3

1.1K 72 0
                                    

*MILLIONAIRE AMAL*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*MY BESTY OF LYF HABIBA BUZY*


                 *PAGE 3*





Alh Sulaiman yaji dad'in samun cikin matarshi Sosai, tare da ro'kan Allah yasa Kar wannan ya zube, ko inta haiyu dan ko y'ar su koma.

Alh Sulaiman yayi wajan sati uku a asibiti yana jinya, inda jikinshi yaji sauk'i Sosai, ranan da Dr yazo da niyan bashi sallama "Alh Sulaiman yace Dr ko ina naji sauki sai dai kasana Ina jin wani iri kaman bani ba.

Dr shuru yayi can ya kalli hjy Rabi yace madam dan bamu waje muyi magana.

Alh Sulaiman yace a'ah babu komai, iyalina ce ka fad'a kawai a gabanta

Dr yace OK tare da kallon Alh Sulaiman yace sakamakon had'arin daka samu ka samu ciwo a kasanka Wanda mukai gwaje gwaje muka tabbatar bazaka k'ara samun haiyuwa ba har abada ba.

Wani irin ihu hjy Rabi ta saki tare da kuka, Tana fad'in yanzu Idan wannan cikin ya tafi shikenan baza muga Kwan muba?

Shiko Alh Sulaiman kasa magana yayi, sai Innalillahi'wa inna ilaihirajiun da yake ta faman nanatawa, kanshi na k'asa ya kasa koda motsashi, lallai wannan itace tashi kaddaran, "sai kuma hawaye lokaci d'aya ya fara zuban mishi, "lallai Dan Adam ba komai bane, ba'a gama maka hallita sai ranan daka koma ga Allah, yau gashi irin jarabtan da Allah yayi mishi"dukiya Allah ya bashi kaman hauka, bai masan Mai zaiyi da itaba, amma kuma gashi yanzu bazai iya bama mace ciki ba Innalillahi'wa inna ilaihirajiun.

Lokaci d'aya tausayin matarshi ya kamashi, wanda ta kwallafa rai akan son taga ta haiyu, Koba komai kaima yau ace ga naka dan.

Dauriya yayi tare da fara bama hjy Rabi hakuri akan tabar wannan kukan, tayi hakuri.

Kallon Dr yayi tare da fad'in Dr do whatever but make sure wannan cikin dake jikin iyalina yazo duniya ba tare da wani matsala ba, "plz Dr sai kuma ya fara kuka gwanin tausayi, lallai Allah yakan jarabci bayinsa shi gashi Allah Ya bashi dukiya masu yawa, amma gashi baida y'ay'a, wani kam Allah ya bashi haiyuwan amma babu dukiyar na abinci ma dakyar ake samu.

Wasu kam gudun haiyuwar ma suke, domin basa so

Dr yace kayi hakuri Alh insha Allah zata haiyu lafiya da yardan Allah, ku d'age da addu'a, "kallon hjy Rabi Dr yayi tare da fad'in hjy kiyi hakuri insha Allah zaki haiyu lafiya, wannan cikin naki zaizo duniya insha Allah cikin koshin lafiya

Sai dai ina son ki cire wani damuwa, fargaba ko tsoro, domin hakan zai iya kawo barazana ga cikin, domin Mai juna biyu ba'a so a ganta cikin damuwa

Cikin kuka hjy Rabi ta Fara fad'in Dr damuwa ya zama dole, tunani ma ya zama dole, domin inba ganin wannan cikin nayi yazo duniya ba, wlh banda kwanciyan hankali, na tabbata idan na rasa wannan cikin Zan shiga cikin wani mugun mawuyacin hali, "Ina son ganin ganin jinina, Indai na rasa wannan cikin shikenan kuma.

Dr yace hjy ki kwantar da hankalinki insha Allah zaki haiyu cikin koshin lafiya, sannan wannan baby din zai zo duniya ba tare da wani damuwa ba, "but Ina son ki dinga kula Sosai, banda yawan aiki, banda d'aukan Abu Mai nauyi infact ma duk wasu aiki wanda zaisa jiki ya jigata kar kiyi, "saboda gudun barazana da cikin naki

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now