18

993 69 6
                                    

*MILLIONAIRE AMAL*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

                 *PAGE 18*




Amal wani hawaye Mai zafi ne ya zubo daga idonta lokaci d'aya ta tashi Tana k'okarin barin wajan amma jiri ya d'ibeta ta fad'i k'asa luuuuuuu tim

Da sauri suka nufeta cikin tashin hankali, usman ya riga kowa zuwa wajan inda ya fara Girgizata amma ina bata ko motsi

Nan mahaifinta na gaskiya yace Suma tayi a d'auko ruwa

Da sauri wata daga cikin y'an uwan Alh Sulaiman suka nufi kitchen sai gasu Da Ruwa inda aka yayyafa mata tayi firgit ta tashi cikin tsoro Tana kallon su, lokaci d'aya kuma ta fashe da kuka tana kallon hjy Rabi tana fad'in mum dama bake kika haifeni ba??  Ko mafarki Nayi??

Hjy Rabi itama kukan ta kuma saki cikin tausayin Amal din, inda ta kamo hannunta tana fad'in Amal....  Sai kuma tayi shuru kuka yaci karfinta sosai

Amal idonta ya sauka akan matar da itace mahaifiyarta, da sauri ta lumshe ido, zuciyarta na Mata wani iri, atamfa matar tasa amma duk ya kod'e, alaman tasha ruwa, shiko mahaifin Nata wani kodaddan Yadi ne a jikinsa, hawaye ne yake zuba a idonta, yanzu wa Innan ne iyayenta??

Matar da take mahaifiyar Amal ta fara ma mijinta magana da French inda shima ya fara bata amsa da duka alamu dai suna magana ne akan Amal din domin Suna kiran sunanta

Bayan sun gama magana mahaifin Amal ya kalli Alh Sulaiman tare da fad'in munyi magana bai kamata muje da ita ba yanzu, gashi yau akayi aurenta, kawai a kaita d'akin mijinta, mu zamu tafi Idan muka je zamu dawo

Nan Alh Sulaiman yace babu damuwa duk yanda suka tsara hakan yayi

Tafiya sukace za suyi inda Alh Sulaiman yace su kwanta a gidan, da safe sai su tafi, hakan koh ta faru inda aka kaisu wani d'aki

Ita kuma Amal Alh Sulaiman da kanshi yace zai kaita d'akin  mijinta, kuka Amal take Sosai cikin tashin hankali haka Alh Sulaiman ya tafi da ita

USMAN shida kanshi ya wuce inda ya nufi gidan shima

A tare suka k'arasa gidan, Dan haka suka shiga cikin gidan kai tsaye

Amal tana manne jikin mahaifinta Tana kuka wanda shima Alh Sulaiman dauriya kawai yake domin shi d'aya yasan abunda yake ji, dan kirjinshi ji yake kaman zai fito Dan azaba

Haka dai suka shiga Bayan sun shiga suka zauna, gidan amsa komai a cikin sa, kuma gidan yana da girma

Nan Alh Sulaiman ya fara magana kaman haka, Usman ina son ka ri'ke Amal tsakani da Allah, sannan ka zama Mai adalci tsakanin matanka biyu, karka zama d'aya daga cikin maza azzalumai marasa adalci

Nan dai yaita ma Usman nasiha Mai ratsa jiki Wanda yana maganan ne dakyar

Kallon Amal yayi sannan yace Amal Kema ki zama mace Mai biyayya domin Aljannanki tana karkashin kafar mijinki, sannan ki sani aure ba wasa bane, sannan komai kika ma mijinki yaji dad'i zaki samu lada, ina son ki sama ranki bauta kikeyi Kinji??  Dan Allah karki bani kunya kinji Amal

Amal bata ce komai ba sai kuka da takeyi haka Alh Sulaiman yaita musu nasiha sannan ya musu sallama inda Usman ya fita rakashi

Bayan Alh Sulaiman ya tafi koda Usman ya dawo a falon ya tarar da Amal tana ta kuka wani irin son Amal dinne yake fusganshi tare dajin tausayinta Sosai

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now