Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsboDRFhzcuLvDUNLJLxsr
*MENENE MATSAYINA ? FANS*
*Idan kinsan bakya karanta book ɗinnan kada kishiga, haka kuma idan kinsan bazakina magana da comment ba kada kishiga dan Allah, domin kokin shiga zancireki.*
*Banason Links, bana son Talle, banson Vedios ko wani irine, banson kowani irin Post ne, only novels kawai.*
*Gareku masoya Menene matsayina ? danku nabuɗe group ɗinnan, fatan bazaku bani kunyaba, wajen yimin comment.*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MANENE MATSAYINA_*
*(fictional story)**Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated to my lovely sister Maryam*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
*Editing is not allowed 📵*
*Page 2⃣2⃣*
Haka Farhana ta wuni gaba ɗaya sukuku, yayinda hawayenta kuwa suka kasa tsayawa, ba irin rarrashin da ba'ayi mataba amma taƙiyin shiru, hakan yasanya kowa fita sha'aninta...
Kwance yake akan makeken gadonsa, wanda yaƙawatu da adon zamani, yakuma sha shimfiɗa ta alfarma. Idan akwai abun da yake da munsa ayanzu, bai wuce wannan laƙabebben auren da aka liƙamasaba, domin kwata kwata shi a tsarin rayuwarsa ma, bai sha'awan yin mata biyu, sai gashi hakan ta kasance dashi. tsuka yayi alokacin da wayarsa taɗau ƙara alamar shigowar ƙira, sam baison damuwa ahalin yanzu, hutu yake buƙata, dan haka amaimakon ya ɗauƙi wayan saima kasheta dayayi haɗi da gyara kwanciyarsa. Haka yayita saƙawa da kuncewa hardai bacci yayi nasaran ɗaukansa,, duk da cewa ba al'darsa bace bacci a kowani time, ko da kuwa dare ne bai kwanciya da wuri...
Kuka Farhana dake durƙushe agaban Abba da Ummie keyi baji bagani, abubuwa biyu ne suka haɗe mata a lokaci guda, na farko shine yau gata zata gidan wani amatsayin mata, ba Farhan ɗintaba, haka kuma yau zata rabu da Ummie da Abba, tatafi can wani gidan da ba'asan daraja da mutumcin taba...
Nasiha mai ratsa jiki, da zuciya, Abba da Ummie suka yimata, wanda rabin nasihar tasu, suna nusar da'itane akan tabi mijinta sau daƙafa, haka kuma tayi haƙuri da halin rayuwa, takuma zamanto mai haƙuri da riƙe sirrin mijinta, da kuma gidan aurenta.. bayan sun kammala yi mata nasihanne kuma suka kaita ga Dadynta do min yayi mata nasa nasiha'n..
Hanunta Dady ya kamo cike da kulawa, haɗi da ƙaunar ƴar tasa, yace da'ita " Haƙiƙa ke kinsace ƴa mai biyayya ga mahaifanta, ina kuma alfahari dake, akoda yaushe, inada tabbacin bazaki bani kunyaba wajen kyautata rayuwar auren ki, duk da cewa bana tare dake amma nasan cewa ke ɗiyace mai matuƙar hankali, nakuma san abun da kikeso da kuma wanda bakyaso, nasan cewa babu soyayya atsakaninki da Yayanki Hameed, amma ina kyautata muku zato nan gaba, kiyi koyi da mahaifiyarki, Farhana domin ita takasance mace mai matuƙar biyayya agareni, bata taɓa bijiremawa umarni naba koda kuwa sau ɗayane, haka kuma ita macece mai haƙuri, idan kika yi koyi da halayyarta zanyi matuƙar farinciki da hakan ,, kuka Farhana tasanya haɗi da rungume Dady'n nata, daga cikin xuciyarta tana mai jin tausayinsu su duka, kasancewar kowannensu ya ɗanɗani zafin mutuwar masoyi. Ahanakali Dady yasanya hanunsa yashiga shafa kan ƴartasa, yana mai jin tsananin tausayinta, acikin ransa...
Jin da Dady yayi cewa motocin ɗaukar Farhana zuwa gidan mijinnata sun ƙaraso, yasanyashi yimata addu'o'in alkhairi da nasara, haɗi da bata kyautar mota sabuwa dal, ƙirar Matrix, duk dacewa tana cikin tarin damuwa amma kyautar da mahaifinnata yayi mata yafaranta ranta sosai...
Haka Farhana tanaji tana gani aka sanyata a mota, sai gidan Malam Hameed,, (domin tun da aka fara maganan auren nasu yatattara nasa ya nasa shida matarsa suka koma sabon gidan da yagina mai kyau da tsari, dake Gomna road)Koda suka isa cikin gidan kaitsaye, babban falon dake cikin gidan suka nufa, wanda acikinsa ne ɓangaren Farhana yake, babban falone dake cike da kayan ƙyale ƙyale na more rayuwa, an ƙawatasa da haɗaɗɗun kujeru, na alfarma, cikin falon yana ɗauke da ɗakuna guda uku, daga can sama ma wasu ɗakunanne guda uku, kasan cewar falon mai bene ne, daga cikinsune kuma mallakin Farhana yake shine kuma na ƙarshe,, baƙa ramin dukiya Abba yakashe wajen ƙawata mata ɗakintaba, sai dai ace masha Allah...
Aunty Balaraba da kuma wasu ƴan uwansu nakusa sune suka kawota, koda zasu tafi saida suka sake yimata nasiha, mai ratsa zuciya kafun sukai mata sallama,, koda Farhana taga dagaske tafiya zasuyi su barta ita ɗaya saita sanya musu kuka, haka dai suka ɗan lallaɓata sukai tafiyarsu...
Ganin datayi cewa ta kwashe awanni azaune cikin mayafin daba tasan dalilin sanya mata shiba, yasanyata yaye mayafin tafito da fuskarta dake lulluɓe waje, ahankali tashiga ƙaremawa ɗakin kallo, tabbas ɗakin nata yayi kyau sosai, kasancewar komai na ɗakin favorite colour ɗinta aka sanya.. Kallon haɗaɗɗen agogon dake kafe jikin bango tayi, inda yanuna mata 10:30 pm , ahankali ta zuro da ƙafafunta dake kan gado zuwa ƙasa, batare da ɓata lokaci ba tashiga rage kayan jikinta, haɗi da kutsawa cikin inda take tunanin toilet ne.. tana shiga kuwa tatarar da toilet ɗinne, saidai haɗuwar toilet ɗin ya matuƙar bata mamaki, cox an ƙawatasa sosai gwanin burgewa,,
taɓe bakinta tayi domin ita ba wannanne agabanta ba yanzu. Shower ta kunna haɗi da tsaya wa dai dai saitinsa ruwa na dukanta, tayi hakanne kuma ko zata samu relief daga tarin damuwar dake narke acikin zuciyarta...
Ɗaure tafito daga ita sai towel daya tsaya iyaka guiwarta, kaitsaye gaban dressing mirror tanufa, tashafa mai ajikinta,, wata zundu memiyar rigan bacci mai kauri da duhu ta sanya ajikinta, ko turaren da tasaba shafawa duk daren duniya idan zata kwanta bacci, yau kasa shafasa tayi, haka tanufi kan gadon ta kwanta, haɗi da takurewa waje ɗaya,,
"" Zannuna miki soyayya irin wacce baki taɓa ganin irinta ba My Fana duk ranan da aka kawominke gidana amatsayin mata ""
Wani irin siraran hawayene suka yi nasaran gangarowa daga cikin idanunta, alokacin da maganar Farhan ɗinta yadawo mata cikin ƙwaƙwalwa da kunnuwanta, awani hira da suka taɓa yi dashi can da jimawa, afili ta furta cewa
" lalle nayi rashin masoyi mai matuƙar nuna mini ƙauna. Allah ya jiƙanka Masoyina ""
kasancewar tagaji yasa bata wani jimaba bacci yayi nasaran ɗaukanta...Ɓangaren Hameed kuwa yanacan tare da Beedah suna shan love ɗinsu tamkar sabbin amare, yama manta da wata wai ita Farhana, saboda zalunci haka yabiye mawa matarsa suka bar Farhana ta kwana ita kaɗai, batare da yaje gareta ba amatsayinta na sabuwar amarya, wacce take buƙatar kulawa...
Cike da mugunta yake juya goran ruwan swan ɗin dake hanunsa, wanda har raɓa yayi sabo da sanyi, ɗan guntun murmushi yayi haɗi da buɗe murfin gorar batare da tunanin komaiba, yashiga tuttulamata akan fusƙarta. Amatuƙar gigice Farhana ta buɗe idanunta, domin kuwa ruwan ya fara shiga cikin hancinta,, dariya yayi wanda yabayyana dimples ɗinsa, haɗi da kashe mata ido ɗaya, lokaci guda kuma ya haɗe fuskarsa tamkar baitaɓa dariya ba cikin lion voice ɗinsa yace " In 20 minute inaso break fast ɗina yazama ready, ruwankine kitashi ki ɗaura yanzu, ruwankine kuma kizauna." yana kaiwa nan azancennasa yasakai yafice daga cikin ɗaki,, kuka Farhana tafashe dashi, na baƙin ciki da takaici.......
Pls manage 👏🏻
Follow me on whatsapp.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇