*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 8*
Sadiya tace Usman ya naji kayi shuru kuma? Kodai baka son aikin soja ne??
Usman yace a'a ba haka bane, Aini bani da wani zabi a halinda nake ciki yanzu, amma ina son kiban daka yau zuwa gobe zan kiraki muyi magana
Sadiya tace shikenan, karka samu damuwa akwai sauran lokaci, amma lokacin baida yawa
Usman yace hakane
Nan suka canza wata firan inda take fad'a mishi baici komai ba
Yace Alhmdlh, tare da fad'in a Ina kike aiki yanzu?
Sadiya tace ina lecturing ne a university of Abuja
Usman yace kai Allah ya taimaka
Ta amsa da Ameen tare da fad'in ina fatan dai an ajiye iyali?
USMAN yayi y'ar murmushi tare da fad'in har yanzu dai, domin aiki bai samu ba, kwakwara taya zamu ajiye iyali??
Sadiya tace Aiba daga nan take ba
Usman tashi yayi tare da fad'in Bari in gudu, sai na kiraki
Sadiya ta amsa da kadai k'i cin komai a gidan nan
Usman yace in nazo next time zanci insha Allah
Har waje ta rakashi inda yahau taxi ya wuce, kai tsaye gidan mahaifiyarshi ya nufa, inda motar ta tsaya a dai dai kusa da kwatar kofar gidansu
Fita yayi yaba ma Mai taxi din kud'i sannan ya shiga cikin gidan Kai tsaye tare da sallama
Amsawa mama tayi wacce take zaune tana yanka alaiyahu, tace a'a har an dawo??..
Yace eh wlh, da wajan aiki ma zan koma, amma nace dole sai nazo na ganki munyi magana
Mama tace maiya faru? Allah yasa dai tafiya?
Murmushi yayi tare da fad'in lafiya, dama akan maganan takarduna dana kaima Alhaji ne, toh yau na had'u da wacce nake baki labari rannan, wacce mukai karatu tare, toh shine tace in nema soja zan samu insha Allah, toh bandai amsa mata ba, saboda Kinga Alh Sulaiman ya amshi takarduna
Mama tace in banda abunka USMAN danya amshi takardun ka AI shima nata bai kamata kakiyi ba, domin raba k'afa akeyi, duk Wanda mutum ya samu, amma idan mutum yace zai zauna waje d'aya ai yana da aiki
Inaga shima ka nemi soja din duk Wanda ka samu shikenan, ni Wlh hankalina ma yafi kwanciya da aikin soja din Domim ban son yawan fushin nan naka, musamman yanda kake nunawa zaka iyayi ma y'ar Alh Sulaiman iyaka, kar wata rana zuciya ta d'ibeka kaje ka illata musu y'a ka janyomin bala'i ina zaman zama na
USMAN yayi murmushi tare da fad'in haba mama sai kace mara hankali, ai yanzu wlh komai tayi baya damuna ko kad'an hasali ma ni yanzu tausayi take bani, domin irin rayuwar data d'aukan ma kanta Abun a tausaya mata ne
Mama tace hakane, Allah ya ganar da ita
USMAN ya amsa da Ameen tare da fad'in yana..... K'aran wayarshi ne alaman Shigowan message wayarshi yasa yayi shuru da abunda yayi niyan fad'a tare da d'auko wayarshi ya fara duba message din kamar haka

YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people