5

985 57 0
                                    

*MILLIONAIRE AMAL*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

                 *PAGE 5*





Usman kai tsaye cikin gidansu Amal ya faka motar, "koda ya faka idonshi ya sauka akan Nata ta mirror itama lokacin akai Sa'a ta d'ago idonta

Wani uban harara ta sakar Mai, tare da fad'in "lafiya kake kallona? Kaman tsohon Maye.

Kufa naga alama talakawan nan Kun fiye kallon mutane, "ka wani sakar min ido kaman zaka cinye ni, Toh nafi karfinka wlh, wahallan mutum kawai, tare dajan tsaki tace fita ka bud'emin kofa jorr

Usman baice komai ba, sai fita da yayi ya bud'e Mata kofar, "domin daka yanzu yayi alkawarin zai maidata mahaukaciya ne In Tana Abu yabar biye mata, sai dai yaita manna mata hauka, "uhm Allah yasa ka iya hakurin dai

Bayan ya bud'e Mata kofar ta fito, "sannan ya rufe kofar,"kallonshi tayi k'asa da Sama riga ne da wando na wani yadi a jikinsa

Tace anjima by 6pm ka shirya cikin shiga Mai Kyau zaka fitar dani, "Ina nufin ban son kasa irin wannan kayan dake jikinka domin ban San driver d'ina yana dressing like a beggar, duk da dama u r a beggar din "sai kuma ta saki murmushi tare da fad'in Talaka bawan Mai kud'i, "Tana fad'in haka tayi gaba abunta

Usman yaji haushin magananta amma saiya basar, tunda ba dukanta zaiyi ba, dole Dai sai dai yayi hakuri.

Usman wajan masu gadin gidan ya nufa ya zauna inda suka fara fira, "d'aya daka cikin masu gadin yace kai Usman Wlh kana k'okari Sosai

Usman yace k'okarin me kuma?

Security din yace wajan tu'ka Amal mana, wlh bata da kirki ko kad'an batai halin iyayenta ba wlh yarinya bata ganin girman kowa hab.....

Usman ya dakatar dashi tare da fad'in ya isa haka, karka manta a karkashin su muke, bai kamata mu dinga gulmanta ba, kodan iyayenta ya kamata mu dinga hakuri

Security din yace hakane, gaskiya ka fad'a, "Allah ya bamu hakurin zama da ita tare da jurewa, "amma halinta sai ita Allah ya shiryata, ta gane Talaka shima mutum ne kaman kowa

usman ya amsa da Ameen tare da fad'in bari dai inje inyi Guga

Security din yace AI an kawo sabon Mai Guga, yanzu kana karkashin Amal ne, kaine driver d'inta, aikinka shine tu'kata

Usman shuru yayi yana nazari, "gaskiya baya tunanin zai jure, domin yasan duk yanda yakai da hakuri da kuma Kai zuciya nesa yasan Amal zata iya kureshi, "amma zai jaraba ya gani

Tun daka wannan ranan Usman ya zama shine driver Amal, babu wulakancin da baya gani, "babban abunda yake damunshi shine yanda yake yawan tunanin Amal, sannan ba kaman daba Wanda yanzu Idan tayi mishi Abu baya wani jin haushi Sosai, sai dai kawai ya bita da ido

Ita kuma ta gefen Amal babu abunda ta tsana kaman taga tana mishi abu yayi shuru yana kallonta

Shi usman baya jin komai game da ita, balle yace yana Sonta, sai dai abu d'aya da ya tabbata shine yanzu yana matukar jin tausayinta, domin irin rayuwar data d'aukar ma kanta abun a tausaya mata ne, gaba d'aya lamarinta babu Allah, "domin inda tasani da bata kyamaci Talaka ba, domin Allah ne yayi su, kuma shi talauci jarabawa ne, haka arziki shima jarabawa ne duka.

MILLIONAIRE AMAL Where stories live. Discover now