16

916 69 4
                                    

*MILLIONAIRE AMAL*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*ANTY HAUWA S ZARIA MMN USWAN*
~Writer of *MAKAUNIYAR RAYUWA* Ina matukar yinki over, Allah ya k'ara basira da d'aukaka~

                 *PAGE 16*





Usman nufa d'akin yayi amma yaji a kulle, jin k'aran tana fasa abubuwa yasa ya fara buga kofar da sauri tare da kiran sunanta yana fad'in sadiya ki bud'e kofar

Amma ina ko sauraranshi batayi ba, sai k'ara jifa take ta kayan d'akin

Usman Jin yayi bugun duniya ta'ki ta bud'e kofar gashi yana jin k'aran tana fashe fashe yasa yama kofar wani mugun bugu ta balle

Tsayawa tayi turus yana kallonta gaba d'aya ta fashe show glass din dake d'akin tare da mirror d'inta da TV din dake manne a jikin bangon bedroom din

Kuka takeyi Sosai, ganin ya shigo yasa ta Fara k'okarin yin gaba Aiko tasa kafarta akan kwalba tuni ya fashe jini ya Fara fita, wani irin razanannan ihu ta saki

Da sauri usman ya nufeta tare da d'aukanta yayi d'akinshi da ita, inda ya kwantar da ita akan gadon d'akin, wajan kafarta ya nufa ya saka hannunshi ya fara cire mata kwalban dake kafarta

Bayan ya cire still jinin yana zuba, dan haka ya d'auko wata riganshi ya d'aura mata a wajan, jinin ya tsaya, ya daina zuba

Tashi yayi ya koma kusa da ita, tare da zama ya kura mata ido wacce hawaye ke zuba a cikin idonta

Sunanta ya kira da sadiya

Bata amsa ba sannan bata kalleshi ba

Bai damu da hakan ba, burinshi dai shine ta saurareshi

Yace sadiya ban taba tunanin haka daga gareki ba, da Farko Nayi tunanin zaki supporting d'ina a duk abunda na Kawo miki, zaki Mara min baya, sai gashi ba haka ba, Allah shine shaida bani da niyan kuntata miki ko kad'an, ban taba tunanin cutar dake ba, wannan Abun daya faru ban kwana dashi ba, ban San Zai faru ba, hasali ma naje ne taron biki, sai Abun ya canza, ina son ki sani ban taba tunanin cutar dake ba, sannan ina son ki d'auka komai ya faru daga Allah ne

Sadiya kuka takeyi Sosai, amma wannan maganan na Usman jinshi kawai take bawai tana sauraro ba, domin gaba d'aya zuciyarta tana fad'a mata Usman ba gaskiya yake fad'a mata ba, dan idonta ya rufe a wannan lokacin, tana bala'in son USMAN tare da kishin shi, zuciyarta wani irin zugi yake mata tare da rad'adi

Usman jin har yanzu tana kuka yasa ya d'agota tare da fad'in sadiya kibar wannan kukan dan Allah, kinga duk kin fasa abunda ke cikin d'akinki gashi Kinji ma kanki ciwo, kinki kibar wannan kukan kuma, plz ki bari haka, kanki zaiyi miki ciwo

Cikin kuka tace ai komai ciwo yake min, wlh Usman komai dake jikina ciwo yake, wani zunubi na aikata haka? Da zan fuskanci wannan sakayyan, yau ko wata uku banyi ba amma ace har anyi min kishiya, taya jikina bazaiyi ciwo ba??

Usman jikina yana bani y'ar soyayyar da kake min zaka daina, yanzu shikenan na rasa ka....... Kuka yaci karfinta Sosai

USMAN gaba d'aya tausayin sadiya ya kamashi Sosai, rungumota yayi Sosai jikinshi sannan ya fara fad'in sadiya bazan daina sonki ba, karki manta ni mijinki ne, sannan abunda mata bakwa ganewa shine idan namiji ya k'ara aure sai kuga kaman Wai baya sonku ne, which ba haka bane, namiji bazai zauna da macen da baya so ba, k'arin aure bashi bane Idan namiji yayi ba za'ace baya son Uwar gidansa ba, yana son matarshi kawai k'arin auren kaddara ne wanda Allah yasa dole saiya k'ara, kuma Allah ya rubuta mishi dole saiya ajiye mace fiye da d'aya

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now