Writing by
Salma mas'ud nadaboEdit by
Raheenat📘 REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
★ we are the best★https://mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&_tn_=H-R
*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
25_26
Basu suka dawo gida ba sai bayan isha lokacin har jidda tayi bacci, d'auke yake da ita har suka qaraso parlour, lokacin rabi'a tana qoqari fitowa daga kitchen, wani irin kallo ya wurga mata jiki ba qwari ta gaishe shi har tayi gaba ya ce, "Keeee.! Tsayawa tayi cikin tsoro da fargaba, Harara ya qara wurga mata cikin tsawa ya ce mata "Sai ki zo ki amshe ta ko?" Jiki a sa6ule ta amshi jidda, ya ce, "Kiyi mata wanka sannan ki samata night dress ki kawo min ita d'aki na dan ban yarda ta rinqa kwana da ke ba ki koya mata halin bera" tsaki yaja Mtsss, sannan ya wuce part din Abba.
Abba na zaune saman two star fuskar shi manne da glass, sanye yake da fara jalabiya blue remote ne a hannusa yana kallon news, Mom na gefen sa tana yanka fruit.
D'au da sallama ya shigo tare da gaishe da Abba, cikin fara'a Abba ya amsa ya ce "Ah har kun dawo daga zuminci?
"Eh Abba"
"toh masha Allah ina jidda?
"jidda tayi bacci"
"madallah" sun dad'e suna hira sama-sama daga nan Sadiq ya wuce part nashi, ko da ya shiga d'akinsa ya iske ankwantar da jidda shima bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito sai da ya gama shirin shi na bacci sannan ya had'a coffee yana sha yana dana laptop din shi ,ya dad'e a haka sannan ya ture laptop d'in tare da janyo jidda jikin shi bacci ya d'aukesa.
*****
Bayan an gama gad'a kowace ta wuce gidan su, da sallama fatuha ta shigo gida lokaci Baffa ya dawo gida yana zaune bisa tabarma inna na kusa da shi baba jummai na gefe su, gefan baba jummai ta je ta zauna washe da baki itama baba jummai murmusawa tayi sun danyi hira sama-sama da fatuha daga nan bacci ya sureta.Baba jummai ce tayi gyaran murya ta ce "Dama jauro ina so muyi wata magana da kai" inna da ke kusa da Baffa tayi qoqari tashi baba jummai ta ce "Kema zauna" haka ko akayi inna ta samu guri ta zauna.
Gwoggo ta cigaba da cewa, "Dama so nake nama ka magana kan fatuha ina so idan zan koma birni sai mu koma tare," Zaro ido Baffa yayi waje yana kallon yar uwar tasa a zuciyarsa ya ce "Anya ko baba jummai tasan me take fada kuwa?"qara murmusawa tayi ta ce, "jauro ina fatan ba za ka watsamin qasa ido ba, a ganina fatuha nima d'iya tace jauro," Baffa ne yayi tsale ya dare ya ce bai san zancan ba babu inda fatuha zata tanan kauyen nan tare da shi baze lamunci hakan ba, baba jummai ce ta fara matsar kwalla tana cewa "Ba komai jauro dan ka ga Allah bai bani haihuwa ba shine zaka wulaqanta ni kan diyar ka, jauro da Allah ya bani haihuwa da yau ba zanji zafin abinda kayi min ba," tana maganar tana kuka inna sai lallashinta take, ganin kukan da take yasa jikin Baffa yayi sanyi dan shi a ganinsa babu abinda baba jummai zata nema a rayuwar shi ya hana ta, sai gashi kan fatuha suna neman samun Matsala da yar uwarsa.
Bayan da ya iya haka ya hakura ya amince tatafi da fatuha, aiko washe da baki ta masa godiya tare da yi masa alqawarin zata riqe amanar fatuha sosai daga nan kowa ya wuce dakinsa.
******
Ko da ya tashi ya gama shirin sa ciki uniform masha Allah yayi kyau sosai, zai d'au briefcase d'in sa kenan jidda ta tashi washe da baki ta ce, "Daddy morning"
"morning too angel"
"uhm yau ma daddy guduwa zakayi ka bar little princess din ka a gida? langwabe kai yayi ya ce "Sorry angel daddy work zai tafi kinji kuma yara basa zuwa, kema very soon zaki fara zuwa school ai kinaso ko angel? washe baki tayi ta ce "Yes daddy zan fara zuwa school kamar yarda su yaya Hanan ke zuwa da Anuty Basma ko?
"Eh mana angel" tsale tayi ta kai masa hug "thanks my daddy" smile yayi tare da yimata peck ya ce, "please angel ki tsaya rabi'a ta maki wanka kin ji, naji grandma na cewa kullun sai kin yi rigima" 6ata fuska tayi ta ce, "Daddy...!
"shhhh.! tare da yi mata peck a kumatu ya fice.A dining area ya had'u da Abba shima yana breakfast, Mom na gefen shi a hankali ya qarasa yayi masu peck sannan ya samu waje ya zauna ya fara breakfast, lafiyayan chips ne da plantain and egg sai tea mai kauri wanda ya sha ovaltine, cikin natsuwa suka gama break d'in su, Abba da Sadiq tare suka fito inda yaran Sadiq ke ta kwasar gaisuwa wajan Abba tare da qamema Sadiq d'in cikin natsuwa motocinsu suka fita daga harabar gidan.
****
Ko da fatuha ta tashi wanke-wanke tayi, sannan ta d'au tulun ta gidan su fatsima ta biya tare suka fito suna tafe suna hirar su, kandala suka hango d'auke da farantin gyadarta qarasowa su kayi wajan ta, Kallon su take jiki ba kwari harara suka wurga mata tare da cewa "Bamu gyad'a ta murtala" jikinta baqwari ta fara zuba masu gyad'ar tasan ko zata mutu baza su bata kudin gyad'ar ba, kuma ta matsa masu su tona mata asiri sai da ta gama zuba masu sannan fatuha ta amsa ta ce "Cikin Murtala da d'an mai gari ya mana alqawari ne muka amshi gyadar, sannan kice masa ko ya bamu murtalar mu ko kuma murtala ta rinqa haihuwa" sannan suka wuce suka barta tsaye tana matsar kwalla.Suna isa rafi suka aje tulu nan su gefen rafi suka wuce gonar mai gari suka fara tsinkar mangwaro da gwaba, sai da suka d'iba son ransu sannan suka zo zasu fita mai gadi ya kama su.
"kai-kai uban wa ya baku ikon shigowa gonar mai gari? har ku tsinke masa mangwaro.! Fatuha ce ta turo baki gaba ta ce, "bala ne ya bani izinin shigowa"
"shegiya mai kama da mayu, shi balan sa'an kine? Koko sabo da raini irin naki dama kin rai uban kowa, inama kika san balan? harara fatsima ta wurga masa ta ce, "idan baka yarda ba sai ka kai mu wajan shi ka ji da kunnan ka" ta ida zancan tana gyara d'aurin zaninta.
"Ai dama ba kunya ta ishe ki ba mindin naji akasin haka na lahira sai ya fiki jin dad'i "
Aiko haka akayi mai gadi jan su fatuha yayi har gaban bala, sai yan harare-harare suke koda ya suma bala ya masa bayani sai ya ce, "shi ya ce su d'inba dan yasan in bai ce ba tuna masa asari zasuyi, na sun ta6a kamasa da kandala gari kowa ya sani ana ganin sa da mutunci sannan yasa mai gadi ya sake su wani irin dad'i suka ji suna ta shewa suka isa rafi suka debo ruwa.
*****
Bai zame ko ina ba sai Yandutse college dan samoma jidda admission, bai sha wani wahalla ba ya samama ta inda duk angama abinda za'ayi, ranar Monday sai ta fara zuwa school sannan ya wuce office, a cewar shi inya dawo gida da yamma zai samamata malamin adini.
****
Kwanci tashi asarar mai rai yau satin baba jummai d'aya a wudil inda take ta had'a kayanta dana fatuha, Fatuha sai kuka take har da majina dan ita a ganinta baba jummai bata mata adalci ba ita tace mata tana son birni da zata kwashe ta su tafi, toh Wallahi sai nayi rashin mutunci idan sunje kenan, cewar fatu a zuciyarta baba jummai ce ta juyo ta ce, "haba fatuha sai ka ce za'a cinye ki sai kuka kike haba fatuha kinsan muna tare kuma zan kula da ke kamar yarda inna zata kula da ke, dan Allah kiyi hakuri kiyi shuru kinji" Inna da ke gefe duk da tana jin wani irin amma tasan baba jummai ba zata tayi abinda zai cutar da fatuha ba amma ko yaya tana jin zafin rabuwa da fatuha saboda fatuha yarinya ce mai shiga rai, ta wani fanni kuma gara fatun ta tafi ko muta nan kauyan sun huta da jarabar fatuha, a hankali inna ke lallashin fatuha har tayi shuru haka shima Baffa da ke gefe haka baba jummai ta gama had'a kayan fatuha cikin yar leda gari yayi zafi ta miqa mata ta rungume.
Baffa kuma yaje taro masu mashin, Sallama fatsima tayi ta shigo falon kallo d'aya zaka mata kasan itama ta ci kuka har ta gaji, wani saban kuka suka dasa ita da fatsima dakyar aka lallashe su sannan baffa ya shigo ya sheda masu gamai mashi din.
Suna kallon su har suka 6ace maganin su Baffa ya goge yar kwallar shi, dan shi kad'ai yasan yarda yake ji, suna isa tasha suka samu motar Kano basu wani dad'e ba motar ta tashi.
*******
Idanuwansa lumshe kamar wanda ke bacci, zaune yake saman resting chair yayi crossing leg's nashi ta6a shin da akayi ne ya sasa ware sexy eye's ball's d'in sa ba kowa bane sai majid murmushi yayi ya ce "Yaushe ka zo ban sani ba?
"yanzu na shigo Mom ta ce min kana nan" sannan ya zauna daya daga cikin chairs din sadiq ya ce, "OK ya aiki?
"Alhamdulillah soma nake na dawo nan da aiki, kai Allah ya taimake ka har yau basu ma transfer ba"
"Aiko dai ai bana fatan hakan wallahi" murmushi sukayi su duka suka cigaba da magana a matsayin su na abokai kuma yan'uwa...
YOU ARE READING
CAPTAIN SADIQ
Romanced'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah...