19

952 62 3
                                    

*MILLIONAIRE AMAL*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

                 *PAGE 19*



Bayan ta gama kukan tasa ta shiga toilet ta wanke fuskanta, sannan ta fito tasa rigan

Bayan ta gama shiryawa ta fito jikinta sai kamshi ke tashi, tunda ta fito yake kallonta amma ta gefen ido, yana son Amal sosai

Bata kulashi ba, shima bai damu da hakan ba, ya tashi ya fita, itama binshi tayi a baya bayan ta sakar mishi wani irin harara ta baya, lol Amal manya wannan shi ake kira harara a cikin duhu, tunda kinyi bai gani ba

A mota ta iskeshi ya shiga yana jiranta

Bayan motar ta nufa zata bud'e

Ganin haka yasa yayi luck din motar ta baya, ido ta lumshe tare da cije lebe, lokaci d'aya kuma tayi tsaki tare da fad'in mai yake nufi??

Gaban motar tayi inda ta bud'e ta kalleshi tare da fad'in ka bud'emin baya in shiga

Bai ko kalleta ba, idonshi na kan wayarshi yace am not your driver now, tunda ba salary zaki bani ba, and wannan mota nane not yours

Amal wani irin Abu taji ya tsaya Mata a wuya dan ba'kin ciki, haka dole ta zauna a gaba, tare da tamke fuska.....

Kai tsaye gidansu ya nufa inda ya tsaya a bakin gate ya kalli Amal tare da fad'in anjima in nazo daukanki Zan shigo

Amal bata kulashi ba, sai bud'e motar da tayi ta shiga cikin gidan kai tsaye

Shi kam usman Kai ya girgiza tare da fad'in ko yaushe zata canza daga wannan halin Nata oho, motarshi yaja Domin zuwa gidan sadiya

Koda Amal ta shiga gida a falo ta iske iyayenta da Mum suna zaune suna fira kaman Sun saba

Amal fuskanta babu yabo babu fallasa ta k'arasa falon sai dai idonta nakan iyayenta, zama tayi kusa da Mum tare da lumshe ido

Mum tace lafiya??

Ido ta bud'e tare da fad'in Ina kwana Mum?

Bayan Mum ta amsa

Sannan ta kalli iyayenta ta gaidasu

Suka amsa cikin fara'a

Amal ta kuma kallon Mum tace shiya saukeni inzo in gaidaku

Mum tayi murmushi tare da fad'in ai yau budan Kai, harda gidansu zaki, ki gaida mahaifiyarshi

Amal bata fuska tayi domin ita kaf duniya babu wanda bata so kaman Usman musamman da take ganin shine yasa fahad bai aureta ba

Ita yanzu bata jin komai akan iyayenta domin tasan babu yanda ta iya sune suka haifeta

Hmm rayuwa kenan, lallai Allah shine mai badawa Mai kuma amsa, yau Ina dukiyar Alh Sulaiman wanda yana d'aya daga cikin masu jerin kud'in Africa amma yau an Wayi gari ya koma babu abun, waye zai taba kawo wannan dukiyar tashi zata k'are ba, Allah kenan babu yanda bayayi, saiya kwace Abu daga hannun wani yaba wani

Gadai mahaifin Amal wanda take ganin bazai taba talaucewa ba, domin yana da mugun kud'i sai gashi Allah ya nuna mata

Amal tashi tayi ta haura Sama inda d'akinta na gidan yake, dialing din number din fahad tayi taji switch off, mamaki abun ya bata haka taita kira taji akashe dole hakura tayi badan taso ba

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now