🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)**Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~{28 August 2019}~
*Wattpad*
@Fatymasardauna*Editing is not allowed 📵*
*Page 2⃣0⃣*Rungumeta Ummie tayi tsam, a ci kin jikinta haɗi da shafa kanta " haƙiƙa kincika ƴar albarka Farhana yanzu na tabbatar da cewa kin riƙe tarbiyan dana baki, bakiyi watsi da shiba, Allah yasanya albarka da aminci haɗi da so da ƙauna acikin *Tarayya* 'nku da Hameed, Allah yayi miki albarka, yakuma faranta ranki tamkar yadda kika faranta namu ran " Ummie tafaɗa cike da jin daɗin amincewar Farhana'n
Murmushin daya zame mata dole tayi, haɗi da sake rungume Ummien tace " Ameen Ummiena keda Abba kunwuce haka a wajena ,, miƙewa Ummie tayi haɗi da cewa tana zuwa, tafice a ɗakin. Ummie nafita Farhana ta rushe da kuka, wani irin ciwo da raɗaɗi take ji acikin zuciyarta amma yaza me ma ta dole ta amince da zaɓin iyayenta, ko da hakan nanufin rasa ranta , baza ta taɓa bijiremawa maganar Abba ba, domin shi ɗin yayi ma ta abun da a duniya babu wanda yayi ma ta shi. Ya nuna mata soyayya tsa gwaransa, duk da cewa ba shine mahaifinta ba amma yabata ilimi, tarbiyya, haɗi da kulawa, uwa uba kuma Ummie wacce ta za me mata uwa ɗaya tamkar dubu, batason ganin ɗigon damuwa ya bayyana akan fuskarta, ta shaida cewa Ummie tsananin, soyayya, take yi mata, tun tana yarinya har kawo yanzun, Ummie bata taɓa musguna mawa rayuwarta ba, bakuma ta bari wani ya musguna mata,, me sunanta kenan idan harta butulce masu, ta hanyar ƙin auren ɗansu, duk da cewa shiɗin yakasance maƙiyinta, amma bazata ƙi mawa iyayenta biyayya sabo dashi ba.. Hanu tasanya akan fuskarta, haɗi da share hawayenta, ta ɗaukar mawa kanta alƙawari'n cewa zatayi biyayya ga mahaifanta, zakuma ta cigaba da roƙamawa Farhan ɗinta gafaran Ubangiji, amma tasan cewa abune mawuyaci zuciyarta, tasake son wani namiji a duniya, bayan Farhan ɗinta...
Cikin tsananin tashin hankali da ruɗani, Beedah ke kallon Ummie , cikin sarƙewar murya haɗi da tashin hankali tace "Wallahi bazai taɓa yiwuwaba, bazan taɓa amincewa ba, Hameed nawa ne ni kaɗai, bazan kuma taɓa yarda wata banza ta mallake shi bayan niba, dama najima da sanin cewa ba sona kukeyiba, shiyasa kuka ɓullo da maganar ƙarin Aurensa, amma zanyi maganin abun, domin ni Beedah ba irin matan nan bane da ake mawa kishiya. Tana kai ƙarshen zan cennata tafice acikin falon tamkar kububuwa,,
sam Ummie batayi mamakin rashin kunyar da Beedah tayi mata ba, domin ita tajima da gane cewa " yarinyar bata samu kyakkyawan tarbiya ba, bata kuma iya girma ma nagaba da ita ba, kuma Aurene dole sai anyishi, koda hakan nanufin barin Beedah gidan...
Tanashi ga cikin bedroom ɗinta, tashiga watsi da kayan shafanta dake, gaban dressing mirror haɗi da cewa " ƙaryane wallahi, bazai taɓa yiwuwaba indai ina da rai , Hameed bazai taɓa yin Aure ba daga kaina ya rufe, babu wanda ya isa ya rabani da mijina, natsaneki Farhana ! natsaneki, tsana mai tsanani kuma ni ce nan ajalinki, matu ƙar ki ka auri mijina !!!
tana maganar ne cikin ihu da ƙaraji haɗi da buge buge, tamkar wata mental problem, durƙushewa tayi awajen tana kuka, gaba ɗaya tayi buji buji da ita, yayinda wasu daga cikin kwalaben da ta fasa, sukai mata rauni a hanu..
Sautin kukanta shiyayi nasarar janyo, hankalin Hameed da yanzu shigowarsa cikin falon, batare da ɓata lokaciba ya nufi ɗakinnata, hankalinsa tashe...
Lokacin daya isa ɗakinnata kwance yatarar da'ita , sai kuka take baki ɗaya tafice a hayyacinta..
Saurin ƙarasawa gareta yayi cike da mamaki yace " Beedah lafiyanki kuwa ?
" Kada kasake ka matso kusa dani !!!,, Beedah tafaɗa cikin ƙaraji.
Tsayawa yayi cak daga inda yake, haɗi da kafe ta da mayun idanunsa da suka fi komai ɗaukar hankali ajikinsa, wani irin kallon mamaki yake jifanta dashi, yayinda ita kuma ta cigaba da rera kukanta,,
ƙoƙari yayi wajen danne tarin damuwarsa haɗi da ƙarasowa gareta,, ɗagota yayi ca ɗak zuwa jikinsa, batare daya kulata da yanda take turje masa ba yanufi bathroom da'ita..
Duk da turjewan da takeyi, bai hanasa yi mata wankaba, haɗi da naɗota acikin towel tamkar ƴar jaririya, kai tsaye kan gado yakaita ya shimfiɗeta.. Lotion ɗinta yaɗauko yashiga shafamata, koda yagama shafamata mai ɗin, wata rigan bacci marar nauyi yasanya mata, ba laifi tayi mata kyau ƙwarai, saida yatabbatar yagama kimtsata kafun ya shiga gyara wajen data hargitsa,, yana gamawa yashiga bathroom shima don yin wanka ..
Koda yafito daga wanka, Brown jallabiya, yasanya haɗi da feshe jikinsa da dadaɗan turarensa, mai sanyaya zuciya, kaitsaye kan gadon yanufa, ya kwanta haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.
Koda taga ya kwanta haɗi da juyamata baya batare, da ya ce da ita ƙalaba yasanyata, fashewa da kukan munafurci, da kisisina.. Jin kukanta yasan yashi saurin juyowa gareta haɗe da jawota jikinsa, Yashiga shafa kan cikinta a hankali,
Yanda yaga bakinta na motsine, yasanyasa gano cewa a kwai abun da take son faɗi , dan haka baijirayi komaiba ya haɗe bakinsu, waje ɗaya,, wani irin hot kiss yake yimata, haɗi da sanya hanunsa abayanta yashiga shafa wa ahankali,, Sosai ya ƙware wajen iya sarrafa mace, da sanyata cikin feeling, koda kuwa itaɗin dutse ce, idan ya raɓeta saita tsinci kanta cikin feeling, lol.
Wani irin hot romance yake yimata, wanda yayi sanadiyar mantar da'ita duniyar da take.. gaba ɗaya numfashinta ɗaukewa yayi, alokacin da taji tattausan labɓansa sun sauƙa akan nipples ɗinta, cike da salo haɗi da ƙwarewa yashiga sucking nipples ɗinnata, daga ƙasanta kuwa hannayensa yasanya yana wasa da'ita... Saida yatabbatar da cewa Beedah tagama fita hayyacinta , kafun ya cillata wata duniyarsa ta daban..
Washe Ga ri
Tsaye yake agaban Mirror ɗin ɗakinsa, yayi kyau matuƙa cikin shigar blue sute ɗin dake jikinsa, mai matu ƙar kyau da tsada, yayin da parking shirt ɗin ta kasance milk colour , sosai tsantsar kyawunsa ya bayyana, yayinda mans pride ɗinsa dake kwance luf kan ƙuncinsa yake ƙyalli da walwali, because yasha gyara ba kaɗan ba...
Yayi mata matuƙar kyau sosai, kyau da adonsa haɗi da ajinsa, su suke tai makawa wajen ƙara ruramata wutar ƙaunarsa, acikin zuciyarta. Wasu zafafan hawaye ne suka samu damar sauƙowa akan ƙuncinta, asa kamakon tunowa da maganar ƙarin aurensa da tayi.
Sarai ya fuskanci irin tarin da muwar data ke ci ki, dan haka yasanya hanunsa yajawota jikinsa, haɗe da matseta cikin faffaɗan ƙirjinsa, cikin sigar lallashi yace da'ita
" Nasan daga jiya zuwa yau kina cikin damuwa, abisa maganar da Ummie taga yamiki, So ki kwantar da hankalinki my Beedah ,insha Allah zan kasance Adali atsakaninku. Yana kai ƙarshen zancennasa yajanyeta daga jikinsa haɗe da sa kai yafice daga ɗakin..
Wani irin kuka ne yaƙwace ma Beedah alokaci guda, haɗe da ɗaukan wayarta ta danna mawa aminiyarta Murja ƙira , bugu biyu Murja ta ɗauki wayar haɗe da cewa " Ƙawata kuma mata agidan *Gwarzon Na miji* ya akayi ne ƙira da...
Kasa ƙarasa maganar Murja tayi, asaka makon kukan da taji aminiyar tata nayi baji ba gani.
Cikin tsananin tashin hankali Beedah tace da Murja " ƙawata kizo gida kisameni please ,, tana kaiwa ƙarshen zancennata ta kashe wayar haɗi da jifa da'ita kan gado,, damuwa ne fal cikin zuciyarta, haƙiƙa tasan Hameed mutum ne mai tsananin biyayya ga mahaifansa, kuma idan tayi sake to fa tabbas tanaji , tana gani zai auri Farhana , duk da tasan irin tsanar da Hameed ɗin yayi mawa Farhana'n..
Haka Beedah tazauna tacigaba da ruskan kuka, zuciyarta cike da tarin baƙin ciki..
Mintuna ƙalilan Murjanatu ta iso cikin gidan, kai tsaye part ɗin aminiyartata tanufa..
Beedah na ganin Murja ta shigo cikin ɗakin, tatashi ta faɗa jikinta haɗe da fashewa da kuka.. Amamakance Murja ke kallon aminiyartata, yanda take kuka, tsakaninta da Allah. Lalle tasan babban abune ya faru ga Beeda'n yanda taga tana kuka, a iya saninta da Beedah bakowani, abune yake sanyata kuka ba, sai abu mai girma kama hanunta tayi suka zauna akan gado....
Follow me....
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇