*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(Maryam Obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAUWA A USMAN*
~JIDDERH~*SHORT STORY*
*PAGE 1*
*TSARKI YA TABBATA GA ALLAH UBAN GIJIN TALIKAI WANDA YA SAKE BANI DAMAN SAKE RUBUTA WANNAN LABARIN , YANDA NA FARA LAFIYA ALLAH YASA IN GAMA LAFIYA*
*WANNAN GAJERAN LABARI NE, DA ZAN RUBUTA SABODA MASOYA NA Y'AN FACEBOOK, MUSAMMAN WANDA SUKE USING K'ARAMIN WAYA, GASHI SUNA SON BIYAN KUD'IN ~NAJEEB~ BABU DAMA, DAN BASA WHATSAPP, INA MATUAKAR YINKU IRIN SOSAI DINNAN, ONE LOVE MARYAM OBAM NA GODIYA DA IRIN K'AUNAR DA KUKE MATA*
Wata mota ce ta tsaya a gaban wani super market, "kiran Prado, gaba d'aya motar tinted ne baka ganin wanda ke cikin motar, sai dai Shina motar ya ganka.
Gaban motar aka bud'e wani matashi, chocolate colour ya fito daka cikin motar, cikin k'ananan kaya, " bud'e Bayan motar yayi Wanda hakan ya tabbatar dashi driver din wanda ya bud'e ma kofar motar ne, "wata yarinya ce Fara sol Doguwa, ta fito daka cikin motar, sanye take cikin k'ananan kaya English wear, " kana ganin yarinyar kasan y'ar wani babba ce, domin batai Kama da matar aure ba ko ince wacce zata mallaki dukiya tata ta kanta, yarinyar tana dakyau duk yanda mutum yakai da kushe, inya kalla Amal zai ga kyawun da Allah yayi mata.
Bata ko kalli saurayin dake tsaye ba, wanda ya bud'e Mata kofar kenan, ta wuce cikin super market d'in, cikin tafiyar ta wacce takeyi kaman bazata taka k'asa ba.
Shiko saurayin daya tu'kota Kai ya girgiza alaman mamakin irin halin wannan yarinyar, "kwata kwata bata d'aukan duniya da sauk'i, "lokaci d'aya kuma yayi d'an murmushi tare da fad'in "dukiya yasata take ganin kowa ba komai bane, amma bata biyo halin ubanta ba, domin ba haka yake ba, "mutum Mai daraja dan Adam da girmamashi.
Amal kam koda ta shiga super market d'in, "tsayawa tayi tana jiran Usman driver d'inta kenan, tana jira ya shigo ya ri'ke mata basket, "kallo d'aya zaka mata Kaga bacin rai a fuskanta, wanda wannan bacin rai din bana komai bane saina Usman daya k'i shigowa ya ri'ke mata basket, "cikin bacin rai ta fita tare da nufa motar inda ta ganshi a cikin motar zaune abunshi yana waya "ranta taji ya kuma baci Sosai, "Wanda yasa ta Fara buga glass din motar.
Usman bud'e Mai yakon ya bud'e kofar motar, saiya sauke glass din motar, "ranta taji ya kuma baci Sosai tare da tambayan kanta Mai yake nufi ne?
Usman yace "Amal lafiya kin gama ne?
Wani irin kallo ta watsa Mai tare da fad'in "karka k'ara kiran sunana a wannan k'azamin bakin naka, daka yau kar in k'ara ji, "karka manta kaine sabon driver d'ina daka yau, "kuma dole kayi abunda nake so, "kar in k'araji ka kira sunana dole ka kirani da madam ko hjy, "sannan maza ka fito ka ri'ke min basket, koni kake so in d'auka da kaina?
Usman kallonta yake, "abunda tayi bai bashi mamaki ba, danya dad'e yana aiki a gidansu, yana ganin yanda take ma mutane, "yana kallonta ne saboda tace ya kirata da hjy ko madam, yarinyar da bata wuce shekara Goma sha bakwai ba, ta kalleshi Wanda yayi 30yr tace ya dinga ce mata madam, "dan murmushi yayi tare da bud'e kofar dan yasan Mai nema dole yayi hakuri, sai dai bazai d'auki raini ba, duk da yana aiki a karkashinta.
Ganin ya fito yasa tayi gaba, "Tana fad'in tsiyar Talaka kenan sai girman kai, "da nuna isa, "in banda raini kana Talaka Ina Kai ina girman kai.
Usman binta yayi cikin super market d'in "inda ya daukan mata basket din kaman yanda ta bukata, "gefen perfumes ta tsaya, inda ta Fara jida kaman ba gobe, "ta d'iba da yawa sannan ta nufi gefen Mai "ta d'auki Wanda take amfani dashi tasa cikin basket din da Usman ke ri'ke dashi, "Tana gama d'iban Mai din tayi gaba wajan biyan kud'i, "shima binta yayi inda ya ajiye basket din aka fara k'irga kayan data d'auka, "fad'a mata kud'in kayan akayi ta mi'ka atm d'inta inda aka cira a POS, aka bata, "Tana amsan ATM din tabar wajan.
Kai Usman ya girgiza Alaman wannan tayi nisa, "bayan ansa kayan a Leda " Usman ya d'auka tare da fitar dasu, "koda ya fita a tsaye ya ganta alaman bazata bud'e motar ba saiya bud'e Mata sannan zata shiga, "booth yaje yasa kayan sannan ya bud'e Mata motar ta shiga ya rufe, "shima shiga yayi tare da tada motar sukai gaba
Kunna radio yayi inda ake Labarai "kaita d'aga tace kashe radio dinnan, "bana son hayaniya.
Baice komai ba ya kashe tare daci gaba da tafiya "Koba komai zai barta kodan mahaifinta, domin shi yasan darajan mutane
Koda suka k'arasa gida, yayi horn Mai gadi ya wangale tankamemen gate din gidan, "Kai tsaye ya shiga da motar,"bayan ya faka ya bud'e ya fito inda ya nufi booth ya kwashi kayan data siyo ta ya wuce dasu
Amal dake zaune cikin mota "ganin ya wuce yasa ranta ya baci Sosai tare da fad'in mai yake nufi? Gashi ya kashe motar babu AC, dole yasa ta bud'e kofar motar da kanta ta fito cikin k'unan rai
Kai tsaye itama cikin falon gidan ta shiga, "inda ta ganshi yana k'okarin fita daka falon, "hannunta ta d'aga zata wanke shi da Mari da sauri ya ri'ke mata hannun....
Tare da kallonta yace karki Fara, "dan Ina aiki a karkashin mahaifinki bashi bane zai baki dama ki wulakantani ba, "ni Talaka ne amma bazan bari aci mutunci naba, "sai yau na k'ara yarda da baki da hankali, baki San darajan d'an Adam ba....
Cikin zafin rai tace nika ri'ke ma hannu da wannan k'azamin hannun naka?
Lallai kayi kuskure wajan tabama millionaire Amal hannu, kana Talaka, shine zaka saka hannunka ka ri'ke min nawa? Ko Mai arziki bai isaba, balle kai 'kazami , jahili matsiya... D'aga hannunshi yayi zai mareta Wanda hakan shi yasa tayi shuru.....
Usman ri'ke hannun nashi yayi cikin bacin rai ba tare daya mareta d'inba, "yace kinci darajan masu daraja, "sannan Ina son ki sani daka yau bazanci gaba da aiki a nan ba, saboda ke, domin bazanci gaba da tu'ka jahila irinki ba, mara tunani, ni Talaka ne, amma na fiki tunda Nasan darajan d'an Adam, Indai duniya ce zata koya miki hankali, "Wanda bai zo cikin taba Tana jiranshi balle keda ke cikinta, mahaukaciya, "yana fad'in haka ya fita fuuuu
Amal kam mamaki take, yauce rana ta farko tunda take a duniya wani yaci mata mutunci, "kuma Talaka, "lallai yayi kuskure saina nuna mishi banbanci tsakanin Mai kud'i da Talaka, saina nuna mishi dole Talaka yama Mai kud'i biyayya, lokaci d'aya ta kalli hannunta daya ri'ke cikin kyama tare da fad'in wannan k'azamin hannun nashi yasa ya ri'keni, murmushi tayi tare da fad'in I will teach him a lesson that he will never forget in his life, this is a promise from me young millionaire Amal......Hmmm ikon Allah muje zuwa muji wacece wannan Amal din
*MARYAM OBAM*

YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people