*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 12*
Hjy rabi tace Aiko zaki canza suna, domin ina Mai tabbatar miki babu inda zashi....
Amal na k'okarin yin magana hjy rabi ta daga mata tsawa tare da fad'in Yimin shuru Mara hankali kawai fitar min a d'aki
Amal Fuuuuu ta fita kai tsaye d'akinta ta nufa inda taita sintiri kaman Mai parade, ba komai take sakawa ba sai yanda Usman zai bar office din Dad d'inta, k'aran wayarta ne yasa ta nufi wayar tare da dauka, fahad ne dan haka yasa ta saki wani murmushi tare da daukan wayar tasa a kunnenta......
Fahad yace my young millionaire kin San wani abu??
Murmushi tayi tare da fad'in a'a saika fad'a
Yace Dad d'ina zaizo ganin Dad d'inki, domin Ayi maganan aurena dake
Amal tace wow really
Fahad yace yes, kin San ina sonki, so bani da wani fata face in aureki
Amal cikin jin dad'i tace Nima Nasan haka, sai yasa koda yaushe nake son ka
Murmushi yayi tare da fad'in I will call you later, tare da kashe wayan....
Amal wani irin ihu ta saki tare dayin tsalle na Murna domin burinta zai cika, zata samu abunda take so....
Sadiya ce zaune a cikin bedroom d'inta, ba komai take tunani ba sai yanda zata shawo kan Usman ya amince ya amshi kayan da Mum d'inta ta bata wanda tace shi zai saka in za'ayi event din...
Lokaci d'aya ta d'auki wayarta tare da kiran Layin usman din, bugu uku ya d'auka yana fad'in amarya bakya laifi.....
Ajiyan zuciya tayi tare da fad'in my dear ina cikin wani hali...
Yace maiya faru???
Tace dan Allah ina son ganinka, ka taimaka kazo muyi magana dan Allah
Usman yace ok Zanzo karki damu gani nan tafe
Kashe wayar yayi
Sadiya babu tashi tayi inda ta fad'a toilet tayi wanka shap shap, sannan ta fito ta saka wata doguwar riga bayan ta feshe jikinta da turare Mai kamshi....
Zama tayi tana jiran zuwan nashi, wayarta ce ta Fara K'ara inda ta d'auka taga usman dinne
Bayan ta d'auka yace nazo, ina kofar gidanku, ki fito....
Tace ka shigo mana
Yace a'ah basai na shigo ba, kizo muyi magana a nan kawai
Tashi tayi ta fita, inda ta sameshi cikin motarshi, kai tsaye ta shiga cikin motar inda ta zauna a gaba.... Kallonshi tayi ta saki murmushi tare da fad'in amma dai yau ga dukan alamu bakaje office ba
Yace Mai kika gani
Tace gashi yau ka amsa kirana da wuri..
Dariya yayi tare da fad'in dole in amsa domin yanda naji muryanki kaman kina cikin damuwa
Sadiya tace Sosai kuwa, wlh my dear ina cikin wani hali, dan Allah karka k'i amincewa da abunda zan fad'a, koda yake mum tana son ganinka....
Yace lafiya kuwa?? Maiya faru??

YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Kısa Hikayeis a story of young millionaire girl, who hate poor people