17

887 65 4
                                    

*MILLIONAIRE AMAL*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

                 *PAGE 17*



*MUNA DA HUMRA DAN SUDAN DASU TURARUKAN WUTA KAYAN GYARAN JIKI NA AMARE KOLECCA MAGANIN INFECTION KAYAN OUM FU'AD AKWAI KYAU SOSAI DA KAYAN GYARAN🙊DUK MESO TAYI MATA MAGANA 08132506044 zakisha mamakin hadin ta,tana turawa kasa kasa kowani gari*







Alh Sulaiman yace kuzo mu shiga ciki in fad'a muku komai, yau zan fad'i abunda na dad'e Ina boyewa wajan shekara da shekaru

Yana fad'in haka yaja hannun amal sukai ciki, wacce jikinta gaba d'aya ya saki

Gaba d'aya su hjy Rabi sun shiga cikin rud'ani tare da damuwa, domin gaba d'aya basu gane Mai yake nufi da abunda ya fad'a ba, dan haka suma suka bishi har cikin gidan

Harda mutanan da suke kiran Amal da y'arsu suka shiga cikin gidan, inda gaba d'aya suka zauna a cikin babban falon gidan

Amal kallon fuskan mutumin tayi inda ta tuna shine dai wannan tsohon Wanda ya kirata da y'arsa Sanda take zuwa skul

Mutumin ne ya d'auko hoto yana nuna ma Alh Sulaiman yana fad'in ka ganta nan wlh y'armu ce Fatima wacce ta rasu

Alh Sulaiman yace wannan ba Fatima bace y'ar uwarta ce

Hjy Rabi tashi tayi tsaye da sauri Tana fad'in Mai kake fad'a haka??  Taya amal zata zama y'ar Uwar y'arsu Bayan bata had'a komai dasu ba, nice nan na haifeta bamu had'a komai d......

Alh Sulaiman ne ya dakatar da ita tare da fad'in hjy Rabi ki gafarce ni, sonki da kuma rashin son in rasaki yasa gaba d'aya na koma mai son zuciya, yasa na aikata babban zunubi na raba yarinya da iyayenta ba tare da sun sani ba, daga ni sai Dr muka San wannan Abun.....

Amal gaba d'aya ji tayi dum dum cikin kanta, Mai Dad d'inta yake nufi???

Saboda tashin hankali da damuwa gaba d'aya ta kasa magana

Dad din yaci gaba da fad'in in baki manta ba, lokacin da nayi accidents a lokacin aka gano kina d'auke da ciki, nayi farin ciki Sosai da wannan labarin

Kwatsam sai Dr yazo min da mummunan labari akan accident din da Nayi na samu matsala akan bazan k'ara haiyuwa ba

Inata ro'kan Allah wannan cikin dake jikinki Allah yasa ki haifa lafiya domin Ina matukar jin tsoran abunda zaisa in rasa wannan cikin dake jikinki

Kuma wani ikon Allah sai gashi bai zube ba, harya isa lokacin haiyuwa, inda na'kuda ya kamaki, mukai asibitin shima a ranan wa Innan bayin Allah aka kawo wannan matar asibti Domin haiyuwa, Wanda wani mai mota ne ya bugeta shine ya kawota asibitin ita da mijinta Wanda a lokacin tare suka fita

Koda suka zo a lokacin Dr yace bazai amshe suba, tunda ba'a nan suke Awo ba, kuma da duka alama zata haiyu ne

Dakyar dai Dr din ya yarda ya amshi matar inda aka kaita d'akin theater domin aiki aka mata a lokacin

Lokacin da kika haiyu kika haifi mace Yarinyar tazo da rai amma wajan gyarata yarinyar ta rasu a wajan nurse Kai tsaye waje tayi inda ta fad'ama Dr

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now