Page 33

2.5K 164 17
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
    
          *_MENENE MATSAYINA ?_*
                *(fictional story)*

    *Written by*
phatymerhsardauna
         *🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated to my lovely sister Maryam*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassocition*

       *WATTPAD*
@Fatymasardauna
      *INSTAGRAM*     @Phatymasardauna

 
*Editing is not allowed 📵*

*🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬*
*HAPPY INDEPENDENCE DAY*
*NIGERIA @59*
*GOMBE @23*
*🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬*

*(Ina miƙa godia ta agareki MARYAM A.I GITAL, My Meeragee, haƙiƙa keɗin tadabance, halaccin ki kuma yakai halacci, naji daɗi sosai a bisa sadaukarwa dakikayi agareni na littafin ki mesuna KOMAI NA DA LOKACI !! Allah ubangiji yaƙaramiki basira da hazaƙa, Allah ubangiji yasanya farinciki, maiɗorewa acikin rayuwarki, alkhairin Allah da rahamarsa, ya ruske ki ke da  magabatanki, aduk inda kuke, Allah yajiƙan mahaifa yahaɗamu dasu a gidan Aljanna Maɗaukakiya, Ameen thumma Ameen..)*

*PAGE 4⃣4⃣to4⃣5⃣*

Yaƙudura a ransa cewa  yau zaije yaɗauko matarsa, saidai ayi duk wacce za'ayi ...

Wanka yayi yashirya kansa cikin wani riga da wando na  black getziner mai matuƙar kyau da tsadar gaske, wandon irin pencil ɗinnan ne yayinda tsawon  rigan   ya kasance iyaka guiwarsa,    Sosai   kayan ya amshi faffaɗan jikinsa mai cike da burgewa,    baƙar hula yaɗaura akansa, yayinda toms ɗin ƙafansa ma yakasance baƙi, masha Allah gaskia Hameed yafito a matsayin cikekken *ABDOUL HAMEED ( servant of the Alloudable )* ɗinsa, tsadadden agogon diamond yaɗaura akan tsintsiyar hanunsa,  nikai na Hameed yayimin kyau sosai, abunka da farin fata acikin baƙin kaya (like Abbana)..

Kaitsaye asibiti yanufa, bayan yacika motarsa dakayan fruit  irin wanda maras lafiya ke buƙata,,    

Koda ya isa cikin asibitin ɗakin da aka kwantar da Farhana yanufa kai tsaye,   saidai me ? yanazuwa yatarar da ɗakin wayam babu su babu alamarsu,,   koda yagarzaya wajen Doctor, shaida masa yayi cewa anbasu sallama tunda sassafe. 

Sam bahaka yasoba, amma babu yanda zaiyi, dole dai yanzu gida zai nufa, saidai zuciyarsa kan tsananta bugawa duk sanda yatuno gamuwarsa da Abba, bazai ma sa kyauba..

Da sallama ɗauke a bakinsa yakutsa kansa cikin falon, babu kowa a falon, sai ƙaran T.V dakuma A.C dake tashi acikin falon,  hamdala yayi haɗi da godemawa Allah, da yasanya bai tarar dakowa acikin falon ba,    kansa tsaye yanufi ɗakin masoyiyarsa Farhana...

Tsaye take agaban tangamemen sif ɗin kayanta, daga ita sai wani pink towel ɗaure ajikinta wanda yatsaya iyaka cinyarta,  jikinta duk ruwa, da'alamun wanka tayi,   gaba ɗaya hankalinta yatafi wajen zaɓan kayan dazata sanya, hakan yasa bataji shigowarsa ba ...   

"Alhamdulillah !!!" yafaɗa cikin zuciyarsa a dai dai lokacin da 'i'danunsa sukai masa tozali da santala santalan cinyoyinta, masu ɗaukar hankali  dakuma firgita sha'awan duk wani lafiyayyen ɗa namiji,   a hankali yashiga takowa gareta cikin takun sanɗa, domin kuwa yalura da cewa batasan ma da shigowarsa cikin ɗakinba,     daidai sanda yaƙaraso bayanta, daidai lokacin itakuma tazame towel ɗin dake jikinta yayi ƙasa, "Ya salam"   gaba ɗaya daskarewa yayi awajen yayi suman tsaye, numfashin sa tsayawa yayi cak, domin kuwa haɗaɗɗiyar surar Farhana zata iya sanya ƙaramin jarumin namiji suma batare daya shiryawa hakan ba,       duk da cewa ba yau yafara ganin surar tata ba, amma gaba ɗaya yaɓata lissafi,     Farhana kuwa harzuwa lokacin batasan yana bayanta ba, kuma still tsaye take babu komai ajikinta,     jikinsa har rawa yake haka yaɗaura hanunsa bisa bayanta,   amatuƙar firgice tajuyo domin ganin maikeshirin faruwa da'ita, wani irin ƙara tasanya, wanda yaratsa kowani kusurwa dake cikin ɗakin...  Saurin jawota yayi zuwa jikinsa haɗe da manneta aƙirjinsa, hanunsa yasanya yatoshe ma ta baki,     

MENENE MATSAYINA ? حيث تعيش القصص. اكتشف الآن