23

984 63 13
                                    

*MILLIONAIRE AMAL*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

                 *PAGE 23*

Amal tuk'i take cikin tashin hankali tare dayin sauri domin ta k'arasa wajan fahad....

Lokaci d'aya kuma ta taka burki kaman ance ta tsaya, a tsakiyar titi ta tsaya inda motoci suka fara Mata horn ganin ta'ki motsi da motar balle ta fito yasa motocin suka fara kaucewa Domin suna tunanin motar ta lallace ma Mai tu'kata ne...

Amal kam duniyar tunani ta fad'a domin tunawa da irin abunda fahad ya aikata ma mahaifinta kafin ya rasu inda ya tozarta shi, har tana ganin kwallan dake fuskan dad din nata sanda yake magana, kaita girgiza tare da fad'in bazan yarda dakai ba, bazan yarda in ganka ba, I don't trust you

Lokaci d'aya ta juya motar ta koma Gida inda ta jefar da wayar tata a falo tayi cikin bedroom d'inta ta kwanta kanta na faman Mata ciwo, zuciyarta na sa'ka mata abubuwa da dama, tabbata fahad k'arya yake fad'a, domin mutuwar mahaifinta inda wani ne ya kashe shi kaman yanda Ya fad'a Toh data tabbata Mum zata Sani domin bata nesa dashi, toh wama zai kashe Dad mutumin da baida abokan gaba...  Tana nan kwance tana jiyo k'aran wayarta tasan dai kiran bazai wuce na fahad ba dan haka taki tashi

Lokaci d'aya kuma ta tashi tunawa da tayi usman zai iya kira shima

Kai tsaye wajan wayar ta nufa Aiko tana d'auka saiga kiran usman ya shigo, dauka tayi fuskanta d'auke da murmushi tare da fad'in hello...

Yace my dear gani nan zuwa gida yanzu hope you are ready for me??

Bata san lokacin data saki murmushi ba duk da tana cikin damuwa

Yace Mai zan Kawo miki

Tace nothing just kawai Kai nake son gani....  Tana fad'in haka ta kashe wayan tana dariya

Ko minti biyu batayi da kashe wayan ba saiga kiran fahad cikin wayar kaman Karta d'auka sai kuma ta d'auka domin tayi warning d'inshi akan karya k'ara kiranta amma tana d'auka taji abunda saida Ya kusan kaita k'asa... 

Fahad yace Amal am try to help you, Amma kinki yarda Toh let me tell you ba kowa bane ya kashe Dad d'inki ba sai mijinki Usman wanda yayi sanadin min barazana domin in rabu dake Dan dole saboda ya aureki....

Amal bata san lokacin da wayar ta fad'i a hannunta ba domin firgici, Usman shine ya kashe Dad d'inta???  Innalillahi'wa inna ilaihirajiun sai kuma ta saki kuka Sosai Mai karfi tare da sauti

Wani kiran ne ya kuma shigowa cikin wayarta  ganin Sunan Usman yasa ta danna mishi Bussy tayi rejecting kiran, k'ara kira akayi taga fahad ne d'auka tayi da sauri takai kunnenta

Fahad yace Amal inada e......  Katse shi tayi

Tace fahad I don't trust you Usman bazai taba kashe dad d'ina ba, domin Nasan Waye shi duk da bana shiri dashi nasan halinshi Mai Kyau ne...

Fahad yayi dariya tare da fad'in Amal Kina da zuciya mai kyau, but Amal trust me har yanzu ina sonki USMAN ne ya rabani dake, Amal inada evidence I will show you the evidence Indai kika zo inda nake, zaki tabbatar da abunda nake nufi

Just trust me, usman ne ya kashe miki dad d'inki, Amal inda bana sonki dana amshi kayan akwatin dana Kawo miki Just think, think Amal...

Kashe wayan yayi inda Amal ke zaune tana faman tunani akan maganan fahad

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now