🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)**Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~{24 Satutday August 2019}~
*Wattpad*
@Fatymasardauna*Editing is not allowed 📵*
*Page 1⃣5⃣to 1⃣6⃣*
Akiɗime dukansu sukayi kanta, Ummie ce tashiga ƙiran sunan Farhana haɗi da jijjagata, kuka Ummie tafashe dashi na tsananin tausayin Farhana , batare da ɓata lokaciba Abba ya umarci Ummie data kaita ɗaki , zai ƙira doctor yazo yadu bata .
drip doctor yaɗau ramata haɗi da bata wasu magun guna yace idan tafarka su bata, domin zata iya farkawa akowani lokaci.
Gaba ki ɗaya Ƴan bikin suna cikin Alhini da kuma tausayin Farhana, domin zuwa yanzu babu inda labatin rasuwan Farhan bai ratsaba, ta sanadiyar haɗarin mota da yayi, take kuma ya rasu batare da ko hospital an kaisaba.
Daga gidan su Farhan kuwa koke koke shiya maye gurbin farin cikin dasuke ciki, a ɗan awannin baya da yawuce, sosai mutuwar Farhan tataɓa ahalinsa, domin shi ɗin mutum ne maison kyau tatamawa ƴan uwansa, haka kuma mutum ne mai raha da shiga zuciya, Momynsa kam tayi kuka harta gode mawa Allah , domin duk cikin ƴaƴanta tafi ƙaunar sa fiye da kowanne, kasan cewarsa mai biyayya agareta. Haka ƴan uwansa suna ji suna gani akayi masa sallah, aka kuma wuce dashi gidansa na gaskia, inda kowannenmu sai yajesa (Allah yasa mucika da imani.)
Tun ana sa lokacin farfa ɗowar Farhana, haddai suka dangana ga Allah, domin kuwa har dare ya raba Farhana bata ko motsaba , haka Ummie taraba dare tana gadin ta waiko zata farfaɗo, amma shiru.
Washe Gari
Zuwa yanzu kam gaba ɗaya hankalin su Abba da Dady yagama tashi, domin dai haryanzun Farhana bata dawo cikin hayya cintaba, saida doctor Hassan yasake yi musu bayani "kan cewa zata iya farfa ɗowa akowani lokaci sannan suka ɗan samu nutsuwa acikin zuciyoyinsu ,,
kalaman Abba sune abun dasuka fara dawowa cikin ƙwaƙwal warta, wani irin ƙara tayi haɗi da ƙoƙarin fusge alluran dake hanunta, wanda tanan ruwan da'aka sanyamata kebi yana shiga cikin jikinta,, saurin riƙeta Ummie tayi haɗi da cewa " kinutsu kada kiji mawa kanki ciwo,, jin muryan Ummie datayi ya doki dodon kunnenta yasanyata , fashewa da wani irin matsanancin kuka haɗi da faɗawa jikin Ummien, rungumeta Ummie tayi tsam ajikinta , tashiga shafa bayanta a hankali , burin ta baiwuce Farhanan tasamu nutsuwaba.
" da gaske ne Ummie Farhan ɗina yarasu, da gaskene bazan sake ganin saba ? kitayar dani daga wannan mumnunan mafarkin danake dan Allah Ummie kitasheni kicemin mafarki nakeyi, tun kafun nayi hauka, kitasheni kice mafarki nake dan Allah Ummiena takai ƙarshen zancennata tana mai rushewa da kuka, ba Ummie ba hatta Atif da Latifa da suke tsaye bakin ƙofar shigowa ɗakin, saida suka fashe da kukan tausayin ƴar uwartasu, hanu Ummie tasa tashare hawayen dasu ka sauƙa kan kuncinta, cikeda rarrashi ta ƙara jawo Farhana jikinta haɗi dacewa " kiyi haƙuri Farhanatu haƙiƙa duk wani mai rai sai ya ɗanɗani mutuwa, tabbas jarabawar kice tazo ahaka, babu kuma wanda ya'isa yasauya tsarin Allah , kiyi haƙuri ki ɗau dangana domin kuwa b....... bata bari Ummie ta karasa zancen nataba , tayi saurin fusge jikinta daga na Ummie haɗe da miƙewa tsaye, duk da kuwa cewa juwa na ɗibanta,
" Jarabawa ! Jarabawa !! fa kikace Ummie maiyasa jarabawata zata zo ahaka ? mai yasa jarabawata zata nisantani da abun sona ? wace kalan ƙaddara ce wannan ? mai na aikata wa u.......
" ya'isa haka Farhana, kada zafin mutuwa yasanya ki saɓi Ubangijinki, wannan bashine tar biyan dana baki ba !! ,, Ummie tafaɗa cikin ƙaraji, domin sam batason zafin mutuwar yasanya Farhana kasa karɓan ƙaddararta."Ina roƙon Allah yasanya haryanzu mafarki nake , domin kuwa bazan iya cigaba da rayuwa ba idan babu kai, kadawo gareni Farhan, kada katafi ka barni kokamanta cewa yaune ranar damuketa fatan tazo garemu, kasha faɗamin cewa Abadan munatare, maiyasa sai yanzu zaka tafi kabarni ? maiyasa baka kama hanunaba muntafi tare ? maiyasa zaka barni acikin duniyar da bata da amfani a gareni ? bazan rayu in babu kai ba Farhan , ina buƙatar ka acikin rayuwata kaine garkuwata .... take kuma duhu ya mamaye idanunta haka tatafi luuu ta zube aƙasa bata ko numfashi. Ummie da sauri tayi kanta, tana ƙiran sunanta , batare da ɓata lokaciba Ummi taɗauki wayarta haɗi da danna mawa Abba ƙira.
Ajiyar zuciya doctor Hassan yayi, bayan yagama checking ɗin Farhanan, cikin ƙarfafa guiwa yace " Haƙiƙa sai kunyi ta katsantsan wajen kula da lafiyarta sbd mutuwar tashiga jikinta sosai, haka kuma tana buƙatar hutu na tsawon 2 days so hakan bazai samu ba dole sai dai, idan bata cikin hankalinta kada kudamu, nayi mata alluran dazasu taimaka wajen bawa jikinta, nutsuwa da kuzari, zata iya kaiwa gobe bata farkaba ,dazaran tafarka kuma zansake yimata wani alluran , because tana bu ƙatar nutsuwa sosai . Godiya sosai Abba da Dady sukayi mawa doctor Hassan , kafun yayi musu sallama yatafi .
Koda labarin rasuwan Farhan ya'isa ga Hameed, baiji koda ɗigon tausayin farhana aransaba, saima sab goginsa da yacigaba dayi, batare da damuwan komai acikin ransaba, duk da kuwa yasan cewa Farhana na kwance ba lafiya.
Kamar yadda dr Hassan ya faɗa hakan ce taka sance domin washe gari Farhana, tana farfa ɗowa yasake yimata alluran bacci.
Hawaye ne kawai ke gangarowa daga ida nun ta, zuwa yanzukam tagama aminta cewa " Farhan ya mutu ya barta, takuma kudurta aranta cewa rayuwa mai daɗi yaƙare agareta, tana matuƙar son Farhan ɗinta fiye da yanda take son kanta, amma haka Allah ya ƙaddara mata, baza su rayu tareba, kuka mai sauti tafashe da shi asakamakon tunowa da kalamansa masu daɗi agareta datayi, daidai lokacin Ummie tashigo cikin ɗakin,
cike da kulawa Ummi takamo hannayen Farhana'n haɗi da cewa " kiyi haƙuri Farhana ki ɗau ƙaddararki aduk yanda tazo miki, idan kikayi hakan saikiga Allah ya musanyamiki , da mafi alkhairi agareki ,,
" Nagama soyayya aduniya Ummie, nama tsani duk wani namiji da zai kusantoni , da kalmar soyayya , bazan taɓa yin aure ba Ummie tunda dai narasa Farhan, to Ummie bazan kuma yin soyayyaba ,, Farhana tayi maganar cike da raunin zuciya.
"kidaina faɗin haka Farhana, yakamata ne kizama mai tawakkali dakuma yarda da ƙaddara , zakiyi Aure Farhana insha Allah nan bada jimawaba,,
Wani irin kallo Farhana kejifan Ummie dashi, mai ɗauke da alamomin tambaya.
Sorry kuyi manage yau bansamu enough time nayi typing ba , wannan ma da ƙyar nayishi ,👏🏻
Whatsapp no
+23407069399224
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇