*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 21*
Bayan sun k'arasa gida, Amal fita tayi daga motar inda tayi cikin gidan da sauri, kai tsaye d'akinta ta nufa inda ta fad'a toilet domin tayi wanka, dan ta gaji sai kace tayi wani aiki
Bayan ta fito daga wanka rigan baccinta tasa wanda ya tsaya mata dai dai cinyarta ta feshe jikinta da turare Mai dad'in kamshi gaba d'aya d'akin ya gauraye da kamshin turaren jikinta
Tana wajan dress mirror a zaune akan stool daga duka alamu tunani takeyi wanda ba tunanin komai take ba saina yanda zata bi iyayenta domin zuwa Niger ita gaba d'aya hankalinta ya kasa kwanciya akan su tafi su biyu, ya kamata ta bisu
Jin an tabata yasa tayi firgit ta tashi tsaye cikin tsoro harda sakin y'ar kara, ta kankame jikin usman
Shi kam ganin haka sai Abun ya bashi dariya, tare da ri'keta a jikinsa shima ya rungumeta yana fad'in calm down Amal nine
Wani irin ajiyan zuciya take saukewa mai cike da fargaba da kuma tsoro
Lokaci d'aya kuma ta Fara k'okarin jan jikinta daga nashi tana tureshi
Ganin haka yasa ya saketa tare da k'ura ma fuskanta ido....
Cikin tsiwa tace karka k'ara tabamin ji....
Ganin yana matsowa kusa da ita yasa tayi shuru tana dan matsawa baya, domin ganin irin kallon da yake mata yasa gabanta ya fara fad'i sosai....
Baya takeyi yana matsawa kusa da ita harta fad'a kan gadon d'akin, shima gadon yahau Tana k'okarin tashi ya janyota saman jikinshi tare da rungumota da karfi ya matseta a jikinsa, Amal ido ta rufe tare da faduwan gaba
Usman idonshi na kan fuskanta Wanda ta rufe ido Sosai Alaman tsoro
Murmushi yayi tare da saukar da ita daga saman jikinshi
Amal na ganin haka ta Fara k'okarin tashi ta gudu, amma sai yasa hannunshi ya ri'keta tare da janyota ya tashi ya kwantar da ita, Ganin yana matsowa alaman yana son yayi kissing d'inta yasa ta saki wani irin K'ara mai sauti tare da fad'in bana so, amma ina usman ko gezau baiyi ba, sai matsawa daya kar'ayi gab da ita inda tayi sauri ta lumshe ido har yana jiyo k'aran bugun zuciyarta
Lokaci d'aya yayi murmushi tare da tsayawa daga abunda yayi niya, yana kallon fuskanta, yana son Amal da yawa, sai dai kuma baya jin zai iya komai da ita ba tare data yarda ba
Dan haka ya tashi ya fita daga d'akin inda ya nufi falo ya zauna akan kujera Mai cin mutum d'aya tare da sunkuyar da kanshi k'asa
Amal kam jin ya fita yasa ta tashi ta rufe kofarta da key tare da zama tana sauke ajiyan zuciya, lokaci d'aya kuma ta fashe da kuka domin tunawa da tayi bata da wani zabi face ta amince dashi komin daren dad'ewa, domin shine mijinta, kuma burin mahaifinta shine ta zauna dashi har karshen rayuwarta
Kuka take Sosai, lokaci d'aya idonta yayi ja kanta ya fara Mata ciwo, tashi tayi ta fad'a toilet ta wanke fuskanta tare da zuwa ta kwanta, harta kwanta ta tashi da sauri ta fita inda ta ganshi a falo ya kifa Kai k'asa
YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people