15

950 69 5
                                    

*MILLIONAIRE AMAL*

*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*PAGE 15*

Bayan an gama d'aura aure nan aka fara taya usman murna, tare da Alh Sulaiman

Bayan sun fita Kai tsaye gidan Alh Sulaiman suka nufa inda akwai mutane y'an biki da suka cika gidan Anata hidiman biki, wanda duk mata ne a cikin gidan ba maza ba, duka sunzo taya su murnan biki

Alh Sulaiman haka ya ratsa ya shiga cikin gidan shida usman wanda sukai d'akinsa kai tsaye, Bayan sun shiga k'iran hjy Rabi yayi a waya tare da fad'in tazo ita da Amal

Ba'a dad'e ba saiga hjy Rabi ta shigo ita da Amal wacce take murna Domin tasan by now ta zama matar fahad, duk da ta kirashi yana ta danna mata busy

Amal ganin Usman cikin d'akin Dad d'inta yasa duk wani annuri dake fuskanta ya dauk'e

Lokaci d'aya tace Dad mai wannan yakeyi a nan??

Alh Sulaiman yace ki sami waje ki zauna

Amal cikin bacin rai tace Dad bazan zauna wajan da wannan ya zauna ba, Dad karka manta ko Waye shi, dahar ka bari Ya shigo maka cikin bedroom only god knows mai zai aikata, tayu harda had'in bakinsa mutanan nan suka cucek.....

Tas ya sauke mata Mari a fuska cikin zafin rai....

Kallon mahaifin nata tayi cikin mamaki tare da fad'in Dad nika mara akan wannan kaskantaccen, akan wannan Talakan ka mareni??

Alh Sulaiman yana K'okarin k'ara marinta usman ya tare shi tare da bashi hakuri akan ya barta yarinya ce

Amal tace ai dole kace haka, tunda ka mallake min Dad, sai abunda kace mishi

Alh Sulaiman wani siririn hawaye ne ya zubo a fuskanshi

Ganin haka yasa jikin amal yayi sanyi bakinta Ya mutu ganin hawaye a fuskan mahaifin nata

Alh Sulaiman yace Amal ban taba tunanin halinki yakai haka ba, har zan baki umarni kiyi shuru amma k'iki yi, nuna Usman yayi tare da fad'in shidai wannan da kike kira Talaka yayi miki rana, sannan wannan da kike kira hala harda had'in bakinsa aka cuceni bazan taba yarda ba, domin na yarda da Usman fiye da kaina.

Usman ya cinye jarabawata da dama Wanda ban taba tunanin zai cinye ba, domin irin jarabawan dana mishi ba kowa zai iya cinyewa ba, amma sai gashi Abun mamaki ya cinye jarabawan cikin sau'ki

Yau fahad yaci min mutunci a bainan dubban jama'a, inda ya tozarta ni, tare da kin aurenki.....

Amal wani irin kuka tasa tare da fad'in Dad anya fahad ne kuwa??

Alh Sulaiman yaci gaba da fad'in amal yau inda kina wajan na tabbata da kin gane Waye shi

Nan ya fad'a musu irin rashin mutuncin da fahad din yayi mishi

Sannan ya k'ara da fad'in Amal daga lokacin da fahad yayi min tujara na tabbata ina Raye ne domin inga aurenki.....

Dan shuru yayi sannan yaci gaba da fad'in Amal nasan ba wani lokaci zan k'ara a cikin wannan duniyar ba, na tabbata ko yanzu na mutu bazaki wulakanta ba domin na bada ke inda za'a ga darajan ki sannan a mutunta ki, Amal ko Bayan raina ban yarda ki saba ma mijinki ba, ina son ki zamo mace Mai biyayya wannan kad'ai za kiyi ki nuna min ke y'ata ce

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now