*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*MAMAN USWAN*
~writer of *MAKAUNIYAR RAYUWA* Allah ya k'ara miki basira tawan, Allah ya bar zumunci, ina matukar godiya gareki, wannan page d'in naki ne kiyi yanda kike so dashi~*PAGE 11*
Usman gida ya nufa kai tsaye inda ya Tarar da mahaifiyarshi tana aikin dafa abinci, zama yayi tare da fad'in mama sannu da gida
Mama ta amsa tare da fad'in har an shigo? Ya aikin?
Yace Alhmdlh, ya kamata dai ki Fara shiri domin mu koma gidana, inda so samu ne ina son ki riga komawa Kafin Ayi biki
Mama tace a'a Usman bazan zauna a gidanka ba, domin ina jin tsoran zama da Sirika, gwara in zauna a nan, yafi min
Usman yace mama haba, Indai bazaki zauna a inda nake ba, miye amfanin samu na?? Dan Allah ki Fara shiri mu koma
Mama tace uhm USMAN bazaka fahimta ba, amma ina son kabar wannan maganan kawai
Usman shuru yayi domin yasan wacece mahaifiyar tashi, Indai ta dage akan Abu, sannan ita mutum ce wacce bata son shiga sabgar kowa, mace ce mai hakuri ga saukin Kai, sai dai fah tana son usman kaman ranta bata had'ashi da kowa
Amal kam koda Dad ya shiga ciki a falo ya ganta Tana ta sintiri wanda hakan ya nuna mishi daka duka alama shi take jira
Aiko tana hango mahaifin Nata ta nufeshi tare da fad'in Dad yanzu akan wannan banzan driver din kake ganin kaman Fahad shike da laifi? Dad Ina son ka koreshi daka aiki domin bana bukatar ya tuk'ani haka kaima Dad naga kana da dri...
Alh Sulaiman ya dakatar da ita tare da fad'in ya isa haka amal, Usman yanzu ba driver d'ina bane, haka Kema yabar miki aiki domin kuwa yana aiki a company d'ina as my PA personal assistants
Amal tace what?? Dad your PA that poor guy, my driver become ur PA how.... Shuru tayi tana jimami tare da nanata Kalman PA lokaci d'aya kuma ta zauna akan kujeran dake falon sannan tace Dad mai yasa zaka bashi wannan muk'amin Dad karka manta shifa Talaka ne inya samu dama he can do anything, Dad karka taba barin Talaka ya rabeka ka barshi yaita shan wahala ta yanda zai gane banbancin Mai arziki da Talaka
Dad plz just for my happiness ka koreshi plz Dad I hate him....
Dad yace amal inaso ki san wani abu d'aya, Usman ya zama yaron dana yarda dashi, domin na gwadashi na gane ba macuci bane, dan haka na yarda dashi yau koda bana Raye na tabbata zai iya ri'ke mun ku tare da kular muku da abunda na bari duk da bani da tabbacin Kafin in mutu ko zan bar wani abu, duba da irin yanda rayuwa take tafiya, babu yanda Allah bayayi sai kiga mai kud'i ya tsiyace Talaka yayi arziki, Allah kenan babu yanda bayayi, saika tara dukiyar daka karshe ciwo ya kama ka, haka za'ayi ta nema maka lafiya cikin abunda ka tara, in bakai Sa'a ba aita neman maganin Ka'ki warkewa har abun daka tara ya k'are
Toh Kinga shi Allah babu yanda ba yayi, dan haka Ina So ki sani Amal ke d'aya ce y'ata dana mallaka, da yawa zasu zo Wajanki ne saboda abunda na tara, ke yarinya ce baki San mai duniya ke ciki ba, ni mahaifinki ne zan iya sadaukar da komai just for your happiness, amma ina son ki sani ya kamata kima kanki karatun ta nutsu ki gane Allah shine mai azurtawa shine mai hanawa, sannan zai iya kwacewa daka hannun wanda yaba, sai kiga ya azurta Wanda bashi dashi, damai arziki da Talaka duka bayin Allah ne, wajan Allah duk d'aya muke babu banbanci
YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people