🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)**Written by*
phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated to my lovely sister Maryam*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION*
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassocition*
*WATTPAD*
@Fatymasardauna
*PAGE 3⃣4⃣to3⃣5⃣*Wani irin ƙara Farhana tasanya alokacin da cikin ta yashiga wani irin murɗawa tamkar hanjin cikin nata zasu tsinke,, cikin tsananin jarumta haɗi da juriya tatattaro duk wani ƙarfin daya rage ma ta, ahankali tashiga takawa har zuwa ɗakinta... Tana kaiwa tsakiyar ɗakin wani irin juwa da kuma ciwo mai tsanani ya zo ma ta take ta zube awajen haɗe dafara ambaton sunayen Allah daya kawo mata agaji ...Wani irin ciwo mararta keyi ma ta wanda takeji tamkar ana zare ranta,,, lokaci guda taji wani irin abu mai ɗumi yana bin ƙasanta, take kuma numfashinta ya ɗauke gaba ɗaya saboda tsantsar azaba......
Hameed ne zaune acikin katafaren office ɗinsa mai kama da aljannar duniya,, wasu files dake gabansa yake dubawa amma kwata kwata hankalinsa baya jikinsa,, wani irin faɗuwar gaba yakeji ga shi ya ƙira wayan Farhana har 4 missed calls amma batai picking ba gaba ɗaya ji yayi hankalinsa yakoma gareta jikinsa yana basa Farhanan sa ba lafiya take ba.... Car key ɗinsa ya ɗauka kaitsaye yafice daga cikin office ɗin, ko sauraran sectary yarsa da take yi masa magana baiyi ba.......
" My Dear !! My Dear !! Soul Mate !!! Where are you ??
tun daga bakin ƙofar falon yashiga kwaɗa ma ta ƙira. amma shiru, babu ko motsinta... dan haka kaitsaye yanufi ɗakinta.....
Cikin matuƙar tashin hankali da kuma firgita idanunsa kebin jinin dake malale akan saman tiles da kallo har zuwa inda Farhana ke yashe bata da alamar rai ajikinta....
Cike da tashin hankali yaƙarasa gareta, sungumarta yayi zuwa ƙirjinsa haɗi da sa hanunsa yana mai bubbuga ƙuncinta haɗe da jijjiga ta " Farhana ! Farhana !! kitashi dan Allah ki buɗe idanunki Yaya Hameed ɗinkine yazo, mai yasa meki Farhana ? waya taɓamin ke ? kitashi dan Allah ,, yaƙare maganar hawaye na ambaliya akan fuskarsa... Ganin ko motsi batayi ba yasanyashi kurma wani irin ihu da ya ratsa kowani kusurwa dake cikin ɗakin.... jijjigata yaci gaba da yi yana kuka tamkar ƙaramin yaro.... Kamar wanda aka tsikara haka ya miƙe daga durƙushen daya ke haɗe da sanya hanunsa yaɗagota jikinsa... Wani abune yafaɗo daga hanunta wanda yaɗauki hankalinsa... sachet ne na wasu pills guda biyu,, baiko damu da duba wani irin pill bane ya nufi hanyar fita da sauri yayinda take rungume aƙirjinsa,, gaba ɗaya jinin dake bin ƙafofinta yagama ɓata masa farar suite ɗin ɗake jikinsa..... Cikin mota yasanyata haɗe da yi mawa motar key, batare da yabari mai gadi yagama wangale masa gate ɗin gidanba yafigi motar tasa da wani irin gudu yafice acikin gidan,, wanda hakan ya matuƙar tsorata Malam Lawal mai gadi domin ko da dukkan alamu ba lafiya ba.....
Wani irin gudu Hameed keyi tamkar zaitashi sama babu ruwansa da wanda ke gabansa ko yake bayansa, saidai duk wanda yaga Motar Hameed nashirin hallaka sa ya kauce ma sa amma badai Hameed ya kauce ba saboda baya ma cikin nutsuwarsa baki ɗaya burinsa kawai yagansa cikin asibiti......
Kan Emergency bed aka ɗaura Farhana yayinda kai tsaye akawuce da'ita cikin A&E gaba ɗaya manyan doctors ɗin asibitin su suka duƙufa akanta domin ceto rayuwarta.... Hameed kuwa dake tsaye agaban ɗakin, gaba ɗaya yakasa zaune yakasa tsaye hankalinsa a matuƙar tashe yake, fatan sa ɗaya shine Allah yasa bawani mummunan abu bane yafaru da farhanan sa... yana nan tsaye tamkar zararre, Abba da Ummie haɗe da Hajiya Kaka suka ƙaraso garesa,, cikin tsananin tashin hankali Ummie ta soma cewa " Hameed ina Farhana mai ya samu ƴata innalillahi wa innalaihirraju'un,, taƙare maganar lokacin da kwalla yacika idanunta...