*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 13*
A haka har suka k'arasa gida inda Mum din sadiya keta faman mita akan ita wannan aure gaba d'aya ya fitar Mata a rai, tare da fad'in munanan kalamai akan USMAN ....
Sadiya dai kuka take tayi inda daga karshe taga Abun yayi yawa yasa ta fara fad'in Mum karki manta shifa wannan arzikin na Allah ne, sannan irin namijin da kike so in aura tun tuni ban samu ba, gashi garin biye ma shawaranki har yanzu Banyi aure ba, karki manta na girma a gida,kuma kwata kwata usman shekara nawa ya bani?? Ya kamata ki jinjina masa domin aurena da zaiyi.......
Rufe min baki mara hankali, ke yanzu har kina ganin baki da wanda zai aureki in usman ya fasa???
Toh Bari kiji Idan kina tunanin wannan shirmen Toh ki daina, domin a yau yace ya fasa zan had'aki da irin mijin da kike so, ba sabon kud'i ba irin wannan saurayin naki ba.
Sadiya tashi tayi Fuuuuu tayi cikin d'akinta domin bazata iya sauraran wannan Abun ba ko kad'an, domin har cikin ranta takejin abunda Mum d'inta take fad'a akan Usman din
An fara hidiman bikin Usman da sadiya Wanda Mum d'inta gaba d'aya ta cire hannunta a ciki, Ma'ana bata wani sakin jiki sosai tana hidiman bikin, Abu d'aya takeyi shine dinner din data had'a wanda wannan tasan dole kawayenta suzo shine kawai take aikin shi dakyau
Usman gaba d'aya hidima yakeyi inda Alh Sulaiman ya bashi gudun nawa Mai tsokan gaske, har usman saida yayi mamakin wannan kud'in
Sanda aka Kai akwati, ranan wanda suka kai akwati sun ga wulakanci, sai dai ma an dan raga musu wai nan tunda Anga yasa kaya masu kyau da tsada.....
Duk yawan kayan da suka kai, domin akwati biyar yayi dai dai karfinshi, amma ya zuba kaya masu tsada, dubu biyu Mum din sadiya tace a basu, wai ai matsiyata ne, komai aka basu za suyi murna, haka aka basu 2k babu irin kayan ciye ciyen da ake badawa na kai kayan akwati
Koda y'an kai akwati suka koma Gida, Wata matar dan uwan mahaifin usman take fad'ama Mama irin abunda akai musu
Murmushi mama tayi tare da fad'in suyi hakuri ai dama shi aure a gaji haka, dole sai Anga abunda ba'a so, sai anyi hakuri
Wannan maganan da mama tayi shine ya kashe bakin kowa
Biki ya rage sauran kwana biyu akayi hadaddiyar dinner daya tara manyan mutane, wanda suka amsa sunansu, ciki harda Alh Sulaiman da hjy rabi , ita kam Amal ban tunanin tasan zaiyi aure domin ita dashi da babu duk d'aya ne, ita burinta a kullum shine ma Dad d'inta ya koreshi taga ya wulakanta a duniya
Anci ansha inda ango da Amarya suka sha kyau, sai dai ango yanda yake kaman dariyan Ya'ke yakeyi, domin shi gaba d'aya ya rasa Mai yasa baya jin dad'i ko kad'an, haka dai har kowa ya watse
USMAN shine ya Kai sadiya gida, inda bayan sun k'arasa take cemai naga kaman wani abu yana damunka koh??
Kallonta yayi tare da fad'in kaman ya?? Mai kika gani??
Tace banga komai ba, kawai dai haka jiki na yake bani
Murmushi ya sakar mata tare da fad'in babu komai , sometimes ina tunanin skul ne, sanda kike zuwa kice in koya miki Abu
YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people