🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*MENENE MATSAYINA ?*
*(fictional story)**Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated to My lovely Sister Maryam*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*Editing is not allowed 📵*
*PAGE 5⃣8⃣*
Yanashiga ɗakin da Farhana ke kwance, baiwani damu da cewa bacci take ba, yasungumeta, haɗe da soma juyi da'ita a tsakiyar ɗakin, kiss yashiga manna mata tako'ina,, a hankali ta buɗe idanunta, jin datayi ana juyi da'ita,, kyakkyawan murmushinsa yayi mata haɗe da ƙiran sunta " My Soul " itama murmushin tayi masa haɗe da neman yasauƙeta ƙasa, baiyi musu ba yadireta akan gado, haɗe da cewa "kiyi haƙuri na tasheki a bacci ko, tsananin murna ne yasanyani yin haka " kallon mamaki tabisa dashi haɗe da neman ƙarin bayani,,, hanu yasa yashafi gefen fuskarta cike da nishaɗi yace "Zansake zama father son a karo na biyu, inatsananin sonki Farhana, inakuma alfahari dake, kincancanci nayi miki komai a a rayuwata, don haka kifaɗamin duk abun da kikeso kome ne shi namiki alƙawarin zanyi miki shi " tsananin farinciki da jin daɗin da Farhana ta tsinci kanta a ciki bazai misaltuba, haƙiƙa tanason Hameed ɗinta, shiya sa take matuƙar so gudan jininsa ya rayuwa ajikinta, rungume juna sukayi cike da tsananin ƙauna, cikin murya mai kama da raɗa tace " kasoni fiye da komai a duniya, shine burina, ina fatan nayi rayuwa mai tsawo dakai anan duniya Appie na, inayi maka son da banama kowa irinsa, inasonka mijina !! " taƙare maganar tana maisake shigewa cikin jikinsa,, " inamai miki soyayyar da bata faɗuwa kokuma kwatantuwa My Soul, kinsamu Hameed kiyi yadda kikeso dashi,, ƴar dariya tayi haɗe da sanya bakinta ta ɗan ciji gefen kunnensa,, dariya suka sakeyi cike da nishaɗi suka rungume juna.....
Daga asibiti kai tsaye gidan Ummie suka wuce, domin tunkan a basu sallama Hameed yasanar da su Ummien cewa Farhana nada ciki, wayyo Allah daɗi zuciyar Ummie kamar tayi yaya, don haka kafun suƙaraso tuni ta dafa mawa Farhana ferfesun kaza wacce taji kayan ƙamshi, ta kumayi mata faten wake da vegetables wanda yaji busheshhen kifi, ga kuma daddaɗan kunun aya,, suna shigowa cikin falon, Ummie taje ta rungume ɗiyarta, cike da soyayya, itama Farhanan rungume Ummien nata tayi domin kuwa tayi missing ɗinta,, sosai Farhana taci faten wake da ferfesun kazan da Ummie tayi mata, harsai da abun yabamawa Hameed tsoro, ganin yanda Farhana ke ɗura abinci acikinta, batare kuma da tace ta ƙoshi ba, Zaiyi magana Ummie tace ya ƙyaleta haka wasu mata masu cikin keyi, arana nnan wuni Farhana tayi a gidan Ummie komai takeso shi Ummie ke dafa mata, Hameed kuwa ko kunyar Ummie bayaji, daga zaran Farhana tace wash, zai zaburo yayi kanta da tambaya "Menene ? Mai kikeso ? Meke damunki ? Zakici ka za ? Kokuma ka za zaki sha ? haka dai zaiyita tambayarta,,
Sai dare kafun Hameed da Farhana suka baro gidan Ummie, tuƙin mota ma haka yadingayi a hankali, wai kada ta jijjaga babynsa yasamu matsala, awannan dare Farhana taga tsantsar kulawa da tarairaya awajen Hameed, itakuwa narke masa tadinga yi.......
Wani irin special kulawa Farhana ke samu daga wajen Hameed, baya taɓa barinta taci abu ko ta sha, saiya tantance, musamman yaɗauko mata ƙwararriyar mai aiki, wacce ya yarda da'ita,,, komai na Farhana yazama na musamman, ko mai nata tattalashi akeyi, gudun kada taci abun da zai kuma cutar da'ita, hatta Beedah Hameed bai yarda da'ita ba, domin shi yanzu kwata kwata, ba wata yarda tsakaninsa da mutane, saboda wasu mutane munafukai ne, kayarda da mutum yazo yaci amanar ka,,,
lokacin da labarin cikin Farhana ya'isa kunnen Beedah baƙaramin tashin hankali tashiga ba, kuka tayi sosai, haƙiƙa tayi nadama baɗan kaɗanba, tasani cewa har'abada ta cuci kanta,, domin kuwa likita yatabbatar mata cewa magungunan data ɗauki tsawon lokaci tana sha, sun haifar mata da matsala a mahaifarta ba lallai ta haihu ba, saidai wani ikon Allah, lokaci ɗaya Beedah ta rame gaba ɗaya tasanya damuwa acikin rai da zuciyarta, sauƙinta ɗaya shine Hameed ya ɗan sauƙo daga fushin da yakeyi da'ita yana kulata amma, sam baya bata fuska kamar da, gaba ɗaya jitayi zaman Nigeria yafita akanta, don haka tasa akai mata visa, tawuce london, domin tanaso ta haɗu da ƙwararren doctor da zai sake duba lafiyarta,,,
cikin Farhana nada wata 4 bikin Latifa, yataso, nan suka shiga shirye shirye, anko ma kaɗai kala goma suka fitar, domin kuwa ɗan sarki Latifa zata aura, biki suka shirya gangariya nagani da faɗa, komai sunayinsa ne cikin kuɗi, babu wani alamar ƙaranta,, yautake kamu tunda safe Farhana kebin Hameed akan yabarta tatafi amma ya hanata waisai da yamma..
Kwance take akan faffaɗan ƙirjinsa yayinda idanunta ke alumshe kamar mai bacci,, hanunsa yakai kan tulin gashin kanta yasoma shafawa cike da ƙauna yace "My Soul !!" "Ummm" ta amsa masa da wata kasalalliyar murya,, gangaro da hanunsa yayi zuwa kan cikinta daya ɗan turo kaɗan, "Pls My Soul kokaɗanne ki barni naƙara kingafa ɗazu banƙoshi ba " yayi maganar da wata irin murya,, "Um um gaskia ni da zafi kakemin fa " tabasa amsa cikin shagwaɓa, " kiyi haƙuri amma yanzu bazan miki da zafi ba " "alƙawari?" "eh nayi alƙawari" yabata amsa yana mai kashe mata idanun sa ɗaya,, kyakkyawan murmushi tayi masa haɗe da sake shigewa cikin jikinsa,, riƙeta yayi ƙam a cikin jikinsa, yayinda ya haɗe bakinsu waje ɗaya, hot kiss suka shiga yi mawa junansu, sosai Hameed yayi romance ɗin Farhana, kafun suka faɗa wata duniya mai cike da nishaɗi a cikinta,,, yasamu gamsuwa yanda yakeso, haka itama Farhana taji daɗi domin kuwa baiyi mata da zafi ba,, Hameed kuwa daɗin dayaji bamai faɗuwa bane, domin ako wacce rana Farhana'nsa sake daɗi take, musamman ma yanzu da take da ciki, numfashinsa har ɗaukewa yake, a yayinda yajisa a babban fadarta....
Sosai tayi kyau cikin shigar wani tsadadden leshi dake jikinta, wanda yasha ɗinkin fitted gown, sosai kayan ya amshi jikinta, abunka da mai ƙaramin ciki, koda yaushe cikin walwali take, Hameed kuwa santin haɗuwar tata kawai yake, yayinda itakuma takeyi masa dariya,, dakansa yaɗauketa yakaita wajen kamun, tunda sukaje wajen kallo yakoma kansu, da wa ƴanda suka sansu dama waƴanda basu sansu ba, haƙiƙa Hameed da Farhana sunyi matuƙar da cewa da juna,, anyi kamu lafiya ankuma tashi lafiya,, duk yanda Farhana taso Hameed yabarta a gidan Ummie harsai angama biki ta dawo, ƙiyawa yayi, har baki Ummie tasanya amma yace sam bai yarda ba, dole Ummie ta ƙyaleshi, shiko yayi hakanne don yane ma ma ta sauƙi daga kace nacen mutane, domin wasu bakinsu gubane,,,
Ranan Asabar aka ɗaura auren Latifa da Angonta Naseer, ɗaurin auren yasamu halartan mutane da dama, bushe bushe kam ansha shi masu algaita sun busa, maroƙa ma kuma sunyi nasu,, ana ce da Latifa anɗaura aurenta, tafashe da kuka,, dariya kawai Farhana tashiga yi, domin sarai tasan Latifa ciki da bai, kukan munafurci kawai take yi zuwa anjima zata daina.... Aranan da aka ɗaura Aure da daddare aka shirya gagarumin diner, awani katafaren hall,, diner ya ƙawatu yanda ya kamata yayinda Big Brother da Big Aunty (Hameed & Farhana) suka nunamawa Latifa zallan gata, sunyi ɓarin kuɗi bana wasaba, domin kuwa su liƙinsu da dala sukayi shi, Atif ma ba'a barsa a baya ba, domin shima yayi mawa ƙanwar tasa gata sosai, kowa saida yayi mamakin irin yawan kuɗin da yayun amarya suka watsa mata,, ana gama diner aka wuce da amarya gidan Mijinta, bayan tasha nasihohi masu ratsa jiki daga wajen Ummie da Abba.......
Haka Farhana taci gaba da rainon cikinta, cikin kwanciyar hankali, domin kulawa take samu daga kowani ɓangare, baga Mijin ta ba, ba ga Ummien taba......
(Manage please..)
*14/October/2019*
*MRS SARDAUNA*