CAPTAIN SADIQ
👮🏼written by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Blood sister deejah📘REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM 🐄
1_2
Yarinya ce yar shekara 10 na hango, tana tafe tana rusa kuka kamar anmata mutuwa, fara ce sosai ita ba siriri ya ba, ita ba lukuta ba, d'ankwallinta ne a hannu hakan ya sa na kalli gashin kanta, bak'i ne sosai amma saboda tsabar datti yayi jawur, kallo d'aya na mai na gane mai laushi ne, rashin kullawa ne yasa yayi haka, Hancin ta yayi jaga-jaga da majina, gata da manyan ido,tana tafe tana kukan, dan ba dainawa tayi ba, dai-dai wani madaidaicin gida ta tsaya chak, gidan kasane natallakawa sosai, dan ko k'ofar gidan bata samu ishashiyar kofa ba, Ihu ta Kara saki kamar an watsa mata ruwan zafi, inna da ke kurya d'aki ta fito tana gyara zani, inda sabo to ya kamata ta saba da halin fatuha, amma ba yadda ta iya dole ta fito inba fitowa tayi ba to wallahi sai dai maqota su fito, ganin inna ta leko yasa fatuha tuma a k'asa tana ihu.
inna ta gyara tsayuwa. ta ce, "ohni fatuha nabani yau kuma wakika tsokana kika ci duku, fatuha ciki murya tsiwa irin na yara masu wayau masu rashin ji ta ce "inna wallahi tallahi kwarankwatsi dubu bani na tsokane shi ba inna" ta k'ara rushewa ta saban kuka inna ta san halin ta sarai shiyasa ta ja bakin ta tayi shuru can kuma ta ce, "to fatuha waya bige ki?
"wallahi inna Rabi'u ne ya bigeni har da taka min ruwan ciki" ta k'ara rushewa da saban kuka kuma inna billahilazi ba zan yarda ba" ta inda zancan tana katse majina hancin ta saboda inna ta san karya irin ta fatuha tasan ba yarda za'ayi rabi'u ya bige ta har ya taka mata ruwan ciki, sai dai in laifi ta masa kuma ko bugun ta yayi bai taka mata ruwan ciki, qila ma satan mangwaro taje ya kamata Inna ta ce, "yi hakuri fatuha ki kyale shi kin ji kuma kiga Rabi'u ba sa'an ki bane kin ji diyar baffan ta"
"kambuuuu..! ta zaro manya idanuwan ta "qur'an inna ban hakura..!
"haba fatuha yi hakuri Zan baki biyar kin ji" washe baki tayi kamar ba ita ke ihu da koke-koke ba ta ce, to inna na hakura kwarankwatsi" Inna ta washe baki fatuha ko ba wai har cikin zuciyar ta ta hakura ba, dan ta dau alwashi sai ta rama dukan da Rabi'u ya Mata haka ta bi inna cikin uwar d'aka tana matse kwalla da katse majina .
Misalin karfe hudu na yamma fatuha ce zaune tsakar gida wadda take share kwal, ba dati ko d'aya da yake inna akwai san tsafta duk yadda ta so ta gyara fatuha da ta fita zata dawo kamar almajira ko sabuwar mahaukaciya saboda tsaban rashin ji ko wanka sai anyi da gaske, inna ke samu ta dirje ta fura take sha hankali kwance daga gani fura na kai mata karo dan sai rausaya kai take kamar kadangaruwa, inna ce ta lek'o daga uwar d'aka ta ce, "fatuha yi sauri ki shirya ki tai makaranta allo.! baki ta turo gaba kamar zata tunkud'i birji ta ce, "gaskeya yau inna ban zuwa, na gaji qur'an kullun Malam d'alha sai ya bigeni" ta inda zancan tana matsar kwalla"
"to fatuha in baki je makarantar ba inaa zaki sauke? baki so na siya maki shanun a yanka ranar sauka? washe baki tayi ta ce, "to inna zani wallahi ko dan ki yanka min shanuwa babba tafi tasu fatsima kwarankwatsi"
"yawa yar albarka maza ki shirya" hijabin ta dake saman igiya ta janyo ta zura ta fita da gudu inna ta girgiza kai ta dau kwanan fura ta Kai madafi ta aje.Fatuha da ke tafe tana yan surutai wanda ko ni (salma) bajin ta nake ba chan ta tsinkayo muryar malam dalha taja birki ta tsaya tana raba ido dan tasan kashin ta ya bushe, dan ba k'aramar makara tayi ba, Malam d'alha ne ya juyo sukayi ido 4 da fatuha ya kwallo ido waje ya ce, keeeeeeeee!! fatuha dan uban ki yanzu ne lokacin zuwa makaranta shegiya mai Kama da mayu, duk kauyan nan kin raina uban kowa" yana huci ya cigaba da cewa, "yau zaki ci gwafar ubanki wallahi" fatuha dake ta raba ido ta duqa da niyar rarumo takalmin ta ta ruga muryar Malam d'alha ce ta tsinke mata tunani "wallahi kika ruga sai na sa basiru ya dauko min ke akai" kasancewa tasan basiru Ba k'aramin kato bane yasa taja ta tsaya chafka d'aya Malam d'alha ya mata yana muzurai kuka ta farayi tana yarfe hannu tana bashi hakuri Allah annabi amma yayi biris ya fisgota ya fara kila kamar an aiko shi, ihu take jera mai da Allah ya isa bugun ta yake amma bakin yaki mutuwa dan kan shi ya gaji da dukan ta ya hakura, fatsima da ke gefe sai matsar kwalla take tana yimai daquwa ta hijabi ta, lalla6owa gefan fatuha tayi Malam D'alha be ganta ba ta ce, "yi hakuri fatuha kin ji Allah sai ya saka maki" fatuha dake matsar kwalla ta turo baki gaba ta ce, "billahilazi sai na rama fatsima, ba yana zuwa gidan qilu zance ba da yamma ba, kwarankwatsin dubu sai nayi maganin shi fatsima"
"Kai fatuha ki kyale shi dan wallahi ki kai mai iskanci har gida zai biki dan Malam D'alha ba wayau garashi ba, ya hadaki da baffa"
"yo nima wayau ya isheni? ta karashe zancan tana washe baki fatsima taja bakin ta tayi shuru haka suka cigaba da karatun su dai-dai gwargwado fatuha na da k'okari sai dai bata jin magana ko kad'an, ba wanda bai san ta akauyan su ba.Mayan motoci ne kira bentley guda 5 suka nufi wani katafarin gate kallo d'aya nayi ma motocin na hadiye miyau dai-dai katafarin gida motocin suka kunna Kai wurin parking suka nufa suna gama parking da sauri wasu sojoji guda 4 suka foot daga ciki motar gaba at the same time sojojin 4 na cikin motor baya suka nufi motar tsakiya ahankali d'aya daga cikin sojojin ya bud'e mai murfin motar tsakiya wani had'addd'en kafa nagani mai sanye da booth yana cikin kakin shi na sojoji karfafen namijine kyauwan sa ya isa wow fari ne Sol idanu sa manne da glass fari wadda ya fido da zala kyan shi da qwarjinin shi dogo ne sosai jikin shi murd'e yana da fad'and'an kirji gashin kanshi mai laushi ne duk da gashi na cikin hula shi na uniform hakan be hana gashinshi bayyana ba, ga sajan shi kwance hanci shi kamar pencil dan tsini briefcase din shi ya amsa hannu daya daga cikin yaran sa, fuskarsa murtuke Ba alamar dariya kamar an aiko mai da wahayin mutuwa, (na ce ohni Salma da guy dinan zeyi dariya da ba k'aramin kyau zaiyi ba) haka yaran suka bashi guri ya wuce Kai tsaya main palour ya nufa wow fad'i tsaruwar palour bata lokaci ne saboda ba karamin haduwa yayi ba baba jummai da ke gafe cikin washe baki ta tsugunna tana kwasar gaisuwa cikin isa kamar mai koyan magana ya amsa tare da cewa, "mom fa?
"ah mai gida tana sama" K'ara d'aurewa yayi dan wannan suna k'ona mai rai yake a hankali yake taka matatakala cikin isa.Kai tsaye d'akin mom ya shiga had'add'an d'aki ne mai kyau sanyin AC sai ratsa d'akin yake hajiya da ke zaune saman kujera dressing mirror tana shafa turare tasha had'add'en leshin ta mai kyau, fara ce bafulata na kallo d'aya zaka mata kasan hutu ya zauna mata, ahankalin ya k'araso yayi huging nata cikin fara'a ta juyo dan tasan ba mai mata haka se son, kiss ya sakar mata a kumatu ya ce, "Mom I miss you..!
"miss u more son welcome back dear, baby ka k'ara girma kamar ba Kai ba" turo baki yayi ya langwabe Kai alamar shagwaba ya ce, "Kai Mom ni dai gaskiya ban girma ba"
"AI ka ji da shi, yanzu dai kaje kayi wanka ka dawo your food is ready a dinning area"
"ok Mom..! ya fice yana murmushi kamar bashine Wanda ke d'aurewa d'azu ba...!
YOU ARE READING
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...