kwantar da murya..
Cikin kuka Beedah ta soma cewa " Kanaso zuciyata tabuga ne My dear ? ina tsananin kishinka tayadda banso kokaɗan naga wata banzar mace ta raɓeka, wallahi jinake zan iya kashe ko wacce mace a kan ka "
saurin rumtse idanunsa yayi alokacin data ambaci kalmar Banza mace, sam a ransa baiji daɗin kalamanta ba, amma dai yanzu farincikinta yake nema bawai akasin hakan ba,,,
Hanunta yakama suka nufi falo bayan ya lallaɓata ta share hawayenta..
Ɗakin Farhana yakuma nufa, saboda ya ƙirata domin so yake yayi zama dasu na musamman, ko da wasa baya ɗaya daga cikin irin mazan da zasu zuba idanu ana abun da'aka ga dama acikin gidansu, domin abun daya faru yau baison kwatan kwacinsa yasake faruwa har'abada...