Page 24

2.8K 209 15
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
 
           *_MENENE MATSAYINA ?_*
                 *(fiҫтiоηӑι sτοrγ)*

       *Written by*
РнӑτγмεrнSӑrδαuпα
*🎈Mгs Sӑrδӑчηa🎈*

*Δεδicаτεδ to Mγ Loυεlγ sisτεг Мӑгӳӑм*

*🌈Kӑiηчшӑ Шriτεг Ӑssoҫiaτiοη*

~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~

*Wannan page ɗin dukansa kyauyane gareki my baby💖ta 💕mama💖 ngd sosai dakulawarki agareni, Allah ubangiji yabar ƙauna...*

*page 3⃣0⃣*

Beedah najin  alamar cewa sunfice acikin gidan, tasaki wani irin kuka mai sauti   haɗe da nufar ɗakinta da gudu,,  wayarta dake aje kan gado, taɗauka haɗi da  danna ma wa Aminiyarta Murja ƙira, don samun mafita akan bala'in dayake shirin tunkarota.....

Ɓangaren su Hameed kuwa kaitsaye asibiti suka nufa,    kasancewar tun kafun suƙaraso, yaƙira  Doctor Nura (babban likitan asibitin kuma abokinsa) yasanar dashi zuwan nasu,  koda suka ƙaraso cikin asibitin Nura dakansa ya zo  ya tarbesu ...

Bayan sun zaunane gaisuwa yabiyo baya,     cike da tsokana Nura yace da Hameed " Allah mai iko, amaryar da'ake ɓoyeta ba'aso muganta, yau sai gashi ankawo min ita har office ɗina,,  Nura  yaƙare zancennasa yana ƴar dariya.

Hararan wasa Hameed ya aika ma sa ha ɗe da sauya akalar maganar da Nura ɗin keyi, ta hanyar cewa " ba surutu nazo kayiminba  malam, ƙira doctor mace tazo tayimini checking ɗin Wifey na bata jin daɗi,,  

Saurin Kallonsa Farhana tayi jin   ya ambaceta da Sunan Matarsa akaron farko,  

Sarai ya ankara da kallon da ta yi ma sa amma sai ya matse, haɗi da cigaba da danna phone ɗinsa dake riƙe ahanunsa.

Murmushi kawai Nura yayi haɗe da ɗaukar telephone ɗin dake kusa dashi, wasu numbers yadanna, haɗi da kara telephone ɗin akan kunnensa...

Mintuna ƙalilan doctor Ruƙayyat tashigo cikin office ɗin,,     bayani Farhana tayi mata akan abubuwan datakeji,      batare da ɓata lokaci ba Doctor Ruƙayyat tace da Farhana tabiyota suje don taimata test...

Blood test Doctor Ruƙayyat tayimawa Farhana,    yayinda tace da Farhana takoma wajen mijinta, kafun result yafito..

Nura ne keta zuba zance, yayinda Hameed ke amsa ma sa jefi jefi, kasan cewarsa mutum marasson hayaniya dakuma yawan surutu,      itadai Farhana kwanciya tayi akan wani, kujera, yayinda idanuwanta kekan Mijinta, kowani motsi yayi tana kallonsa, hakanan ta tsinci kanta dason kallonsa...

koda Doctor Ruƙayyat takawo result ɗin, Doctor Nura tabawa,, kana  tayi ficewarta daga cikin office ɗin...

Murmushine ya bayyana a kan fuskar Nura,  bayan yagama karanta takaddan result ɗin Farhana dake hanunsa..

Hanu doc Nura yamiƙomawa Hameed haɗe da cewa " Congratulation aboki na,  inata yaka farinciki do min  matarka tana ɗauke da juna biyu na tsawon sati bakwai ,,

Cikin tsananin mamaki Hameed ke kallon Nura    " dagaske kake Nura ko wasa ? kanaso kace Farhana tana ɗauke da gudan jinina a  ciki'n ta ?    Hameed yayi tambayar cike dason samun ƙarin bayani akan maganar da doctor Nura yafaɗa..

"Ƙwarai kuwa Hameed Matar ka na ɗauke da cikinka na 7 weeks"  doc Nura yasake maimaita maganar tasa..

Take Hameed yazube aƙasa, haɗi dayin sujjada ya gode ma wa Allah abisa kyautar da ya azurtashi dashi,    wani irin tarin farinciki dabazai taɓa misalta wa ba, yake ji acikin zuciya da kuma ransa..

MENENE MATSAYINA ? حيث تعيش القصص. اكتشف الآن