🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)**Written by*
''' Phatymerh'''
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~[26 August 2019]~
*Wattpad*
@Fatymasardauna______________________________
*Thanks All my Wattpadian fans, ina alfahari daku comment ɗinku yana sani nishaɗi.**Nagode da Comment dakuma voted ɗinku.*
*Ina godia sosai sisters musammanma, Jiddab nd HafsaMuhammadHafsa, ana mugun tare 🤝🏻*
_______________________________
*Editing is not allowed 📵*
*Page 1⃣8⃣**Bayan Sati ɗaya*
Gaba ɗaya komai na Farhana ya sauya, kallo ɗaya za kayimata kafahimci cewa tana cikin damuwa.
Ido ta tsuramawa plate ɗin abincin dake aje gabanta, tamkar mai yin nazari ga me da abincin, amma a zahiri hankalinta da komai nata, yatafine izuwa tunanin masoyinta da yayi mata nisa na har abada, tsawon lokaci Ummi dake tsaye bakin ƙofar shigowa falon , ta ɗauka tana kallon Farhanan da'ayanzu ta naƙasta rayuwarta da yawan tunani,
Num fasawa Ummie tayi haɗi da sauƙe ajiyar zuciya, ta nufi inda Farhana'n take.Dafa kafaɗarta da ta ji anyine yasanya ta , saurin ɗago kanta don taga ko waye ,, ganin Ummie ce tsaye yasanya ta fashe wa da kuka, haɗi da rungume Ummien, , hanu Ummie tasanya bisa bayan Farhana'n, tashiga shafawa cikin alama ta lallashi,
ko kaɗan Ummie bata yi yunƙurin hanata kukan data keyi ba, saboda wani lokaci kuka rahama ne ga bawan daya ke cikin ƙunci,, saida tagaji dan kanta kafun ta tsagaita da kukan ta shiga sauƙe ajiyar zuciya..
Ganin haka
yasanya
Ummie kama hanunta suka zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon,
"Ba iya nutsuwarki nake soba Farhana, hadda hankalinki da kuma tunaninki, ya kamata zuwa yanzu ace, kin fauwalamawa Allah al'amuranki, kuka da damuwa basune zasu sanya kiji sauƙi acikin zuciyar kiba, bakuma sune zasu gusar miki da raɗaɗin rashin Farhan arayuwar kiba, kidawo cikin hankalinki Farhana, ki koma ga Ubangiji'nki ki ro ƙamawa Farhan, yafiyarsa da kuma rahamarsa, yafi ace ki zauna kina yimasa kuka, hakan ba bu abun da zai haifar, kin hana kanki ci da sha, duk sabo da mutuwan Farhan, so kike kema kikashe kanki ? ,, Ummie tatam baya.
"Zanyi matuƙar farinciki Ummie idan hakan ta kasance, nafiso nima na mutu , domin kuwa rayuwata bata da amfani matuƙar babu Farhan acikinta...."Ya'isa haka Farhana !! tun da ni ban'isa nafaɗa miki kiji ba, kici gaba dayi !!! Ummie tafaɗi haka cikin ɓacin rai, haɗe da tashi tanufi ɗakinta, tanajin kukan da Farhana'n ta fashe dashi, amma ko juyowa batayiba tashige ɗakinta, domin zuwa yanzu abubuwan Farhana sun soma bata haushi, sai kace akanta aka fara yimawa mutane mutuwa, gaba ɗaya ta hana kanta da ƴan uwanta sukuni.
Kuka sosai tayi kafun daga bisani tasanya hanu, tashare hawayenta, haɗe da jawo plate ɗin abinci'n tasoma tsakuran, kaɗan tanaci, jitayi magani ma yafiye mata abincin daɗi, amma bayanda ta'iya haka tashiga turasa cikinta, domin tayi amanna cewa idan har batasanyawa hanjin cikinta, abinci ba yau, to fa balalle ta'iya kaiwa gobe ba, saboda tsabar yunwa dake nuƙur ƙusanta.
Ahankali tatura ƙofar ɗakin haɗe dayin sallama, cikin sassanyar muryarta da a yanzun ta dashe saboda yawan kuka..
Ummie dake zaune gaban dressing mirror , ta amsamata a taƙaice kuma ci ki ci ki..
jikintane yayi sanyi, dajin yanda Ummie ta amsa ma ta , domin tafuskanci har yanzu fushi Ummie keyi da'ita.Kaitsaye wajen Ummien tanufa haɗi da ɗaura kanta, bisa kafaɗan Ummien, cikin muryar ta mai sanyi da tausayi, tace " kiyi haƙuri Ummie dan Allah kada kiyi fushi dani, ki yafe min Ummiena, fushinki a gareni haɗarine,, kafun takai ƙarshen zancennata ma tuni ruwan hawaye sungama wanke mata fuska.
Tsananin tausanyinta ne yadaki, zuciyar Ummie , take itama zuciyarta, ta karye,
Hanunta ta sanya haɗi dajanyo Farhanan jikinta , ƙoƙarin gusar mata da damuwarta Ummie tayi, ta hanyar bata shawarwarin dazasu taimakamawa rayuwarta, dakuma nusar da'ita kan cewa tayi haƙuri da rayuwa aduk yanda taka sance mata.. Haka Ummie tayi ta bata shawarwari har sai da ta fuskanci taɗan sake ranta.Cike da tarin mamaki Ummie ke kallon Abba, kafun daga bisani ta sauƙe ajiyar zuciya haɗi da cewa
" Banƙi ta ta ka ba Alhaji amma agaskia maganar auren Farhana, yanzu da am bashshi, saboda tana cikin wani hali, baikamata kuma ace ankawomata wani maganar da zai sake tada ma ta da hankaliba,, Ummie tayi maganar cike da al'ajabin halin da Farhana zata tsinci kanta idan labarin ya'isa ga kunnenta.Murmushi Abba yayi irin nasu na manyan dattawa, haɗi da yimawa Ummie ƙarin bayani da kuma nusar da'ita dalilan daya sanya, yake son Auren Farhana'n kar yawuce 2 weeks masu zuwa .. Duk dacewa Ummie ta fahimcesa, amma tana matuƙar tausayin ɗiyarta da kuma halin rayuwa, da zata fuskanta.
Balaifi zuwa yanzu kam Farhana ta ɗan saki jikinta, domin tana cin abinci, har taɗi da Ummie sukan ɗanyi, saidai duk sanda ta tsinci kanta ita kaɗai a ɗaki, takan zama tayi kuka bana wasa ba.
Yanzuma kwance take kan doguwar kujera, yayinda tayima wa kanta matashi da cinyar Latifa, gefe kuwa Bro Atif ne yaza ge sai basu labaran nishaɗi yake, burinshi kawai shine Farhana taji daɗi, kuma tayi farinciki, balaifi kuma ya lura cewa labaran nashi sun sata nishaɗi...
Ummie ce tashigo cikin falon fuskarta cike da tarin fari'a, bata ko kalli Atif dake mata maganaba, ta kama hanun Farhana suka nufi hanyar fita daga falon,, tun data ga Ummie taji wata irin faɗuwar gaba, haɗi da tsinkewar zuciya wanda bata san daliliba...
Kaitsaye part ɗin Abba taga sunnufa, stiil Ummie nariƙe da hanunta bata sake ba. Abba da Dady haɗi da Hajiya Kaka suka tarar acikin falon, take taji faɗuwar gabanta ya tsananta.. Kusa da Ummie ta zauna, haɗe da soma ƙaremawa falon kallo tamkar wata baƙuwa.
Ƙamshin turarensa shiyafara Ziyarta falon kafun shi ya samu ƙarasowa.. Saurin rumtse idanunta tayi haɗe da kawar da kanta gefe, Allah yasani ta tsani ƙamshin turaren da kuma mamallakin turaren,, sam ko ganinsa bata sonyi.
Kamar koda yaushe haka yashigo cikin falon, fuskarsa ba yabo ba fallasa, haka yake koda wani lokaci abune mawuyaci, kagane farincikinsa, ko baƙin cikinsa,, Miskilin mutum ne na gaske ...
Saida ya gaishe dasu Dady kafun yanemi, waje yazauna haɗe da duƙar da kansa ƙasa..
Abbane yayi gyaran murya haɗe da kallon Farhana , data takure waje ɗaya, da hanu yayi mata alama akan tazo, cikin sanyin jiki tamiƙe ta ƙarasa garesa haɗi da zama akusa da ƙafafunsa ta duƙar da kanta ƙasa.
Gyara zama Abba yayi haɗe dacewa " Hameed da Farhana, inaso ku bani aron hankalinku kuji mai zan faɗa muku, amatsayina na mahaifinku, inada iko kuma da hujjar da zan yanke kowani irin hukuncine, akan Kowannenku ... Abba bai kai da ida maganar ta saba,
zuciyoyi biyun suka shiga tsalle da bugawa, wani irin tarin fargaba da tsoro shiyayi nasaran ɗarsuwa azuciyar kowannensu.....
((Topa komai Abba zaice oho 🤷🏻♀))
Whatsapp no+2340706939924
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇