*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 25*
~LAST PAGE~
Mutane ne makil a wajan wanda suka taru, Amal kam dake kwance gaba daya jini ne ke zuba daga fuskanta hannunta wajan cikinta
Shi kam usman yana rami dashi da motarshi, gaba daya mutane anata magana domin asan yanda za'ayi a ciro shi, jim kadan saiga motar asibiti da security nan aka fara kokarin ciro motar usman wanda wata mota tazo domin ciro motar, ita kam Amal daukanta akayi akayi aka sata a mota domin fara bata taimakon gaggawa
Ansa karfen wanda ya kamo motar harya fara fita motar ta kara fadawa cikin ramin, nan mutane sukai ta salati tare dajin tsoran abunda zai faru
Nan aka kara kamo motar cikin ikon Allah akayi nasaran ciro motar wanda usman ke zaune a baya gaba daya fuskanshi ya canza ya kumbura suntim kaman wanda ya kone, ga jikinshi jini keta faman zuba, sai dai abunda yaba mutanan wajan mamaki shine jin ance bai mutu ba yana da rai wannan yaba kowa mamaki, inda da yawa daga cikin mutanan suke fadin lallai yana da sauran lokaci amma duk wanda yayi wannan mummunan hatsarin toh tabbas ba'a mishi tunanin rayuwa
Nan aka sashi a mota akai asibiti dasu inda ake ta musu taimakon gaggawa, yayin da yan sanda suka fara duba motarsu domin son gano shaidan ko su waye su
An kaisu hspt inda akai emergency dasu domin ceto rayukansu, gaba daya usman ban tunanin ko numfashi yana yi
Likitoci ne akansu inda ake basu taimakon gaggawa, sai dai abunda yaba kowa mamaki, har yanzu usman nada rai bai mutu ba
Police kam Sun gano wayar Amal a cikin motarta sai sai babu wani shaida da zaisa su gane daga inda ta fito, dan haka sukai amfani da wayar domin duba contact dinta
Shi kam usman babu abunda aka gano domin motarshi tayi rugu rugu
Nan aka Fara duba number din Amal inda Suka ga mum kiran number din sukayi bayan hjy rabi ta dauka Suka fada mata tazo waje kaza
Cikin tashin hankali take tambayan police din lafiya maiya faru?? Domin dai taga number din Amal ne kuma ba ita tayi magana ba, haka dai ta dauko hijab cikin tashin hankali inda ta fara tafiya domin zuwa inda aka ce mata
Tun kafin ta karasa gabanta keta faman fadi domin hango wajan koba ta tambaya ba tasan anyi hatsari a wajan, gaba daya hankalinta a mugun tashe yake, haka dai ta karasa wajan
Inda ta nufi wajan police din nan ta fara tambaya gadai motar Amal ta gani glass a fashe ta tabbatar hatsari tayi, nan police Suka mata bayani kuka ta Saki Suka nufi asibiti inda hankalinta ya kara tashi ganin harda usman shima
Gaba daya anyi ma Usman daure daure a jikinsa kuma ana kanyi domin ya samu karaya a jikinsa
Hjy Rabi kuka take Sosai inda ta kira mahaifiyar usman din ta shaida mata abunda ke faruwa
Itama cikin tashin hankali tazo asibtin ganin halinda suke ciki yasa gaba daya Suka shiga cikin tashin hankali
Nan dai sukai zugum suna jiran suji mai Dr zaice musu, an kira sadiya itama wacce ta tsorata da ganin abun

YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Historia Cortais a story of young millionaire girl, who hate poor people