*MILLIONAIRE AMAL*
*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)**https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*
*http://WWW.Maryamobamnovels.com*
*Wattpad@ Maryam-obam*
*Instagram@maryam_obam*
*DEDICATED TO.....*
*MY LOVELY MUM*
*PAGE 4*
lokacin da Amal ta shiga shekara Goma sha d'aya a duniya, "a lokacin zata shiga JSS1 inda ta kafe ita baza tayi secondary skul a k'asar nan ba, domin y'ay'an masu kud'i waje ake kaisu karatu,"inda tace yawanci y'ay'an talakawa ne suke karatu a wannan k'asar, taya ina y'ar mai kudi ace zanyi karatu cikin wannan k'asar?
Daddy ganin yanda tilon y'ar tashi ta dage yasa ya amince Amal taje waje tayi karatu.
Amma mamanta hjy Rabi wacce take kira da mum inda ta kafe Amal bazata waje karatu ba, "inda tace a nan ya aka kaya balle taje wata k'asar karatu?
Amal tayi fushi Sosai tata ta yanke, inda ta daina kulata na wani lokaci, "domin a cewarta uwarta bata Sonta, tunda bata son abunda take so, "Dad d'inta ne kad'ai ke Sonta, tunda shine yake mata abunda take so..
Bayan Amal ta Gama fushinta da Mum dinta, taje ta sami Mum dinta a d'aki akan ta barta taje waje karatu, bata son yin karatu da yaran Talakawa, musamman makarantur masu kud'i ana bama yaran talakawa scholarship
Mum tayi murmushi tare da kallon y'ar tata, tace Amal, kiyi hakuri ki duba ko wata makaranta Mai tsada sai kishiga
Tashi Amal tayi rai bace ta fita, domin tasan tunda mum ta kafe Toh ko zata mutu bazata Bari taje waje karatu ba, "wannan dalilin yasa Amal hakura amma fah badan taso ba, dan dai Anfi karfinta ne babu yanda ta iya.
Amal an shiga skul, tunda ta shiga bata hulda da kowa sai wata yarinya mai suna afra, wacce itama babanta mahaukacin Mai kud'i ne, ya ri'ke ma'kamai da dama, "wannan dalilin shine yasa Amal ke shiri da ita, "duk da makarantar yaran masu kud'i ne y'ay'an wance da wane "amma Amal ganinsu take kaman talakawa tunda tasan Daddy d'inta yafi nasu kud'i, tunda yana cikin masu kud'in Africa na y'an kasuwa na hudu yana son zama na biyu a halin yanzu domin kasuwancin shi yana ja Sosai
Tunda Amal ta shiga secondary school ta k'aro wani wulakanci, "Ga wani shegen son girma, "ko kad'an bata son raini, tasha Koran masu aikin gidansu akan laifi kalilan Wanda bai taka kara ya taka ba "yayin da wasu suke gudawa da kansu domin cin zarafin su, da takeyi, da kuma magana mara dad'i, ta dinga fad'in shi dama Talaka haka yake, "burin Talaka yaga mai kud'i ya wulakanta, toh ta Allah ba taku ba,tunda kuka zo a talakawa dole kuyi mana biyayya.
Lokacin da Amal ta cika shekara Goma sha uku a duniya, daddy d'inta ya shirya Mata wani haddan birthday party, inda tayi inviting Friends d'inta, An kashe dukiya Sosai, "a lokacin mahaifinta ya Mata kyautar da yaba kowa mamaki, inda ya mallaka Mata kud'i Naira million d'ari biyu da hamsin cikin account d'inta, "sannan yace ya bata kyautan gida a duk state din da take so a cikin Nigeria, sannan ya kara da fad'in Akwai tanadin da yayi ma y'arsa amma sai wani lokaci zai bayyana.
Rungume daddy dinta tayi tana murna, tare da fad'in "this is d best gift ever"you are d best daddy in d world
Hjy Rabi kam bata so yaba Amal wannan kyautar yanzu ba, "taso sai tayi aure ya bata, domin tana da rawan kai, gashi yanzu an bata wannan kud'in ta tabbata sai abunda ta gani yanzu
Tun daka wannan lokacin Amal ta k'aro wulakanci, tare da raina kowa, da kuma kallon kowa a d'age
Akwai sanda tama teacher d'insu raini harta zageta, "da yake skul din y'ay'an masu kud'i ne ba'a duka, shine akace tayi kneel down, a matsayin punishment d'inta.

YOU ARE READING
MILLIONAIRE AMAL
Short Storyis a story of young millionaire girl, who hate poor people