🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)**Written by*
phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈**Dedicated to my lovely sister Maryam*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCITION*
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassocition*
*WATTPAD*
@faymasardauna
*INSTAGRAM*
@Phatymasardauna_*NOTE*: haƙiƙa har cikin zuciyata naƙudurta kan cewa bazan sake posting a WhatsApp ba, amma masoyana kunnunamin ƙauna, kuma kunfito kunnuna kuna tare dani, naji daɗi sosai kuma insha Allah zandinga yimuku posting aduk sanda nayi typing,, sai dai kuma agaskia iyaka group ɗin da akemin comments zanna turawa, wanda basayimin comment kuma bazan tura musu ba, saboda ba amfanin hakan, Safna, Sareenah, Raudah, Ummu khulsum, fatyma, Jawaheera, kausar nd Nasiba, Kuna dagirma acikin idanuna, tayadda zan iya yi muku duk wani abun dakukeso, sabo da haka naji bayanan ku kuma zancigaba da posting a WhatsApp insha Allah, inasonku kamar yadda kuke sona,, *FATYMA SARDAUNA FANS* group ina sonku sosai da sosai Allah yabar ƙauna atsakaninmu Ameen ..._
*📵Editing is not allowed*
*PAGE 4⃣0⃣to4⃣1⃣*
Koda ya'isa gidannasu kaitsaye ɓangaren Ummie yanufa, sosai Ummie tayi mamakin ganinsa domin batayi tsammanin dawowansa nankusaba,, bayan sun gaisane kuma shiru ya biyo baya, sarai Ummie tana ankare dashi, takuma gano take takensa amma saita basar taci gaba da ayyukan dake gabanta,, ganin dayayi cewa Ummie tashareshi ne yasanyashi, siɗaɗewa yafice daga ɗakinnata. Kaitsaye ɓangaren su Farhana yanufa fatansa ɗaya shine Allah yasa ya'iske ta.....
Kwance take akan gadon ta yayinda ta ƙudundune waje ɗaya, sanye take da wata Turkish Abaya dusty pink colour, gaba ɗaya rigan tabi jikinta talafe, hakan ne yasamu daman bayyana kyakkyawan surar jikinta,, duk da cewa ta rame amma hips da boobs ɗinta sunanan kamar yanda suke,, yanayin kwanciyar da tayi yasanya taba mawa ƙofa baya, tayanda bazataga wanda yashigo cikin ɗakin ba harsi ta juyo garesa, kaitsaye idan kakalleta zakai zaton bacci take, amma ba baccin take ba, damuwa ce cike a ranta, dakuma tsantsar kewa da soyayyar mijinta, da ke damunta...
Jingina yayi da ƙofar ɗakin nata, haɗe da sanya hanunsa bisa kan faffaɗan ƙirjinsa, yayin da ya watsa ma ta manya manyan idanuwansa akanta, wani irin tsananin tausayin ta ne ya cika zuciyarsa, haƙiƙa yasan baiyi ma ta adalci ba, amma hakan dayayi shine dai dai domin laifin da ta aikata a garesa yaci yayi mata kowani irin hukunci ne, don ma yana yimata son so ne, dababu abun dazai sa ya dawo gareta, ya tabbata da'ace watace ba Farhana'nsa ba to da yarabu da'ita kenan har gaban abada, amma a yanda yakejin tsananin soyayyar Farhana bayajin zai'iya cigaba da rayuwa babu ita .....
Sake lumshe idanuwanta dasuke zubar da ƙwalla tayi, alokacin da daddaɗan ƙamshin turarensa yashiga kawo ma ta ziyara cikin hancinta, kokaɗan bata kawo cewa shiɗin bane domin dai jin ƙamshin yariga daya zame ma ta sabo, saboda hancinta yasaba da ƙamshin sosai shiyasa take yawan jinsa ako dayaushe.
Hanunsa yasanya bisa kafaɗunta, a matuƙar razane ta juyo don ganin wanda ya aikata hakan agareta, manya manyan idanuwa'nta masu rikirkita masa tunani aduk sanda takalleshi dasu, tawaro alamar tayi tsananin mamaki'n ganinsa, murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi haɗe da ɗaga mata gira alamar Yadai, hanunta dayake rawa takai kan fuskarsa domin tabbar da cewa mafarki take ko akasin sa,, aikuwa jitayi tataɓa lallausan sajen sa dake kwance lub agefen fuskarsa,, alamar dagaske ne bawai mafarki take ba,, wani irin kuka tafashe dashi haɗe da faɗawa cikin jikinsa,, rungumeta yayi tsam acikin jikinsa yana mai sauƙe wata irin nannauyar ajiyar zuciya, kuka Farhana keyi sosai yayinda ta rungumeshi ƙam tamkar ance wata zata ƙwace ma ta shi,, hanunsa yasanya bisa kanta ahankali yake shafa long hair ɗinta dayasha gyara sosai sai tashin ƙamshin haɗaɗɗun mayukan gyara gashi yake..