*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 6*
Amal fad'i take mahaukacin tsoho, wanda bai San abunda yakeyi ba, tsiyar Talaka kenan, zafin talauci ya sashi hauka, zai zo Ya dinga kirana da y'arsa, waima nice Fatima, "ta Ina na zama y'arsa matsiyaci Talaka dashi.
Usman dai baice komai ba, sai tukin da yakeyi, amma shima Abun ya bashi mamaki, taya zai kira Amal da Fatima harya dinga kiranta da y'arsa? "duk yanda akayi kawai tsufa ne ko kuma kama ce sukeyi da y'ar tasa, wacce yake cewa ta rasu, "Toh In banda abunshi daka ganin mutum saiya Fara kira da Fatima, kuma Bayan yace ita Fatima din ta rasu....
Amal ce ta katse mishi tunani tare da fad'in waya baka daman taba min jiki, da wannan kazamin jikin naka?
Wai Mai yasa kake k'okarin son tabani ako da yaushe? Mai yasa kake son goga min tsiya da talauci? Wannan ya zama na karshe da zaka K'ara tabamin jiki k'azami kawai, Dallah kayi sauri ka kaini gida inje in wanke wannan daudar takaicin daka Shafamin, in banda warin tsiya babu abunda jikina yakeyi
Lokaci d'aya kuma taja tsaki tare da fad'in shi dama Talaka a kullum burinshi yaga ya goga ma Mai arziki tsiya, gaba d'aya warin jikinsa nake Kazami tsaki ta kuma ja
Shidai Usman bai tanka mata ba, domin yanzu ya daina biyema haukarta Dan hauka takeyi domin Mai hankali bazai aikata abunda takeyi ba a cewar shi
Amal sai tsaki take saki tana fad'in aikin banza dana hofi, ko a gidan ubansa na zama Fatima oho, dole Dad yasa a kama wannan matsiyacin tsohon, inma Dad bai d'auki mataki ba dole ni in d'auka "akai bazan fad'ama Dad ba saiya dawo daka tafiyar da yayi amma nida kaina zan fara d'aukan mataki
Bayan sun isa Gida Kai tsaye gefenta ta nufa inda ta fad'a toilet danta wanke tsiyar da take fad'i Usman ya goga mata
Wanka ta shiga ta dad'e a toilet "Tana wanke jikinta cikin kyama da tsanar Usman yanda harya taba mata jiki yana Talaka, Talakan ma Mai mata bauta Dan aikinta, "lokaci d'aya taja tsaki tare da fad'in zan d'auki mataki akanshi cikin gaggawa shima idan ya k'ara yunkurin tabani, matsiyaci
Bayan ta fito ta d'auko mai d'inta ta Fara shafawa tare da shafa turare oil a jikinta, sannan ta d'auko body spray shima ta feshe jikinta dashi, "Fara shinshina jikinta ta farayi "lokaci d'aya taja tsaki tare da fad'in kai har yanzu ina warin jikinshi Kazami
Turaren ta k'ara fesawa amma daka ta shinshina jikinta sai tace Tana warin tsiyar Usman, dole toilet ta kara komawa dan tayi wanka, " ta k'ara daukan lokaci a toilet din Kafin ta fito ta k'ara shafe jikinta da turare bayan tasa Mai
Wata riga tasa wanda ya tsaya mata dai dai Giwa, ko d'ankwali babu akanta ta nufi part d'in Mum dinta
Bayan ta shiga hjy Rabi tace Amal ina hanaki irin wannan shigar karki manta akwai maza masu mana aiki a cikin gidan nan
Tace kai mum miye dan nasa wannan kayan?
Hjy Rabi tace wato ke baki son gaskiya koh? Wlh Amal zanyi matukar saba miki in kina irin wannan banzar shigar
Amal kuka ta Fara tana fad'in waini Mai yasa bakya sona mum? "Dad ne kad'ai yake son abunda nake so yanzu mai shigata tayi
Hjy Rabi ganin tana kuka Kun San y'a da uwa, saita Fara Mata magana cikin sigar rarrashi, "a'a Amal taya uwa zata haifi y'a da cikinta ace bata Sonta? A ina kika taba ganin anyi haka? "kawai Amal irin abubuwan da kikeyi shine bana so, karki manta kefa mace ce, bai kamata kina irin abunda kikeyi ba"sannan irin shigar da kikeyi karki manta masu gadi naza ne, driver d'inki namiji ne, haka masu ba flower ruwa maza ne, Gamai Guga shima na miji ne, kuma duka babu muharramanki a ciki, Kinga bai dace kina irin wannan shigan ba ko kad'an
YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Nouvellesis a story of young millionaire girl, who hate poor people