Page 17

2.2K 179 6
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
 
           *_MENENE MATSAYINA ?_*
                 *(fictional story)*

       *Written by*
Phatymerhsardauna
       *🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated to My Lovely sister Maryam*

*🌈Kainuwa Writers Association*

~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~

~{,31 August 2019}~

*(Wannan shafin dukansa kyautane gareki HAJJAJU, kiyi yanda kikeso dashi, iya wuya muna jone insha Allah, ngd da kulawarki a gareni. 🌹)*

*Editing is not allowed 📵*

     *Page 2⃣3⃣*

Wani irin tsanarsa ne yasake ɗarsuwa acikin zuciyarta mai tsanani, zata iya ɗaukan komai a duniya amma banda wulaƙanci, cike da ƙunan zuciya tamiƙe haɗi da shigewa bathroom tasakar mawa kanta shower,   koda tafito awankan, mai kawai tashafa, haɗi da sanya wata  doguwar riga mai faɗin gaske irin wacce ake ƙira da suna bubu gown, duk da cewa bata sanya rigar dan tayi mata kyauba, amma sai gashi tayi mata kyau ajiki, ganin haka yasanya ta zumbula hijabi, domin ɓoye kyawun da rigar tayi mata,    kwanciya tayi bisa gado  haɗi da lumshe idanuwanta,,  take nasihar da Ummie tayi mata yashiga yawo acikin ƙwaƙwalwarta,,inda take ce mata

"tabi mijinta komai yace da'ita tayi, kada tai mai musu, matuƙar bai saɓamawa mahaliccintaba,, wasu siraran hawayene sukayi nasaran gangarowa daga cikin idanunta,, haka ta miƙe cikin sanyin jiki ta fice aɗakinnata.

Kaitsaye falon ƙasa ta sauƙa ba kowa cikin falon sai ƙarar A.C dake tashi, domin kuwa gari baigama waye waba,  inda take tunanin nanne kitchine  tanufa, cikin sa'a kuwa ta tarar da nan ɗinne..
Jigum tayi cikin kitchine ɗin tana nazarin mai zata dafa because batasan dame zata faraba,, shi wani irin mutum ne  miskilin gaske   da babu wanda yasan favorite food ɗinsa, kuma koda ma tasani bazata girkaba, domin bataso tagansa cikin farinciki..

A ƙagauce ta dafa coffee haɗi da soya chips, ko ƙwai babu, haka ta jere mai akan derny table ɗin dake cikin falon, kana ta koma ɗakinta.

Tana kwanciya akan  gadonta ta fashe da kukan tausayin kanta, saida tayi mai isarta kafun ta tashi ta shige cikin bathroom dan wanko fuskarta datayi caɓa caɓa da hawaye..

Hameed kuwa yana gama kimtsa kansa, cikin shigarsa tazuwa office, kaitsaye briefcase ɗinsa ya ɗauka haɗi da sakansa, yafice daga cikin ɗakin batare da ko kallon inda, Beedah ke kwance shame shame  bisa gado tana baccin asaran data saba yi kowacce rana,  yayiba.

Yana fitowa falon, yanufi derny table, azatonsa zaiga lafiyayyen break fast, sai kuma yaga akasin hakan. ko da ya ɓuɗe warmer ɗin dake aje ƙan table ɗin, wani munafukin murmushi yayi haɗi da  Ƙanƙance manya manyan  idanunsa yakuma waresu  alokaci guda,   wani munafukin murmushi ne yabayyana akan fuskarsa batare da ɓata lokaci ba yasanya hanu yaɗauki food flaks haɗi da  mug ɗin da coffee ɗin keciki, kai tsaye  sama yanufa inda zai sadasa da ɗakin Farhana ...

Ba kaɗanba Farhana ta tsorata, asakamakon jin ƙaran bankaɗo ƙofar tata da akayi tamkar za'a ɓalla,  ganinsa da tayi yasanya gabanta faɗuwa, amma saita dake haɗi da kawar da kanta gefe.
 
A hankali yashiga takawa harya isa gareta,  hanunsa yasanya yajawo lufayanta da ƙarfin gaske, har saida ta birkito zuwa jikinsa, hanunsa yasanya yashafi gefen fuskarta da yayi ja, haɗi da sakin murmushinsa daya saba yi idan zai gudanar da tsantsar mugunta,   zaunar da'ita yayi abisa kan gado haɗi da jawo kujera shima ya zauna yanamai fuskantarta, kulan da ya shigo dashi ya buɗe, haɗi da  turo mata  gabanta,         " Ci " yafaɗa ataƙaice , babu kuma alamar wasa atattare dashi, kallon sa tayi haɗi da kallon cikin kulan, batare da tace dashi ƙala ba.

"Kici nace !!! " ya sake  faɗa cikin tsawan daya
matuƙar razanata,

hanunta na rawa haka tashiga ɗaukan chips ɗin da babu alamar ɗanɗano ajikinsa  tana kaiwa bakinta,,  Yayinda shi kuma Hameed ya kafeta da idanunsa masu kalan gold baya ko ƙyaftawa, wanda hakan kuma ke haifar da zubawar tsikar jikin ta akai akai.

Loma shida kacal tayi tacire hanunta acikin kulan, dan batajin zata iyaci gaba da ci. 

Ganin haka yasanya Hameed buɗe murfin mug ɗin da  coffee'n  ke ciki, fuskarsa babu alamar wasa ko sassauci yakai Mug ɗin zuwa bakinta, daga kallon dayake mata kaɗai, tafahimci abun dayake nufi, saurin ja da baya tayi domin kuwa, bazata iya shaba saboda yana da zafi,  hanunsa yasanya haɗi da kamo kanta da ƙarfi yashiga tuttulamata coffee ɗin, bako tausayi.

gaba ɗaya ta shiɗe domin kuwa rabin coffee ɗin hancinta yake shiga, babakintaba, ga kuma zafinsa daya fara ƙona mata fata, duk yanda taso ta ƙwaci kanta kasawa tayi, haddai numfashinta yashiga seasing,, cike da salon mugunta yasake mug ɗin daga hanunsa, take sauran coffee ɗin dayayi ragowa ya watse ajikinta, yana saketa tashiga kwara ra amai baji bagani,
murmushi yayi haɗi  da ɗage kafaɗunsa sama, alamar ko oho, batare daya kula da halin datake cikiba ya sanya kai  yafice daga ɗakin.

Tamatuƙar galabaita, domin kuwa amai tayi bana wasaba, dan saida   ta amayar da duk wani abun dataci,  da ƙyar ta iya jan ƙafafunta tanufi toilet, a ƙagauce ta yi wanka, kasancewar duka jikinta ya ɓaci da amai.

Tana gama mopping gurin data ɓata, jiri yayi nasaran ɗaukarta, take tazube akan gado,    ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, yayinda ƙwallan azaba ke gangarowa daga cikin idanunta, bajimawa wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita...

Ba'ita ta farkaba sai bayan sallan azahar, koda ta tashi, ji tayi gaba ɗaya jikinta ba ƙwari, haka dai ta daure ta yi wanka.

Zaune tayi jugum tana tunanin halin ƙiyayya da kuma mugunta Irin nasa agareta,  batasan mai tai masa ba da  yake gwada mata tsananin ƙiyayya, kuka tafashe dashi mai cin rai, aranta tana dana sanin aurensa datayi, domin hatta gwammace da Atif aka auramata, bazai taɓa gwada mata kwatan kwacin tsanar da Hameed keyimata ba.    Haka gaba ɗaya Farhana tayi wunin ranan sukuku, haɗi da tarin damuwa, babu kuma mai rarrashinta...

Baishigo cikin gidanba sai 10 pm, kaitsaye bedroom ɗinsa yanufa,   kayan jikinsa yashiga ragewa haɗi da faɗawa bathroom.

Ɗaure yake da towel daga ƙugunsa zuwa guiwarsa, kyakkyawan surar jikinsa tayi matuƙar bayyana, kallo ɗaya zakai masa kagane cewa ƙaƙƙarfan namijine maiji da jarumta, ma abocin motsa jiki, domin kuwa jikinnasa a murɗe yake, yayinda 6 packs ɗinsa suka  bayyana akan cikinsa raɗau, haƙiƙa Hameed yana ɗaya daga cikin irin gwarazan jaruman maza, wanda wasu mata dayawa suke fatan mallaka amatsayin miji.
Da hand dryer yayi amfani wajen  busar da tulin gashin kansa wanda tsabar yawa  harsai da yayi tozo, mai kawai yashafa haɗi da sanya dogon pencil jeans nd t-shirt, yakuma feshe jikinsa da turarensa mai ƙamshin gaske.

Cike da iyayi haɗi da kisisina, taturo ƙofar ɗakin, hakan yasanya Hameed dake latse latse a laptop  ya ɗago kansa ya kalleta,  sanye take da wata shara sharan sleep gown wacce za'a iya ƙira da ita gwamma babu,  fuskartannan tasha meckup, tamkar mai zuwa gasan kwalliya ta dunia, yayinda kanta kuma yasha kitso da gashin doki wato (atachment), murmushin gefen baki yayi mata haɗi ɗa ɗauke kansa daga gareta yaci gaba da'abun dayakeyi.

Cikin son jan hankalinsa, ta ƙaraso gareshi haɗi da hayewa saman jikinsa, tasakarmai kiss a kan kwantaccen sajensa  dayake matuƙar ɗaukar hankalinta ako da yaushe, bata tsaya anan ba haka tashiga suɗesa da lashesa tamkar tsohuwar mayya, ganin dayayi tana ƙoƙarin wuce gona da irine, yasanya hanunsa  ya matseta ajikinsa haɗi da lakatan saman hancinta, ya kuma kashe mata ido guda ɗaya, haɗe da sakin wata ƴar guntuwar murmushi ,  take fuskar Beedah tasauya, domin sarai ta fuskanci abun dayake nufi.

A hankali yajayeta daga jikinsa haɗi da mikewa yanufi, ƙofar fita, cikin hanzari Beedah tasha gabansa haɗe dacewa " Inazakaje kuma dear ?
"Ɗakin Farhana" yafaɗa ataƙaice.

Follow me.

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

MENENE MATSAYINA ? حيث تعيش القصص. اكتشف الآن