🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)**Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~{27 August 2019}~
*Wattpad*
@Fatymasardauna*Editing is not allowed 📵*
*Page 1⃣9⃣*
Batare da Abba ya lura da halin da suke ci ki ba yaci gaba da cewa..
" kuyi haƙuri da hukuncin da na yanke a ga me daku, haƙiƙa Mamana (Farhana) kin haɗu da jarabawa da kuma ƙaddarorin rayuwa, kinrasa mahaifiya tsawon shekaru, yanzu kuma kinrasa mutumin da yakasance Garkuwa agareki,, nazauna nayi dogon nazari na kuma ga bai kyautu ace munbarki hakaba, yana da kyau musa ma miki abokin rayuwa, saboda samun nutsuwarki,, da fatan bazaki bani kunya ba ?
Gaba ɗaya kalaman Abba sun ɗauremata kai, domin sam bata fahimci mai yake nufi ba.. Maganar Abba'nne yasake dawo da'ita cikin hankalinta, inda yake cewa
" Dady,Hajiya Kaka, Ummie, inaso kuzama shaida cewa nabamawa ɗana *Hameed* Auren ƴata *Farhana* wanda za'ayi nanda Sati biyu masu zuwa insha Allah..
Tashin hankali wanda ba'asa masa rana,, Jin maganganun Abban sukayi tamkar sauƙan guduma acikin kawunansu..
Hanun Farhana Abba yakamo cike da kulawa ya ce da'ita " haƙiƙa nasan balallene kiji daɗin hukuncin dana yanke akanki ba, amma nasan cewa ke ƴa ce mai biyayya ga mahaifanta, inada tabbaci kuma bazaki watsamin, ƙasa a ido ba, ban yanke hukunci saboda son zuciyata ba, sai domin farincikinki, amma matukar kikace ba kyaso, tofa bazan miki dole ba, kada kuma kiji nauyin kowa da ke cikinmu, kisanar dani abun dake cikin zuciyarki, idan ba kyaso bamai miki dole...Ganin dayayi bakinta yana motsawa, alamar akwai abun data keson furtawa,
yasanyasa sakin wata munafukar murmushi datafi kuka ciwo, haɗi da cewa.
"Alhamdulillahi, haƙiƙa kai mahaifine agaremu, kanada haƙƙin dazaka yanke kowani, irin hukunci ne akan mu, saboda haka dagani har Farhana mun'amince, zamu cika umarninka da yardan Allah babu kuma wanda zai saɓamaka acikinmu,, yakai ƙarshen zancen nasa still yana wannan munafukin murmushin nasa dake ƙunshe da ma'anoni dayawa..
Murmushin jindaɗi Abba yayi, haɗe da godemawa Allah daya basa ƴaƴa masu biyayya agaresa, nanfa kowa dake cikin falon yashiga, sanya musu albarka da nema musu zaman lafiya da juna, Hajiya Kaka kam babu wanda yakaita murnan, kasan tuwar hakan ,,
Farhana kuwa komai nata daina aiki yayi, yayinda tazura masa manyan idanunta da suke zubar da ruwan hawaye, kallonsa take cike da tarin mamaki, duk da cewa shi baiko kalli, inda take ba, tabbas murmushin data gani akan fuskarsa ma kaɗai, ya tabbatar ma ta da cewa yashiryamata wata ƙulleneniya..
Lura da Ummie tayi Farhanan bata cikin nutsuwartane, yasanya ta kama hannayenta suka fice daga cikin falon. Kai tsaye ɗakinta, tanufa da'ita ..
Ummie nafita daga ɗakin. Farhana tarushe dawani irin kuka mai ban tausayi, da tsuma zuciya, kuka take sosai baji bagani, tabbas mutuwan Farhan yajanyomata tonon asiri, lalle ta yarda cewa mutuwar Farhan shine, babban ƙaddararta a rayuwa, tunda gashi ana shirin haɗata aure da babban maƙiyinta Hameed. a ranan Farhana tayi kukan dako sanda labarin mutuwar masoyinta Farhan ya isketa batayi shiba ,, a ta ƙaice dai saida wani zazzafan zazzaɓi ya sauƙa ajikinta, a sakamakon kukan da tajima tana ruska, har yazamana bata ko iya ɗago kanta saboda, tsabar ciwon kai da zazzaɓi.Tsabar tashin hankali ko ganin gabansa bai iyawa, da ƙyar ya iya kai kansa, part ɗinnasa, kaitsaye bedroom ɗinsa yanufa, yana shiga yasoma watsi, da duk wani abu da yayi arba dashi acikin ɗakin,, stull ɗin dake aje tsakiyar ɗakin, yaɗauka haɗi da wurgi da shi, take ƙaran fashewar tangamemen dressing mirror'n dake kafe jikin bangon ɗakin, ya ratsa kowacce kusurwa na ɗakin, domin kuwa stull ɗin akansa yasauƙa . .
gaba ɗaya yabirkice, idanuwansa sunkaɗa sunyi jajur da su, yayinda bakinsa ke fitar da hucin zazzafar iska,
sam baita ɓa tunanin wannan tashin hankalin zaitun karo saba, wani laifi ya aikatamawa Abba haka, da zai haɗa aurensa da Farhana ? yarinyar data zama tamkar karuwan gida, yarinyar daya kamata da wani ƙato yafi sau a ƙirga, mene sunan sa kenan idan ya auri Farhana " Mijin Karuwar gida " wata ɓangare na zuciyarsa tasanar dashi hakan, da ƙarfi yace " No ! noo !! nooo !!! hakan bazai taɓa faruwa daniba, bazan taɓa zama mijinki ba Farhana, na tsaneki ! banasonki !! bana ƙaunarki !!!, Abba mai yasa kayanke mana wannan hukuncin ? Abba why !!! ? yakai ƙarshen zancennasa cikin ƙaraji, da kuma ƙunar zuciya.
Zama yayi abakin gado, haɗi da rumtse idanunsa, babu abun dayake hangowa acikin idanun sa, face lokacin daya ganta kwance cikin ƙirjin Farhan, yana kissing ɗinta, saurin datse lips ɗinsa yayi, alokacin da hawaye suka sauƙo daga cikin idanunsa zuwa kan fuskarsa, wutar tsanar Farhana ce, kawai ke ruruwa acikin zuciyarsa .. Wani irin mugun murmushi yayi, a lokacin da zuciyarsa tagama haɗa masa tarkon, dayake son jefa Farhana ciki, yajima yana saƙawa da kuncewa, kafun daga bisani ya miƙe haɗe da rage kayan jikinsa ya wuce bathroom..Baƙaramin ruɗewa Ummie tayi ba, alokacin da ta zo ɗakin Farhana tataradda ita cikin mawuyacin hali, tabbas dama tasan hakan zai iya, faruwa da Farhana'n kasan cewar har yanzu, tana cikin al'ajabin da kuma jimamin rashin masoyinta.. Koda dr.Hassan yazo allurai da magunguna yayi mata, baji mawa tasamu wahalallen bacci yayi gaba da'ita.. Kafun yatafi saida yasake jaddadamawa Ummie cewa akiyaye shiga damuwarta, gudun samun matsala,, godiya Ummie tayi masa kafun sukayi sallama...
Ahankali tasoma buɗe idanunta, da suke cike da tarin ƙwalla. " Sannu Farhana kintashi ?,,
muryan Ummie yadoki dodon kunnuwanta. Kai kawai ta'iya gyaɗawa alamar "eh" domin sam batajin ƙarfi acikin jikinta.. datai makon Ummie tayi wanka, haɗi da sanya doguwar riga marar nauyi. Saida Ummie tasanyata agaba kafun taci abinci, haɗi da komawa ta kwanta...Hanunta Ummie tariƙo cike da tausayi haɗi da ƙarfafa guiwa ta soma cewa " Haƙiƙa bani na haifekiba Farhana, amma soyayyar da nakeyi miki, bazan iya misaltataba, inayi miki soyayyar da banamawa ƴata ta cikina wato Latifa, nice nan naraineki tsawon sheƙaru 20, dan haka nafi kowa sanin halayenki, nasan abun da kikeso da kuma wanda bakyaso, nasan farincikinki nakuma san akasin hakan, kamar yadda nake matsayin uwa agareki, haka nakeso nacigaba da kasancewa agareki, har gaban abada, kimanta cewa nina haifi Hameed, kisanar dani sirrin zuciyarki, nasan a yanzu babu soyayyar Hameed a zuciyarki ko ɗigo, amma inaso ki sanar dani cewa "zaki iya rayuwar aure dashi ko a'a? kada ki ɓoyemin Farhana, amatsayina na mahaifiyarki"
Wasu zafafan hawayene sukayi nasaran, gangarowa daga cikin idanun Farhana, amma saitayi saurin sakin murmushi haɗi da cewa " Idan Farhana zataƙi kowani namiji aduniya, to baza tataɓa ƙin yayanta kuma ɗan uwanta ba, bazan taɓa bijiremawa Abba ba Ummie, saboda inason Abbana, kowani yakawomin ba Yayana ba, zan Auresa Ummiee.... Kukane ya hanata ƙai ƙarshen zancennata, kawai saita faɗa jikin Ummie tasaki kuka mai taɓa zuciya......
Follow me...
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇