Page 29

2.2K 165 11
                                    

   🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
    
          *_MENENE MATSAYINA ?_*
                *(fictional story)*

    *Written by*
phatymerhsardauna
         *🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated to my lovely sister Maryam*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassocition*

       *WATTPAD*
@⁨Fatymasardauna⁩

    *PAGE 3⃣6⃣to3⃣7⃣*

Yanzu shikenan Ummie nayi asaran ɗana dake  cikina,, wayyo Allah na.... Tadurƙushe awajen tana mai ruskar kuka...... Hanu Ummie tasa haɗi da ɗagota daga durƙushen da ta ke zuwa jikin ta  rarrashinta Ummie tashiga yi cikin sigar son kwantar ma ta da hankali.... "  Ya'isa haka daina kuka domin kuwa kuka babu  abun dazai haifar miki,, Ina roƙon  Allah daya bayyana  gaskiyan wannan al'amari,,  Ummie tana kaiwa nan azancenta ta nufi ɗaƙinta yayinda tabar Farhana tsaye tana zubar da ƙwalla........

Cikin tsananin damuwa Farhana takoma ɗakinta, wanda yake mallakinta alokacin da take  budurwa,,     takure kanta tayi waje ɗaya haɗe da soma rera kuka mai taɓa zuciya...Bakomai ke damunta ba sai zubewar da akace cikinta yayi sannan kuma wai ita ake zargi (wato ita akace tazubar dashi)  lallai duk wanda yayi ma ta haka yakasance azzalumi agareta, baikuma kyautawa rayuwartaba... Kuka  tasake rushewa dashi  asakamakon tunowa da tayi cewa lallai Hameed na fushi da'ita wanda hakanne kuma ya hanasa zuwa gareta.....Allah sarki Farhana kuka tayi sosai babu mai rarrashinta,, haka fuskarta tayi jajur yayinda idanunta suka kumbura suntum,,,  tana tsaka da kukan Allah yakawo ma ta bacci ya yi gaba da'ita,, (like my little bro Basheer sanda yake ƙarami  lol )..........

Zaune yake abakin makeken gadonsa yayinda yasanya duka hannayensa ya tallafi kansa dayayi ma sa nauyi,, damuwa ce fal acikin rai da zuciyarsa,, saurin ware manyan golding eyes ɗinsa yayi alokacin da tunanin pills ɗin daya faɗo da ga hanunta sanda ya ɗaga ta yazo ma sa,, dasauri yafice daga ɗakinnasa kaitsaye yanufi ɗakinta....

Ɗakin yananan kamar yanda suka barshi jiya domin kuwa har jininta dake kan tiles ɗin yabushe yayi baƙi,, gakuma pills ɗin yashe aƙasa.... Hanunsa na rawa yaɗauki maganin  *...........* shine sunan dake rubuce ɓaro ɓaro jikin  maganin  ( bazan rubuta sunan maganin ba saboda tsaro )  ƙara waro manya manyan idanunsa yayi bayan yagama karanta sunan maganin  " Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un !! Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un !!! haka yaita faɗa harsau uku yayinda hanunsa ke dafe da saitin zuciyarsa, daya kejinta tamkar zata fito waje ta tarwatse,, yayinda idanunsa ko ke fitar dawani irin zazzafan hawaye... Sake kallon magungunan yayi akaro na biyu,, tabbas yanzu zuciyarsa taƙara yardar masa da cewa Farhana dakanta tazubar masa da gudan jininsa,, ada yafara kokonto amma ayanzu yayarda dacewa dasaninta komai yafaru... Wani irin baƙin ciki da haushin Farhana ne suka cika mai zuciya haka yajuya yafice aɗakin jiki asaɓule.....

Cike da mamaki Beedah ke kallon yanda fuskar Hameed tayi jajur da'ita ga kuma kwalla nasauƙa akan fuskarsa abun dabata taɓa gani ba a iya tsawon rayuwarta dashi wato hawayensa... Cike da tsoro haɗi da mamaki ta ƙaraso garesa "My Dear...  Bai bari ta ida zance'n nataba  ya faɗa jikinta  haɗe da rungumeta ƙaƙam yana mai zubar da ƙwalla tamkar  ƙaramin yaro,,,,, 

"Maiyasa Beedah ? Maiyasa Farhana ta yi mini haka ? 

Sororo Beedah tayi tana kallonsa jin yanayi mata wasu irin tambayoyi marassa ma'ana wanda bakuma tada amsarsu  daƙyar ta'iya cewa " ban fahimci maikake nufi ba Hameed kayimini bayani maiyake faruwa ?

"Farhana tazubarmim da cikin ɗana dake jikinta abisa wani ɗan ƙaramin dalilinta na daban, maiyasa tayi mini hakan kokinsan yanda nakeji ajikina kuwa bazan.....  Saikuma yayi shiru haɗe da janye jikinsa daga nata kaitsaye yanufi ɗakinsa.......

MENENE MATSAYINA ? حيث تعيش القصص. اكتشف الآن