22

974 54 7
                                        

*MILLIONAIRE AMAL*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

                 *PAGE 22*



Koda suka fito daga cikin jirgi fita sukayi waje, inda Amal ta kalli mahaifiyarta tace yanzu Ina zamu dosa??

Mahaifiyarta tace toh gadai ni nan ne dai

Amal ta kalli mahaifinta tace Abba Ina tunanin mu fara zuwa wajan iyayenka, kaman hakan zaifi kafin muje gidan su mama

Mahaifinta yace Nima haka nake tunani, nan suka tsaida mota suka shiga inda suka nufi gidan mahaifin Amal

Cikin ikon Allah duka sun sasanta da iyayensu, komai yayi dai dai sun nemi gafaran iyayensu, inda suma iyayen suka amshi laifinsu na d'aukan al'ada da muhimmanci akan addini, inda sukai tajan Amal a jiki

Amal ta saki jiki dasu kaman ba ita ba, Tana ta shiga cikin y'an uwan iyayenta, sunsha yawo Sosai, inda ta tabbatar ita y'ar dangi ce gaba da baya

Ta lura iyayen mahaifiyarta talakawa ne, amma dangin babanta suna da hali Sosai

Kakannin Amal sunce iyayenta bazasu koma Nigeria ba, a nan zasu zauna, a saman mishi aiki domin ya farayi

Nan mahaifinshi ya basu gida inda suka koma can, amal satinta d'aya kullum tana tunanin usman, gashi basuyi waya ba, dan bata samu ta siya sim ba, gashi kullum basa zama, dan haka yau dole ta siya sim Domin tayi magana dashi

Bayan sun fita ita da wata y'ar yayan mahaifiyarta, tace zata siya sim

Bayan ta siya ta k'osa su koma gida, domin tayi magana dashi

Koda suka koma d'aki ta shige inda ta kira Usman din

Harya tsinke bai d'auka ba, shuru tayi tana tunani ko ina ya shiga oho

Tana cikin tunani saiga kiranshi ya shigo cikin wayarta, da sauri ta d'auka

tare da fad'in hello

Yace sai yau aka tuna dani??

Tace uhm uhm ban siya sim bane sai yau na siya

USMAN yace OK yasu Mama??

Tace lafiya

Nan ya fara tambayanta hope komai dai lafiya??

Tace eh, tare da furta Kalman ngd sosai da kulawa

Murmushi yayi tare da fad'in cikin ranshi Wai Amal ce yau take mishi magana haka.....

Katse Mai tunani tayi da fad'in naga yan uwana da dama, harda kakannina, naji dad'in had'uwa dasu Sosai, a baya na d'auka kud'i shine komai Amma a yanzu na gane zuri'a shine komai, babu abunda yakai dangi talakawa ko masu kud'i, nida kaina Ina jin kunyan kaina akan abunda na aikata a baya......

Usman ya katseta Da fad'in Alhmdlh Amal Ina Mai farin ciki da kika gane hakan, Amal ba komai kud'i yake badawa ba, mutunci yafi komai akwai abunda kud'i bazai miki ba amma mutunci saiya miki shi

Allah yasa mu dace

Ta amsa da Ameen tare da fad'in Ina Dad d'ina da fatan yana lafiya domin Nasan Mum bazata fad'amin yana yin jikin ba

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now