*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*MY LOVELY MUM*
*PAGE 2*
*masu tambaya cewa wannan novel din kona kud'i ne? A'a na kyauta ne bana kud'i bane, so kowa zai iya karantawa, is just a short story for my love once*
Amal da sauri ta haura Sama, direct d'akinta ta nufa, inda tayi toilet tasa soap ta Fara wanke hannun da Usman ya ri'ke mata cikin kyama, "tare da fad'in sai yayi daya sanin tabamin jiki da yayi, "matsiyacin Talaka.
Koda Usman ya fita, taxi yahau inda yace akai shi, dutsen Alhaji, koda suka k'arasa a kofar wani Gida suka tsaya, gaban gidan kwata ne, k'ato sai wani katako da akasa ake hawa a wuce, cikin gidan ya shiga da sallama.
Amsawa akayi, wata mata dake d'aki tace Usman ne? " yace eh nine Mama, sannu da gida. " Tace yauwa , Har an dawo? Naga kazo da wuri yau.
Yace eh wlh mama na ajiye aikin ne bazan iya ba.
Salati ta saki tare da fad'in dan Allah Usman ka rufa mana asiri, kasan fah kaine komai namu, da wannan aikin muka dogara, yanzu inkace ka ajiye ya zamuyi?
Yace mama Allah zai rufa asiri, tunda Dai anyi karatun, sai a gode ma Allah insha Allah za'a samu aiki, Koba yanzu ba.
Mama tace wani aiki, yau shekaranka hud'u da Gama karatu amma babu aiki, "yanda wannan k'asar ta Gama lalacewa sai kana da hanya zaka samu aiki, in baka dashi kuma sai dai kaita zama, "yanzu yanda aiki ke wahala Aiko masu hanyar ma sai sunji jiki suke samu, balle kai dan Talaka, "Toh wai maima akama a wajan aikin ne daka ajiye?
Yace bazan d'auki wulakanci ba, ko kad'an.
Mama tace shi Alhajin ne ya wulakanta ka?
Yace a'a, tare da fara bata Labarin abunda Amal tayi mishi, "da kuma abunda ya fad'a mata.
Mama tace oh ikon Allah, amma Aida baka biye mata ba, "yace Mama sai in bari ta mareni?
Tace ba haka nake nufi ba, ina nufin da baka biye mata har ka ajiye aikin ba, mai nema ai baya zuciya, sannan Mai nema sai yayi hakuri, kasan shi Mai kud'i ganin Talaka yake ba komai ba, "Ina son koda gaba ka samu wani aikin kayi hakuri, gaba d'aya duniyar kwaya nawa ce ma? "in ba'a hakuri da juna ai mutum bazai taba samu yakai inda yake soba.... K'aran wayar usman yasa mama yin shuru
D'auka Usman yayi yaga Alhaji Sulaiman Kura, dannawa yayi tare da gaidashi cikin girmama.
Bayan Alhaji ya amsa yace kai Usman Mai yayi zafi kaida ibtisam harka ajiye aiki?
Nan ya fara bama Alhaji labari, tare da fad'in Alhaji kayi hakuri Nasan kana mutunta na k'asan ka, rainane ya baci har takai da hakan.
Alhaji yace Usman, tun sanda na d'aukeka kana mana Guga, nake ta Lura dakai, na kuma yaba da hankalinka, wannan shine silan dana tambaya kace ka iya tuki sai yasa nace ka dinga tu'ka Amal, badan komai ba sai dan na yaba dakai da kuma hankalinka, ina son ka dawo bakin aikin ka gobe sannan kayi hakuri da Amal kasan yarinya ce k'arama.
Usman yana ganin darajan Alhaji da kuma mutuncin shi, wannan shine dalilin da yasa yace zai dawo aikin.
Bayan ya kashe wayan, ya fad'ama mama yanda sukayi.
YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people