*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*HAJIYA NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
*PAGE 9*
Amal cikin gida ta koma Kai tsaye, da gudu ta k'arasa falon gidan inda ta iske hjy rabi a falon, cikin murna take fad'in Mum mum kalli irin kyautar daya bani
Hjy Rabi kallon zoben da yaba Amal tayi Wanda kallo d'aya tasan zoben ya haura Million 8, tace amal dan Waye ne yaron??
Amal tace Wlh Mum ban sani ba, yadai bani kyauta, sannan abunda na sani shidai Dan kasuwa ne, bai cika zama a Nigeria ba, domin business d'inshi gaba d'aya a waje yafi yi
Mum tace ikon Allah, amma wannan kyautar daka had'uwa baki gama sanin koshi waye ba
Amal tace kai mum koni da kaina zan iya siya fah, ni a wajena ba komai bane danya bani zoban nan ba, hakan da yayi ya nuna yana sona, tunda kalli fa irin kyautar da yayi min.....
Shigowan USMAN falon tare da sallama yasa amal yin shuru tare da kallonshi cikin shiga Mai Kyau wanda ya bata mamaki.
USMAN gaida hjy rabi yayi tare da fad'in nazo amsan file din
Alh Sulaiman ne ya aikoshi amsan file wajan hjy Rabi wanda ya manta dashi a gida which is very important, gashi yanzu zasu shiga meeting an nemi file din an rasa, shine ya tuna Ashe yana gida bai d'auko ba, shine ya Aiko USMAN yazo ya amsa
Hjy rabi Bayan ta amsa gaisuwar tace OK Bari inje in d'auko maka
USMAN ya amsa da Toh
Tashi hjy rabi tayi tare da nufa sama danta d'auko mishi
Amal tunda ya shigo ta watsa mishi wani irin kallon tsana, ita a nata tunanin yana tu'ka dad ne kaman yanda yace ta bashi Aron shi,
USMAN kam gaba d'aya Satan kallonta yake, yana jin wani irin Abu a kanta wanda bai taba jiba sai yau, da sauri ya Fara kwaban zuciyarshi akan ta daina yaudaranshi domin har abada Amal ba sa'arshi bace tafi karfinshi nesa ba kusa ba
Fitowan hjy rabi ne yasa ya dawo daka duniyar tunanin da yake ciki, inda ta mi'ka mishi file din tare da fad'in gashi ka kai mishi USMAN
Amsa yayi tare da fita, tuk'i yake yana kallon fuskan Amal da sanda guy dinnan ya kamo mata hannu yasa mata zobe da sauri ya taka burki ya tsaya tare da ajiyan zuciya...
Usman ya dad'e a tsaye Kafin yaja motar yayi gaba, lallai ya kamata ya cire ma ranshi wannan tunanin, hanya d'aya ya kamata yabi shine ya amsa ma Sadiya domin dai ta cire kunya ta fad'ama Usman kudirinta, tun daka lokacin ya danja baya da ita domin Baya Sonta, inda ya kawo uzuri da fad'in baida aiki, har tace ita shi takeso sannan in baya son aikin soja zata sama mishi wani, Toh daka baya kuma ya samu aikin company din Alh Sulaiman inda ta k'ara mishi magana Yadai nuna mata tayi hakuri, amma still tana kiranshi akai akai suna magana
Usman yana tuk'i harya k'arasa office inda yakai ma alh Sulaiman file din aka shiga meeting
Bayan sun fito daka meeting inda Usman ya koma nashi office din, zama yayi yana tunani tabbas ya kamata ya auri sadiya, zaisa aje a nema mishi aurenta
Hakan ko akayi usman yama k'anin mahaifinshi magana inda aka tura gidansu sadiya an kuma amince an bashi ita
Usman ganin Idan yayi aure zai manta da amal amma kullum kaman kara Sonta yake, Abun yana matukar damunshi Sosai, sai dai in yana waya da sadiya yakan manta da amal din, domin tana mishi kalamai masu dadi daka sun gama wayar kuma saiya fara tunanin amal
YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people