*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 20*
*Gamai bukatar sauraran Littafin bariki na fito, da bak'in Aljani, da Littafin jawaheer audio, kuyi searching ~AL'AMARIN DUNIYA TV~ A YouTube zaku dinga samun abubuwa da dama, irinsu maganin k'arin ni'ima da sauransu, subscribe the channel plz*
Amal idonta nakan matar cikin damuwa, tace mama maiya faru
Matar ta Nisa sannan tace zan fad'a miki, duk da banso ki sani ba, amma nasan dole gaba ki sani, musamman da muke shirin tafiya gida domin mu nemi gafaran laifin da muka aikata
Mu y'an asalin garin Niger ne, inda muke zaune a zender, sunan mahaifina Mlm Ibrahim mahaifina Talaka ne Sosai bashi da karfi mu hud'u ya haifa, yayyina uku maza saini daya mace, duk wani son duniya iyayena Sun d'aura min musamman ma mahaifina da baya iya boye irin son da yake min gashi sunan mamanshi aka samin wato kakata, Maryam, ita mahaifiyata Tana boyewa saboda kawaici Kar ace ta cika son yara, haka yayyuna maza suke nuna min so, a lokacin ba'a karatun boko, wama ya wani san da boko balle Ayi, sannan muna da wata al'ada Wanda mukeyi, tun kina yarinya ake bada aurenki a garin, Nima hakan ta faru dani aka bada aurena, mu bamu san wani soyayya ba, toh Wama yake da lokacin soyayya, sai dai kawai a d'aura aure kwayi soyayyan a d'akin keda mijinki
Toh sai dai nida na Fara tasowa sai Mai?? Na had'u da wani mutum Mai suna Abdallah, Abdallah dan yamein ne shima duka a cikin k'asar Niger yake, abdallah yayi karatun boko har gaba da secondary iyayenshi masu hali ne yazo wajanmu bautar k'asa a wani makarantar da gwamnati ta gina wanda yara basu fi mutum ishirin ba a duka makarantar, domin a lokacin an fara wayar ma jama'a dakai akan ilimin boko,
Nidai iyayena basu sani ba, domin su basa ra'ayi ko kad'an a cewarsu su basu yarda da wani karatun boko ba
Wata rana na fita babban yayana Mai suna Umar ya aikeni siyo mishi sukari na fita Mai shagon dake kusa baya nan inda nayi gaba, a nan na had'u da abdallah inda na bada kud'i aka bani sikari, shiko Ashe a lokacin yaji yana sona, koda na amsa nayi gaba nan ya biyoni, da yake dan boko ne yana da wayewa, saiya wayince Inda ya nuna min kaman yana tambaya ne...
Daga wannan rana abdallah ya shigo cikin rayuwata, inda mukai mugun sabo, ashe wannan sabon sonshi ne ya kamani wanda har takai sanda ya furtamin abunda ke ranshi na amince, wanda gaba d'aya na manta da irin al'adan garinmu, na kuma Manta da an bada ni, wannan al'adan a garinmu ana matukar muhimmanta shi, tun iyaye da kakanni akeyi, kuma har lokacin ba'a samu wanda ya musa koya bijire ma wannan al'adan ba sai a kaina wanda hakan yaja min mugun matsala tare da fushin iyayena akai na, inda shima abdallah ta gefenshi Ashe an Mishi mata shima ya bijire akan shifa baya so ni yake so
Hakan nima ta gefe na, inda iyayena suka juyamin baya aka matso da maganan biki na, inda shima ta gefen Abdallah aka fara shirin nashi bikin, wani abun kaman had'in baki, abun ya kasance rana d'aya, ana gobe za'a d'aura aure abdallah yazo ya d'aukeni inda yace mu gudu, da Farko naki yarda inda ya nunamin indai ban bishi ba shikenan an rabu mu har abada
Ganin dagaske hakane yasa na bishi muka bar k'asar inda muka zo Nigeria muka sa aka d'aura mana aure, Nigeria da Niger ba d'aya bane, mu French muke su English wannan dalilin yasa takardanshi baiyi amfani ba, daga baya ya fara neman teaching shima akace dole sai yana jin turanci ganin Abun bamai yihuwa bane yasa ya hakura, inda dan kud'in daya dibo muke ta amfani dasu, ya siya min kaya kud'in Haya abinci duk a ciki
YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people