Page 36

2.6K 167 15
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

        *MENENE MATSAYINA*
            *(fictional story)*

   *Written by*
phatymasardauna
      *🎈Mrs Sardauna🎈*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

       *WATTPAD*
   @fatymasardauna
      *INSTAGRAM* @phatymasardauna

*Editing is not allowed📵*

*Wannan page ɗin Kyautane ga duk wani masoyin HAMEED da FARHANA, kuyi yadda kukeso dashi...*

*PAGE 5⃣0⃣to5⃣1⃣*

Zumbur tatashi zaune sakamakon jiyo sautin muryarshi datayi a falo,,   harta miƙe saikuma takoma ta kwanta....

Mintuna ƙalilan Ummie tashigo cikin ɗakin hanunta riƙe da goran hatsabibiyar tsumi, wacce ke sanya gwarzon Namiji shiɗewa yakuma fice a hayyacinsa, yayinda yatsinci kansa tsundum cikin babban head guater...

"Farhana" Ummie taƙira sunanta... "Na'am Ummi" ta amsa tana mai tashi zaune...

"Ungo karɓi wannan tsumin kishanye shi tas, bakuma naso kisha shi a zaune, kisha a tsaye, sannan kiɗauko kayanki Hameed na falo yana jiranki zaku wuce gida "

Amsar goran tsumin tayi haɗi da tashi tsaye, tas tashanye tsumin haɗe da aje goran agefe, duk dacewa tsumin yanada ɗan bauri kaɗan, amma bayanda ta'iya dolenta ta shanye tunda Ummie takasa ta tsare...  Ganin tashanye tsumin tas, yasa Ummie ficewa daga cikin ɗakin.

Zundumemiyar hijab tasanya ajikinta, haɗe da jawo trolly bag ɗinta,  wanda dama kayanta sunacikin trolly ɗin a kimtse, kaitsaye falo tanufa.....

Kallo ɗaya yayi mata ya kau da kansa gefe, yayinda itakuma takafesa da kyawawan idanuta, bakaɗan ba yayi mata kyau cikin shigar ƙananan kayan dake jikinsa, haƙiƙa itakam ta more miji, bakuma ƙaramin sa'a tayi ba saboda samun haɗaɗɗen gaye mai aji da kamala kamar Hameed awannan zamanin wahala garesa, domin kuwa Hameed yahaɗu takowani fanni, yana da abubuwan burgewa da dama...

"Inawuni" tafaɗa tanamai duƙawa ƙasa cike da ladabi,  

Saida yaɗau kusan five seccond kafun yace da'ita "Lapiya"  batare da yakuma kallonta ba...

Ummie ce tajata ɗaki, tayi mata nasiha mai ratsa jiki, haɗe da bata wasu ƙarin sirruka dazatayi amfani dasu wajen mallake mijinta batare da boka ko malam ba, ta kuma bata haɗaɗɗun tsumi masu rikita oga,, godia sosai Farhana tayi mawa Ummie, haka sukayi sallama cike da kewar juna....

Yana gaba ita kuma na biye dashi abaya, haka suka fito daga cikin falon..

Yanashiga cikin motar yajawo ƙofar yarufe haɗe dasoma ƙoƙarin kunnata, Farhana dake tsaye cikin sanyin jiki, tasanya jakanta a gidan baya, yayinda itakuma tashiga gidan gaba tazauna,,   dawani irin gudu yafigi motar tasa, ko kula maigadi dake yi musu asauƙa lafiya baiyiba,,         koda suka hau kan titi gudu yaci gaba dayi...   Gaba ɗaya tatakura, domin tunda suka soma tafiya bawanda yace da ɗan uwansa ƙala,  daga yanda taga fuskarsa aɗaure tamau, tasan cewa lallai haryanzu fushi yake da'ita.. Cikin sassanyar murya tace "Appie na"   

"Ummm" ya amsa mata ataƙaice batare dako kallonta yayi ba,   ganin haka yasa jikinta ƙarayin laƙwas... "Appie na" tasake ƙiran sunansa akaro na biyu,,   ko gizau baiyiba balle tasa ran zai amasa mata,  daidai lokacinne kuma suka iso ƙofar katafaren aljannar duniyar gidansa, horn biyu kacal yayi maigadi ya wangale masa makeken gate ɗin gidan, yayinda shikuma yacusa hancin motarsa ciki.... 

MENENE MATSAYINA ? حيث تعيش القصص. اكتشف الآن